Shekaru 7 bayan Tsige Shi daga Shugaban DSS, Lawal Daura Zai Fito Takarar Gwamna

Shekaru 7 bayan Tsige Shi daga Shugaban DSS, Lawal Daura Zai Fito Takarar Gwamna

  • Lawal Daura, tsohon shugaban hukumar DSS ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina a zaben 2027 mai zuwa
  • Tsohon babban jami'in tsaron, ya ce lallai akwai bukatar a sauya gwamnatin Katsina mai ci don ta gaza cimma nasarori a wa'adin farko
  • Alhaji Lawal Daura ya zayyano manyan dalilan da suka sanya shi ayyana tsayawa takarar, da kuma yadda yake son jihar Katsina ta koma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (SSS/DSS), Lawal Daura, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina a zaɓen shekarar 2027.

Lawal Daura ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 6 ga watan Janairu, 2025, inda ya kawo rashin tsaro da kuma abin da ya kira gazawar gwamnatin jihar ta yanzu a matsayin dalilansa na shiga takarar.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya yi amai ya lashe, ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC

Lawal Daura ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Katsina.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda a lokacin da ya kai wa Lawal Daura ziyarar ta'aziyya. Hoto: @ibrahimmasari20
Source: Twitter

Lawal Daura zai nemi takarar gwamnan Katsina

A zantawarsa da DCL Hausa, Lawal Daura ya bayyana cewa ya kammala yin shawara kan burinsa na shiga siyasa kuma nan ba da daɗewa ba zai bayyana jam’iyyar da zai yi takarar a cikinta.

Lawal Daura ya soki salon shugabancin Gwamna Dikko Radda, inda ya bayyana cewa idan jagora ya kasa tabuka abin arziki a wa'adinsa na farko, to babu bukatar neman sake zabensa.

Ya buga misali da cewa, shugabanci kamar lodi ne; idan ya yi wa mutum nauyi, gara a sauke masa domin gudun kada ya lalata kayan da aka ɗora masa.

Ya jaddada cewa ko da yake bai taɓa tunanin tsayawa takara ba a baya, amma halin da jihar Katsina take ciki ya yanzu ya tilasta masa fitowa domin ceto al'umma.

Dalilin shigar Lawal Daura harkar siyasa

Tsohon shugaban jami'an tsaron ya bayyana cewa matsin lamba daga manyan mutane da masu ruwa da tsaki a jihar Katsina ne ya sa ya yanke shawararsa ta shiga harkar takara.

Kara karanta wannan

PDP ta yi rashi, tsohon sanata ya fice daga jam'iyyar bayan shekara 20

Lawal Daura ya ce waɗannan mutane sun nuna matuƙar damuwa kan yadda matsalar rashin tsaro ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a jihar Katsina, in ji rahoton Daily Nigerian.

Daura ya nuna cewa kwarewarsa a fannin tsaro na tsawon shekaru za ta taimaka masa wajen kawo karshen ayyukan ta'addanci da suka addabi jihar idan aka zaɓe shi.

Lawal Daura ya zargi Gwamnatin Dikko Radda da gazawa wajen cimma nasarori a Katsina.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, wanda Lawal Daura ya zarga da gazawa wajen magance tsaro. Hoto: @dikko_radda
Source: Facebook

Lawal Daura ya amsa kiran al'umma

Tsohon shugaban na DSS, da aka tsige shi daga mukamin a 2018, ya ƙara da cewa duk da ya daɗe yana sha'awar siyasa tun zamanin Shehu Shagari, aikin tsaro ya hana shi bayyana kudurinsa.

Amma a yanzu, Lawal Daura ya ce siyasa ce kaɗai hanyar da zai iya yin amfani da ita don taimaka wa mutane su ji daɗin rayuwa cikin tsaro da samun ci gaba.

Lawal Daura ya kuma ce idan aka kira mutum domin ya bauta wa al'ummarsa, bai kamata ya ƙi ba, musamman idan ya ga cewa yana da kwarewar da za ta iya samar da mafita fiye da kowa.

Kalli bidiyon hirar a nan:

Abubuwan sani game da Lawal Daura

Kara karanta wannan

Bayan Sokoto, an fadawa Trump jihar da ya kamata ya kai sabon hari a Najeriya

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, an haifi Lawal Daura, shugaban hukumar DSS da aka kora daga aiki ne a ranar 5 ga watan Agusta, shekarar 1953.

Lawal Daura dai ya fito ne daga karamar hukumar Daura, ta jihar Katsina kuma ya yi karatunsa na jami'a a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, jihar Kaduna.

An ce ya fara aikin jami'in tsaron farin kaya a shekarar 1982, inda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban DSS a 2015, aka tsige shi a 2018.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com