Lawal Daura kafa tasa gwamnatin yayi a gefen ta Janar Buhari - Col. Dangiwa Umar

Lawal Daura kafa tasa gwamnatin yayi a gefen ta Janar Buhari - Col. Dangiwa Umar

- An Sauke Daura ne saboda ya mamaye majalisa da jami'an tsaron farin kaya

- Kanal Dangiwa Umar yayi tsokaci kan yadda lamarin yake

- Lawal Daura bai nemi izinin shugaban kasa ba yayi wannan aiki

Lawal Daura kafa tasa gwamnatin yayi a gefen ta Janar Buhari - Col. Dangiwa Umar
Lawal Daura kafa tasa gwamnatin yayi a gefen ta Janar Buhari - Col. Dangiwa Umar

Kanar Dangiwa Umar, tsohon gwamna a lokacin mulkin soja na Babangida, ya tofa albarkacin kinsa kan yadda aka tumbuke aka kori, tare da kama da bincikar mafi karfi a gwamnatin shugaba Buhari, shugaban DSS, Lawal Musa.

Abubakar Dangiwa, yace an ma ja lokaci kafin a sallamin Malamin wanda a cewarsa ya dade yana cuzguna wa mutane, yana ma kuma tafiyar da tasa gwamnatin ba tare da ya shawarci shuwagabanninsa ba ko ma ace ya bi ka'idar da gwamnati da tsarin doka ya tanada.

DUBA WANNAN: Sabbin hanyoyin shigo da man fetur arewa

Ya kuma kara da cewa, duk wanda ya bi sahun Lawwalin, ya kamata shima a hukunta shi a kotu.

Ya kuma ce wannan zai zama darasi kan yadda ake kokarin tayar da dimokuradiyya a Najeriya.

In za'a tuna a baya, bayan da ogansa IBB ya kansile zaben Abiola, saboda kishin dimokuradiyya, Dangiwa Umar, barin gwamnatin kawai yayi yace baya yayi, lamari da ya kara zaizaye sauran mutuncin gwamnatin lokacin a idon jama'a, wanda dole daga karshe, Babangidan ya hakura ya koma Minna daga fadar Mulki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng