Tankar Mai Ta Kutsa cikin Ayarin Motocin Shugaban Majalisa, Akpabio, an Rasa Rai
- An samu rasa rai bayan wata tankar mai ta buge ayarin motocin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya yi ajalin kashe wani jami’in da ke tare da su mai suna Ibrahim Hussaini
- Akpabio ya bayyana cewa marigayin ya bar mata biyu da yara hudu, tare da daukar alkawarin samar musu da aikin yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Wata tankar mai ta kutsa ayarin motar Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio a jihar Oyo.
An tabbatar da cewa lamarin ya yi sanadin mutuwar wani jami’i da ke tare da tawagar da ake kiransu ‘Dispatch riders’ mai suna Ibrahim Hussaini.

Source: Twitter
Godswill Akpabio ya fadi rashin da ya yi
Akpabio ya bayyana faruwar lamarin ne a zaman Majalisar Dattawa na ranar Talata 23 ga watan Disambar 2025, cewar Premium Times.
Yayin zaman majalisar, Akpabio ya jajanta wa iyalan marigayin bisa wannan babban rashi da suka yi.
‘Dispatch riders’ su ne jami’an ‘yan sanda ne da ke hawa babura a matsayin wani bangare na tsaron manyan jami’an gwamnati.
Shugaban Majalisar Dattawa yana da akalla irin wadannan jami’an guda hudu a ayarinsa.
Ko da yake Akpabio bai bayyana takamaiman inda lamarin ya faru ba, ya ce abin ya faru ne a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, bayan ayarinsa sun dauko shi daga filin jirgin saman Ibadan.
Akpabio ya ce:
“Mun je jihar Oyo ne domin halartar bikin nadin wani abokin aikinmu, amma motocin da suka zo daukana daga filin jirgin saman Ibadan… abin takaici, direban tankar mai ya murkushe jami’ina, har kansa ya fashe. Mun riga mun birne shi mintuna 15 da suka wuce a jihar Kogi. Ya bar mata biyu da yara hudu.”

Source: Facebook
Akpabio ya roki a ba marayu aikin gwamnati
Shugaban Majalisar Dattawan ya roki shugabannin ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati da su bai wa ‘ya’yan marigayin aikin yi kai tsaye.
Ya kara da cewa idan babu guraben aiki a halin yanzu, shi da kansa zai tabbatar da daukar ‘ya’yan aikin yi, cewar TheCable.
“Da yardar Allah, ina ba da shawarar a dauki manyan ‘ya’yansa guda biyu aiki nan take a kowace hukuma da za ta iya. Idan kuma hakan bai yiwu ba, zan dauke su aiki da kaina a cikin harkokina na kashin kai.”
- In ji Akpabio.
Bayan wannan bayani, Sanatan Kogi ta Yamma, Sunday Karimi, ya mike da batun bayanin kai tsaye domin gabatar da lamarin a hukumance a gaban Majalisar Dattawa.
Yayin da yake jajanta wa Akpabio, Karimi ya ce marigayin jami’in tsaron, wanda ke da mukamin DSP, ya kusa yin ritaya a shekara mai zuwa.
Ya bayyana cewa Hussaini, dan asalin jihar Kogi, ya fara aiki a cikin ayarin Akpabio tun daga shekarar 2023, lokacin da ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Tsohon dan majalisar tarayya ya yi hatsari
Kun ji cewa tsohon dan majalisar tarayya, Hon. Ogbonna Nwuke, ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota.
Hon. Nwuke ya yi godiya ga Allah bisa yadda ya cece alshi daga hatsarin, wanda ya auku ranar Litinin, 22 ga watan Disamba, 2025.
Rahoto ya nuna cewa motar ta kama da wuta, amma Allah ya cece shi ta hannun wasu mutane da suka kawo dauki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


