Tsohon 'Dan Majalisar Tarayya Ya Yi Hatsari, Motar da Yake Ciki Ta Kama da Wuta

Tsohon 'Dan Majalisar Tarayya Ya Yi Hatsari, Motar da Yake Ciki Ta Kama da Wuta

  • Tsohon dan Majalisar wakilai, Hon. Ogbonna Nwuke, ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a jihar Ribas
  • Hon. Nwuke ya fito ya godewa Allah bisa yadda ya cece alshi daga hatsarin, wanda ya auku ranar Litinin, 22 ga watan Disamba, 2025 a Fatakwal
  • Rahoto ya nuna cewa motar da tsohon 'dan Majalisar ke ciki ta kama da wuta, amma Allah ya cece shi ta hannun wasu mutane da suka kai dauki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers, Nigeria - Tsohon ɗan Majalisar Wakilan Tarayya, wanda ya taba wakiltar mazabar Etche/Omuma, Hon. Ogbonna Nwuke, ya gamu da mummunan hatsari a jihar Ribas.

Rahoto ya nuna cewa Hon. Ogbonna Nwuke, ya tsallake rijiya da baya saboda munin hatsarin, wanda ya auku ranar Litinin, 22 ga watan Disamba, 2025 a birnin Fatakwal.

Kara karanta wannan

Rawani ya fadi: Kotu ta yanke wa basarake da wani mutum 1 hukuncin kisa a Gombe

Hon. Ogbonna Nwuke.
Tsohon dan majalisar wakilan tarayya daga jihar Ribas, Hon. Ogbonna Nwuke Hoto: Ogbonna Nwuke
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaoto cewa tsohon 'dan majalisa ya tsira da rayuwarsa bisa taimakon mutane amma motar da yake ciki kirar SUV ta kama da wuta a hatsarin.

Tsohon 'dan Majalisa ya yi hatsari

Lamarin ya faru ne a kan titin Eastern By-pass, kusa da Hypercity a cikin birnin Fatakwal yayin da Hon. Nwuke ke tuƙa motar da kansa a kan hanyarsa ta zuwa Trans Amadi.

Sai dai cikin ikon Allah, ya samu nasarar tsira ba tare da samun rauni ba bisa taimakon mutanen da suka kai masa dauki, suka fito da shi daga cikin motar.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin ta wayar tarho, Nwuke ya ce ya gode wa Allah bisa yadda ya tseratar da shi daga hatsarin.

Ya bayyana cewa duk da asarar motarsa da ya yi wacce ta kama da wuta, yana jin matuƙar godiya kasancewar ya fito da ransa.

Iyalan Hon. Nwike sun gode wa Allah

Kara karanta wannan

Tinubu ya sa lokacin da sababbin jakadu za su fara aiki bayan amincewar majalisa

'Diyar tsohon dan majalisar ta fari, Ebony Nwuke, ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da gode wa Allah bisa ceton mahaifinta daga hatsarin da ka iya jawo asarar rai.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, Ebony Nwuke ta bayyana godiyarta ga Allah bisa ceton mahaifinta, tana mai cewa, "Idan dukiya ce za a iya samun wata amma rai guda daya ne."

Jihar Ribas.
Taswirar jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ta ƙara da cewa Allah ya mayar da abin da zai iya zama jimami zuwa farin ciki, tare da kiyaye rayuwar mahaifinta, abin da iyalin suka ɗauka a matsayin babbar ni’ima.

"A yau, Allah ya kwaci mahaifina daga bakin mutuwa. Don haka zuciyata ta cika da godiya.
"Ana iya maye gurbin motoci, ana iya gyara ƙarfe, ana iya ƙirga dukiya da kuma ambatonta, amma rayuwa ta fi komai amfani kuma da zarar ta tafi, ta tafi har abada.

Ayarin kakakin Majalisar Jigawa ya yi hatsari

A wani rahoton, kun ji cewa hatsarin mota ya rutsa da ayarin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Rt. Hon. Haruna Aliyu Dangyatin a hanyarsa ta zuwa Maigatari.

Kara karanta wannan

'Shirya komai aka yi': An 'gano' yadda rashin tsaro ya fara a Najeriya

Bayanai sun nuna cewa Kakakin Majalisar ya tsallake rijiya da baya a hatsarin wanda ya rutsa da motar ayarinsa a lokacin da yake hanyar zuwa garin Maigatari da ke cikin Jigawa.

Shaidun gani da iso sun bayyana cewa daya daga cikin motocin da ke rakiyar Kakakin, Toyota Hilux ta ‘yan sanda, ce ta sauka daga titi, ta fara tunguragutsi a gefen hanya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262