Yawan karatu na sa tsawon rai- Inji masana

Yawan karatu na sa tsawon rai- Inji masana

Masana ilimin kimiyya sun fitar da wani bincike da ke nuna cewa yawan karatu na sanya tsawon rai.

Yawan karatu na sa tsawon rai- Inji masana

Binciken ya hada da mutane 3500, kuma an fara shit un shekarar1992 sai yanzu aka kammala shi. An rarraba mutanen gida uku. Na farko ba masu yin karatu bane, na biyu suna karatu kadan kadan, su kuma na uku suna tsananin karatu.

Sakamakon binciken ya bada mamaki matuka inda ya nuna wadanda suka fi tsananin karatu sune mata masu aiki kuma wadanda suke da matsakaicin ilimi. Yawan karatu na kara ma dan adam tsawon rai da kasha 17, idan kamanta da masu karatu kadan.

Sa’annan binciken ya nuna masu yawaita karatu na rage yiyuwar mutuwarsu a samartaka da kasha 23 fiye da wadanda basa karatu gaba daya. masu karance karance suna fin marasa karatu tsawon raid a shekaru 2.

Ga abin da masanan suka ce

“ mutanen da ke karatu na akalla awa daya a rana sunfi yiyuwar samun tsawon rai fiye da wadanda basa karatu.”

Don haka banda sauran amfanin karance karance littafai, zasu iya kara maka tsawon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel