Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar Malami, EFCC Za Ta Ci gaba da Tsare Tsohon Minista

Kotu Ta Yi Watsi da Bukatar Malami, EFCC Za Ta Ci gaba da Tsare Tsohon Minista

  • Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi fatali da bukatar tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami na samun beli daga EFCC
  • Kotun ta yanke hukunci cewa hukumar EFCC na ci gaba da tsare Malami a karkashin doka, da kuma bin halastaccen umarnin kotu
  • Wannan na zuwa ne yayin da wata kungiya ta dura kan Malami, inda ta zarge shi da kin mutunta umarni kotu a lokacin da yake ofis

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi fatali da bukatar da ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya shigar yana neman a umarci EFCC ta sake shi.

A hukuncin da ya yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a Babangida Hassan, ya bayyana cewa EFCC na ci gaba da tsare Abubakar Malami ne bisa umarnin wata babbar kotu.

Kara karanta wannan

Kotu ta gindaya sharudda masu tsauri kafin sakin Ministan Buhari, Ngige

Kotu ta yi fatali da bukatar Abubakar Malami na ba da belinsa daga hannun EFCC.
Abubakar Malami, tsohon ministan shari'a da kotu ta hana EFCC ta ba da belinsa. Hoto: @aamalamiSAN
Source: Twitter

Zargin Abubakar Malami da martanin EFCC a kotu

Tsohon ministan, ta hannun lauyansa Sulaiman Hassan, ya roki kotu ta ba da shi beli, yana mai cewa ci gaba da tsare shi yayin da ake gudanar da bincike ya sabawa ‘yancinsa na dan Adam, in ji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malami ya ce babu hujjar da za ta tabbatar da tsare shi na tsawon lokaci, yana mai neman kotu ta ba da umarnin sakin sa nan take.

Sai dai lauyan EFCC, J.S. Okutepa, ya kalubalanci bukatar, yana mai cewa an tsare Malami ne bisa umarnin tsarewa da wata babbar kotu a Abuja ta bayar.

Okutepa ya bayyana cewa Mai shari’a S.C. Oriji ne ya bayar da umarnin tsare Malami, bisa tanadin Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuffuka (ACJA).

Ya kara da cewa EFCC ba za ta tsare kowane mutum fiye da lokacin da kotu ta amince ba, yana mai jaddada cewa duk matakan da hukumar ta dauka suna bisa doka.

Kara karanta wannan

Malami: EFCC ta kai samame gidan da 'yar marigayi Buhari ke zaune

Kotu ta yi fatali da bukatar belin Malami

A hukuncinsa, Mai shari’a Babangida Hassan ya goyi bayan EFCC, yana mai cewa kundin tsarin mulki da dokar ACJA sun amince da tsare mutum idan akwai sahihin umarnin kotu.

EFCC za ta ci gaba da tsare Abubakar Malami bayan hukuncin kotu.
Abubakar Malami, tsohon ministan shari'a da EFCC ke ci gaba da tsarewa. Hoto: @aamalamiSAN, @officialEFCC
Source: Twitter

Alkalin ya ce bukatar da Malami ya gabatar tana da matsala ta fuskar doka, domin tana neman kotu ta soke ko ta yi nazarin hukuncin wata kotu mai matsayi iri daya.

“Karbar wannan bukata zai sa wannan kotu ta zama kamar kotun daukaka kara kan hukuncin wata kotu mai matsayi iri daya,” in ji Mai shari’a Babangida.

Ya kara da cewa kotun ba ta da ikon yin hakan, don haka ta yi watsi da bukatar belin baki daya, in ji rahoton The Guardian.

Hukuncin kotun na nufin cewa Abubakar Malami zai ci gaba da kasancewa a hannun EFCC, har sai lokacin da umarnin tsarewarsa ya kare ko kuma wata kotu mai hurumi ta bayar da wani sabon umarni.

EFCC ta kai samame gidajen Malami

Kara karanta wannan

Abin da ya sa ake ganin ya kamata a daure kusan duka ministocin Buhari a gidan yari

A wani labari, mun ruwaito cewa, EFCC ta kai samame wani gida da ke da alaƙa da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami, a wani mataki da ya ja hankali.

An ce Nana Hadiza Buhari, matar Malami ta uku kuma ’yar tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, tana cikin gidan a lokacin da jami'an suka kai samamen.

Masu bincike sun kuma karkata hankalinsu kan wasu asusun banki da mu’amaloli na kuɗi da ake zargin suna da alaƙa da lokacin da Malami ya rike muƙamin Antoni Janar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com