Tsohon Hafsan Sojoji Ya Nausa Kotu kan Zargin Yana da Alaka da Ta’addanci
- Tsohon Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Faruk Yahaya (mai ritaya), ya garzaya kotu kan zargin da ke danganta shi da ta’addanci
- Yahaya ya bai wa wadanda suka yi zargin da kafafen yada labarai wa’adin awanni 72 su janye kalamansu tare da neman afuwa
- Janar din ya ce matakin shari’ar na da nufin kare mutuncinsa da kuma tsare gaskiya da kwarewa a hukumomin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya (mai ritaya), ya shiga kotu kan zarginsa da ta'addanci.
Yahaya ya dauki matakin shari’a domin kare mutuncinsa, bayan zarge-zargen karya da ke danganta shi da daukar nauyin ta’addanci.

Source: Facebook
Ta'addanci: Farouk Yahaya zai dauki matakin shari'a
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon kakakin rundunar sojin kasa, Birgediya Janar Sani Usman (mai ritaya), ya fitar wanda Vanguard ya samu.
Sani Usman ya bayyana cewa tsohon Manjo Janar Danjuma Ali-Keffi (mai ritaya) ne ya yi wadannan kalamai yayin wata hira da aka yi da shi.
A cewarsa, Faruk Yahaya ya umarci lauyoyinsa, karkashin jagorancin Mohammed Ndayako (SAN), domin mika takardun gargadi na shari’a ga mutanen da kafafen yada labaran da abin ya shafa.

Source: UGC
Wa'adin da Farouk Yahaya ya ba masu zarginsa
Sanarwar ta bayyana cewa takardun gargadin, da aka sanya wa kwanan wata 17 ga Disamba, 2025, sun bai wa wadanda abin ya shafa wa’adin awanni 72 su janye zarge-zargen gaba daya, su nemi afuwa ba tare da wani sharadi ba, sannan su daina kara yada labarin.
A cewar takardar:
“Rashin bin wannan gargadi zai haifar da daukar cikakken matakin shari’a.
“Irin wadannan zarge-zargen karya da mugunta suna da hadari, kuma suna iya rushe amincewar jama’a ga hukumomin kasa da kuma mutanen da suka yi wa kasa hidima cikin kwarewa.”
Dalilin Farouk na daukar matakin shari'a
Sani Usman ya kara da cewa Janar Faruk Yahaya ya bayyana cewa daukar wannan mataki ba wai kawai don kare mutuncinsa ba ne, har ma domin kare kwarewa, gaskiya da rikon amana a ayyukan gwamnati.
Ya jaddada cewa ba za a kyale labaran karya da zarge-zargen mugunta su ci gaba ba tare da kalubale ba, musamman idan suna iya bata sunan wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa kasa hidima.
Tsohon sojan ya ce yana da tabbacin hakan zai taimaka wurin kare mutuncinsa da sanar da duniya halin da ake ciki, cewar Premium Times.
Malami ya musanta zargin hannu a ta'addanci
Mun ba ku labarin cewa tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya yi tsokaci bayan ambatar sunansa cikin mutanen da ake zargi da daukar nauyin ta'addanci.
Abubakar Malami ya bayyana cewa ko sau daya ba a taba gayyatarsa a ciki ko wajen Najeriya kan batun da ya shafi daukar nauyin ta'addanci ba.
Malami wanda ya taba zama babban lauyan gwamnati ya bayyana manufar da mutanen da ke yada zargin daukar nauyin ta'addancin ke son cimmawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

