Faruk Yahaya: Ina da gogewa a fannin yaki, zan iya shawo kan matsalar tsaron Najeriya

Faruk Yahaya: Ina da gogewa a fannin yaki, zan iya shawo kan matsalar tsaron Najeriya

  • Shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahaya ya tabbatar da gogewar da yake da ita a filin daga
  • Kamar yadda ya sanarwa majalisar wakilai a ranar Talata da ya gurfana a gabanta, ya ce gogewarsa za ta sa ya shawo kan matsalar tsaro
  • Majalisar wakilan Najeriya ta kira Manjo Janar Farouk Yahaya domin tantance shi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi COAS

Farouk Yahaya, shugaban rundunar sojin kasa ya ce yana da gogewar da zai iya shawo kan matsalar tsaron kasar nan.

Yahaya ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da lamurran tsaro domin tantancewa.

Shugaban sojin ya ce ya halarci yaki da kwantar da tarzoma a Liberia inda ya kara da cewa gogewarsa kadai ta isa ta inganta tsaron kasar nan, The Cable ta ruwaito.

"Na bayyana tare da gogewata ta tsawon shekaru 36, ganin cewa na shiga rundunar a ranar 27 ga watan Satumban 1985 kuma ina daga cikin 'yan aji na 32 na makarantar horar da hafsoshin soji ta kasa," yace.

KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 56 da kifi ya hadiye kuma ya amayo shi, ya bada labari dalla-dalla

Faruk Yahaya: Ina da gogewa a fannin yaki, zan iya shawo kan matsalar tsaron Najeriya
Faruk Yahaya: Ina da gogewa a fannin yaki, zan iya shawo kan matsalar tsaron Najeriya. Hoto daga Nigerian Army
Asali: Facebook

KU KARANTA: Nnamdi Kanu dan ta'adda ne da IPOB yake kasuwanci, Cewar Asari Dokubo

Manjo Janar Yahaya ya bada tarihin gogewarsa

"An yaye ni a ranar 2 ga watan Satumban 1990 kuma an tura ni makarantar rainon sojoji. Daga nan na cigaba da yin kwasa-kwasai masu alaka domin samun gogewa kuma na yi aiki a wurare daban-daban.

“Kasa da shekaru uku da suka gabata, an tura ni Liberia inda na samu gogewar farko a filin daga," yace kamar yadda TheCable ta wallafa.

Manjo Janar Farouk Yahaya ya maye gurbin marigayi Attahiru

A cikin watan da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin shugaban rundunar sojin kasa ta Najeriya.

Ya maye gurbin marigayi Laftanal Janar Attahiru Ibrahim wanda yayi hatsarin jirgin ya rasu a wata ranar Juma'a a garin Kaduna.

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya tayi kira ga 'yan ta'addan Boko Haram da su ajiye makamai kuma su nemi yafiya tare da sasanci.

AA Eyitayo, babban kwamandan Div 7 na rundunar sojin kasa, yayi wannan kiran a ranar Lahadi a wani taro da rundunar ta shiryawa manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Eyitayo ya ce 'yan ta'addan Boko Haram suna cikin dimuwa bayan gagarumin luguden wuta tare da matsanta musu da sojoji suka yi, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel