Dalla Dalla: Yadda Matasan Najeriya Za Su Shiga Aikin Sojan Kasa lkarkashin DSSC
Abuja - Rundunar sojojin kasan Najeriya ta bude shafin daukar sababbin dakaru karkashin DSSC, Course 29/2026, inda ake gayyatar wadanda suka cancanta su nemi zama cikakkun jami'ai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rundunar sojojin ta ce an bude shafin daukar aikin na DSSC ne ga fararen hula da kuma sojoji da ke aiki, kuma za a dauki ma'aikatan ne a bangarori daban daban.

Source: Twitter
An bude shafin daukar sababbin sojoji
A cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta ce za a fara cike fom din neman aikin ne ne daga ranar 7 ga Janairu zuwa 4 ga Fabrairu, 2026, kuma komai za a yi shi ne a shafin rundunar na yanar gizo kyauta ba tare da biyan ko kwabo ba.
Ɓangarorin da rundunar ke neman ma'aikatan sun haɗa da: Injiniyoyin soji, fannin sadarwa (Signals), fannin lafiya, Injiniyoyin lantarki da kanikawa, da kuma fannin ilimi.
Shirin daukar aiki na DSSC na bai wa ƙwararru damar shiga rundunar sojoji domin bayar da ƙwarewarsu ta musamman a fannonin da suka dace da su.
Domin ƙarin bayani, rundunar ta bayar da lambobin waya 08179269294 da 08109959294, waɗanda za a iya kira kullum daga karfe 8:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.
DSSC: Sharuddan neman aikin sojojin kasa
A cikin wata takarda da aka haɗa da sanarwar, rundunar ta ce dole ne masu neman aikin su kasance haifaffun ’yan Najeriya, kuma su kasance tsakanin shekaru 20 zuwa 32 zuwa ranar 30 ga Maris, sai dai an kara yawan shekarun likitoci zuwa 40.
Dole ne duk masu sha'awar aikin su kasance cikin koshin lafiyar jiki, hankali da zuciya bisa ƙa’idojin sojojin Najeriya, tare da cika sharuddan tsawo, wato mita 1.68 ga maza da mita 1.65 ga mata aƙalla.
Rundunar ta jaddada cewa dole ne masu sha'awar yin aikin su kasance mutanen kirki, ba tare da tarihin aikata laifi ba. Haka kuma, ba za su kasance mambobin ƙungiyar asiri ko kungiyoyin tsafi ba, kuma ba za su kasance da zanen jiki ko rubuce-rubuce a jiki ba.
Ga sojojin da ke aiki, dole ne su kasance ba su da matsalar saba wa hukuma, kuma su gabatar da takardar amincewa daga kwamandan su.
Takardu da cancantar da ake bukata
Dole ne masu sha'awar yin aikin su mallaki aƙalla digiri na farko da sakamakon Second Class Lower ko HND Upper Credit daga makarantar da aka amince da ita.
Rundunar ta ce za a yi amfani da takardun karatun da aka same su ne daga 2011 zuwa 2025 kawai, kuma dole masu sha'awar yin aikin su gabatar da sahihiyar takardar haihuwa ko shaidar shekaru, takardar asalin jiha, da takardar kammala NYSC.
Za a buƙaci masu sha'awar yin aikin su gabatar da dukkan takardun karatunsu na asali ba kwafi ba yayin tantancewar ƙarshe. Haka kuma, masu digiri na musamman, kamar likitoci su kasance suna da cikakkiyar rajista da ƙungiyoyin ƙwararru da doka ta amince da su a Najeriya.
Masu bada shaida da sauran sharudda
Dole ne masu sha'awar yin aikin su samu mutane biyu masu mutunci daga jiharsu ta asali da za su iya tsaya masu, a cewar rahoton Premium Times.
Rundunar sojojin kasan ta ce waɗannan mutanen za su kasance ko dai ciyaman ko sakataren ƙaramar hukuma, ko babban hafsan soji da bai gaza mukamin Laftanal Kanal ba, ko kuma mataimakin kwamishinan ’yan sanda (ACP) ko sama da haka.
Dole ne waɗannan masu bada shaida su sanya hannu kan takardun neman aikin tare da haɗa hoton fasfo nasu. Haka kuma, masu sha'awar yin aikin za su bayar da ingantattun lambobin tuntuɓar iyaye ko masu kula da su da kuma na wanda zai gaje su.

Source: Getty Images
Bukatar samun kwarewa a fannin da aka nema
Baya ga sharuddan neman wannan aiki, dole ne masu sha'awar yin aikin su cika ƙa’idojin ƙwarewa na musamman gwargwadon sashen da suka zaɓa.
An bude shirin DSSC ga ƙwararru a fannonin Injiniyoyin soji, fannin sadarwa (Signals), fannin lafiya, Injiniyoyin lantarki da makanikai, da kuma fannin ilimi.
Wannan ya haɗa da injiniyoyi masu digiri a fannonin gini (civil), lantarki, injina, kwamfuta da makamantansu; ga likitoci, ana bukatar kwararrun likitoci, malaman jinya, masu hada magunguna da sauran ma’aikatan lafiya da suka yi cikakkiyar rajista da hukumomin su; da kuma masana ilimi masu sahihin digiri da takardun koyarwa.
Rundunar ta jaddada cewa duk masu neman shiga waɗannan sassa dole ne su mallaki digiri, takardun ƙwarewa da rajistar doka da suka dace da fannin da suke nema.
Za a tilasta wa 'yan Najeriya shiga aikin soja?
A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar sojojin Najeriya ta fitar da sanarwa, domin wayar da kan al'umma kan jita-jitar cewa za ta tilasta wa matasa shiga aikin soja.
An danganta jita-jitar da cewa Laftanar-janar Waidi Shuaibu ne ya yi ikirarin tilasta wa matasa shiga soja, sai dai rundunar ta fito ta yi bayani.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta jawo martani daga jama’a, inda wasu suka nemi sojoji su maida hankali kan matsalolin tsaro da ya addabi mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



