zarge Zargen Rashawa: Cikakken Jerin Sunayen Ministocin Buhari da EFCC Ta Cafke

zarge Zargen Rashawa: Cikakken Jerin Sunayen Ministocin Buhari da EFCC Ta Cafke

Abuja - Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kara zurfafa bincike kan wasu manyan jami’an gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tun bayan sauyin gwamnati a 2023, hukumar ta mayar da hankali kan binciken zarge-zargen almundahana, amfani da ofis ba bisa ka’ida ba da kuma karkatar da kudaden gwamnati a wasu muhimman ma’aikatun tarayya.

EFCC na ci gaba da tuhumar wasu daga cikin ministocin Buhari
Tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari da allon hedikwatar hukumar EFCC, Abuja. Hoto: @MBuhari, @officialEFCC
Source: Twitter

Daga cikin wadanda ake bincike akwai tsofaffin ministoci masu rike da manyan mukamai a lokacin Buhari, ciki har da Timipre Sylva, Abubakar Malami da Hadi Sirika, kamar yadda BBC ta rahoto.

Ministocin Buhari da EFCC ta cafke

Legit Hausa ta yi nazari kan ministocin Buhari da EFCC take nema ruwa a jallo, ta cafke ko ta shiga kotu da su:

1. Chris Ngige

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: 'Yar Buhari ta fadi yadda ake amfani da sa hannun marigayin

EFCC ta cafke Chris Ngige kan zarge-zargen rashawa
Chris Ngige, tsohon ministan kwadago da samar da ayyuka, wanda EFCC suka cafke. Hoto: @SenNgige
Source: Twitter

Chris Ngige, tsohon ministan kwadago da samar da ayyuka shi ne ministan Buhari da a baya bayan nan hukumar EFCC ta cafke shi tare da gurfanar da shi gaban kotu kan zarge-zargen rashawa.

EFCC ta gurfanar da Ngige a gaban kotu bisa tuhume-tuhume takwas da suka hada da cin zarafin ofis da karbar kyaututtuka daga 'yan kwangilar asusun NSITF.

Ngige, wanda ya yi minista a gwamnatin Buhari har a wa'adi biyu, daga Satumbar 2015 zuwa Mayun 2023, ya musanta aikata dukkan tuhume-tuhumen.

Wata babbar kotun tarayya da ke da zamanta a Gwarinpa, Abuja ta ba da ajiyar tsohon ministan a gidan yarin Kudu a ranar 12 ga Disamba, har zuwa lokacin duba bukatar belinsa, kamar yadda Legit Hausa ta rahioto.

A ranar 18 ga Disamba, muka ruwaito cewa kotun ta amince da bukatar belin wucin-gadi da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta ba Ngige a baya.

Kara karanta wannan

Kotu ta gindaya sharudda masu tsauri kafin sakin Ministan Buhari, Ngige

2. Timipre Sylva

EFCC ta ayyana Timipre Sylva a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Timipre Sylva, tsohon karamin ministan man fetur da EFCC ke nema ruwa a jallo. Hoto: @HETimipreSylva
Source: UGC

Timipre Sylva, tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma tsohon karamin ministan man fetur, yana daya daga cikin ministocin da EFCC ke nema ruwa a jallo.

A lokacin Buhari, shugaban kasa ne ke rike da mukamin ministan man fetur, amma Sylva shi ne ke kula da harkokin yau da kullum na ma’aikatar, wacce ita ce tushen kudaden shiga mafi girma ga Najeriya.

A ranar 10 ga Nuwamba, EFCC ta ayyana Sylva a matsayin wanda ake nema bisa zargin almundahana da ya kai sama da dala miliyan 14, kwatankwacin Naira biliyan 21.

Hukumar ta ce wata kotun jihar Legas ta riga ta bayar da umarnin cafke shi tun ranar 6 ga Nuwamba, a cewar rahoton Legit Hausa.

A wancan lokaci, an bayyana cewa Sylva ba ya cikin Najeriya. Mai magana da yawunsa, Julius Bokoru, ya fitar da sanarwa yana mai cewa EFCC ba ta taba gayyatar Sylva a hukumance ba kafin ayyana shi a matsayin wanda ake nema.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi watsi da bukatar Malami, EFCC za ta ci gaba da tsare tsohon minista

Ya kara da cewa tsohon ministan yana kasar Birtaniya domin duba lafiyarsa, kuma zai mutunta duk wata gayyata da zarar ya kammala jinyar.

Mun ruwaito cewa lamarin Sylva ya kara daukar sabon salo bayan da EFCC ta je gidansa da ke Abuja, ta sanya jan fenti tare da rubuta “EFCC – KEEP OFF”, abin da ke nuna cewa an rufe ko an killace wurin domin bincike.

3. Abubakar Malami

Abubakar Malami na ci gaba da zama a hannun EFCC kan zarge-zargen rashawa.
Abubakar Malami, tsohon ministan shari'a da ke tsare a hannun EFCC. Hoto: @aamalamiSAN
Source: Twitter

Hukumar EFCC ta cafke Abubakar Malami, tsohon Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a, a wani mataki na ci gaba da bincike kan zarge-zargen da ke kansa.

Malami ya fito da kansa ya tabbatar da cewa hukumar ta gayyace shi domin amsa tambayoyi kan wasu dala miliyan 346.2 da kasar Switzerland ta mayar wa Najeriya, wanda aka ce wani bangare ne na kudaden da tsohon shugaban mulkin soja, Sani Abacha, ya wawure.

EFCC na zargin Malami da amfani da ofis ba bisa ka’ida ba, tare da hada-hadar wanke kudi, musamman wajen shigar da wasu kamfanonin lauyoyi cikin lamarin, duk da cewa gwamnatin tarayya ta kusa kammala tsarin dawo da kudin tun farko.

Kara karanta wannan

Labarin tsohon sakataren Buhari da ministoci da mukarraban gwamnati ke shakka

Malami ya musanta dukkan zarge-zargen, yana mai cewa hannunsa tsaf yake. Haka kuma, ya karyata ikirarin da wasu jaridu suka yi cewa ana zarginsa da daukar nauyin ta’addanci, yana mai cewa ba a taba bincikensa ko tuhume shi da irin wannan laifi ba a Najeriya ko waje.

Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa Malami ya na ci gaba da zama a hannun EFCC bayan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi fatali da bukatar beli da ya shigar gabanta.

A hukuncinsa, Mai shari’a Babangida Hassan ya goyi bayan EFCC, yana mai cewa kundin tsarin mulki da dokar ACJA sun amince da tsare mutum idan akwai sahihin umarnin kotu.

4. Hadi Sirika

Hadi Sirika da diyarsa sun gurfana gaban kotu bisa tuhume-tuhumen da EFCC ke yi masu.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da allon sanarwar hukumar EFCC. Hoto: @hadisirika, @officialEFCC
Source: Facebook

Hadi Sirika, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, yana fuskantar shari’a kan shirin kaddamar da jirgin saman Najeriya “Nigeria Air” a karshen mulkin Buhari.

Wannan shiri ya jawo ce-ce-ku-ce bayan gwamnatin Bola Tinubu ta bayyana cewa kamfanin ba mallakin Najeriya ba ne, har ma majalisa ta magantu a kai.

Ministan sufurin jiragen sama na yanzu, Festus Keyamo, ya bayyana cewa “Nigeria Air” ba komai ba ne illa jirgin Ethiopian Airlines da aka yi wa fenti da tambarin Najeriya, in ji wani rahoto na Punch.

Kara karanta wannan

Malami: EFCC ta kai samame gidan da 'yar marigayi Buhari ke zaune

EFCC na zargin Sirika da amfani da mukaminsa wajen bai wa ‘yarsa Fatima da surukinsa Jalal Hamma kwangiloli da ayyukan tuntuba a shirin, da kuma ba su wasu kwangiloli na gine-gine, ciki har da aikin fadada filin jirgin saman Katsina.

Kotu ta bayar da belin Sirika a kan Naira miliyan 100, yayin da shari’ar ke ci gaba, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.

5. Mamman Saleh

EFCC ta cafke Mamman Saleh, tsohon ministan makamashi kuma ta gurfanar da shi gaban kotu.
Tsohon ministan makamashi, Mamman Saleh da EFCC ta gurfanar gaban kotu. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Facebook

Mamman Saleh ya yi aiki a matsayin Ministan Makamashi a ƙarƙashin tsohon Shugaba Buhari, kuma EFCC ta cafke shi tare da gurfanar da shi kan zargin damfarar Naira biliyan 33.8, in ji rahoton ICRC.

Saleh, wanda Buhari ya naɗa a matsayin ministan makamashi a watan Agustan 2019, sannan aka sallame shi daga aiki a watan Satumbar 2021, yana fuskantar tuhume-tuhume guda 12 da hukumar EFCC ta shigar.

Hukumar EFCC, ta gurfanar da Mamman a watan Yulin 2024 bisa zargin haɗa baki da jami’an ma’aikatar da kamfanoni masu zaman kansu don karkatar da Naira biliyan 33.8i, kudaden da aka ware don ayyukan samar da wutar lantarki na Zungeru da Mambilla.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawar ta gabatar da shaidu 17 da kuma kayayyakin shaida guda 43 kafin ta kammala bayar da hujjojinta.

Kara karanta wannan

EFCC ta cafke bokaye da kudin kasashen waje na boge bayan damfarar 'yan Najeriya

Sai dai, Mamman ya musanta tuhume-tuhumen, inda ya bayyana cewa masu ƙara sun gaza gabatar da kwararan shaidu masu gamsarwa da za su kai ga yanke masa hukunci ko kuma tilasta masa yin kariya.

A cikin hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, 11 ga watan Disamba, Mai Shari’a James Omotosho ya yi watsi da wannan buƙatar ta Saleh, inda ya bayyana cewa masu ƙara sun kafa hujjoji masu ƙarfi da suka kamata tsohon ministan ya amsa tuhume-tuhumen da ake yi masa.

EFCC sun cafko Ngige a gidansa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an EFCC kusan 20 ne aka ce sun kutsa gidan tsohon ministan kwadago, Chris Ngige a Abuja, suka tafi da shi ofishinsu.

Fred Chukwuelobe, tsohon hadimin Ngige, ya ce jami'an hukumar yaki da cin hanci da rashawar ba su bari tsohon ministan ya sauya ko da kayan barcin sa ba.

A kwanakin baya ne aka bada Ngige “beli” bayan wata gayyata da EFCC ta yi masa, inda aka yi masa tambayoyi kan wasu batutuwa da ba a bayyana ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com