Bidiyon yadda Aka Yi wa Ɗan Majalisar Zamfara Ruwan Duwatsu da Ihun 'ba Mu Yi'
- Ana zargin fusatattun mutane sun tayar da kura a garin Dansadau da ke Zamfara, bayan sun yi wa dan majalisar mazabarsu ature da duwatsu
- Mutanen sun zargi dan majalisar da rashin ziyartar mazabarsa, rashin jajanta wa wadanda hare-haren ‘yan bindiga suka shafa a yankin
- A cikin wani bidiyo da Legit Hausa ta samu, an ga yadda mutane suka rika jifar dan majalisar, har da marinsa, suna ihun 'ba ma yi'
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - An samu wasu fusatattun mutane da suka kai hari kan wani dan majalisar dokokin jihar bisa zargin gazawa wajen wakiltarsu da kuma yin watsi da al’ummar mazabarsa.
Rahotanni sun nuna cewa fusatattun mutanen sun yi wa dan majalisar, Kabiru Mikailu ruwan duwatsu, kasa da ihun 'ba ma yi' a garin Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Source: UGC
'Dan majalisa ya sha ruwan duwatsu a Zamfara
Channels TV ta rahoto cewa Hon Kabiru Mikailu, wanda ke wakiltar mazabar Maru ta Kudu a majalisar dokokin Zamfara, ya sha duka a hannun jama’a yayin da ya yi wa Gwamna Dauda Lawal rakiya a wata ziyara da ya kai yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa jama’ar yankin sun fusata matuka ganin dan majalisar, inda suke zarginsa da yin watsi da garin Dansadau tun bayan zabensa.
An ce 'dan majalisar bai kara waiwayar yankin Dansadau ba, kuma ba ya kai masu ko da ziyara ce, balle a yi maganar kai masu wani romon dimokuradiyya.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce Kabiru Mikailu bai halarci bukukuwan Sallah a garin ba, haka kuma bai kai ziyarar jaje ga iyalan mutanen da hare-haren ‘yan bindiga suka shafa a yankin ba, duk da yawaitar matsalolin tsaro da ake fama da su.
An ce jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma da kuma hana lamarin yin muni fiye da haka, amma bidiyo ya nuna yadda dan majalisar ya sha ruwan duwatsu, har da mari a gaban jami'an tsaron.
Ziyarar gwamna da ta jawo dukan 'dan majalisa
Gwamna Dauda Lawal ya kai ziyara Dansadau ne domin kaddamar da aikin sake gina titin Dansadau–Gusau mai tsawon kilomita 90, wanda ake ganin zai taimaka sosai wajen inganta harkokin sufuri da tattalin arzikin yankin.
A yayin ziyarar, gwamnan ya kuma bayar da umarnin sake gina da gyaran babban asibitin Dansadau, tare da samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana domin inganta rayuwar al’umma.
Gwamna Lawal ya jaddada kudirin gwamnatinsa na dawo da tsaro, sake gina muhimman ababen more rayuwa, da kuma inganta jin dadin al’ummomin da matsalar tsaro ta shafa a fadin Jihar Zamfara.
Sai dai, bayan kammala dukkan ayyukan da gwamnan ya je yi, sai fusatattun mutane suka hango Hon. Kabiru Mikailu, suka kuwa ce 'da wa Allah ya hada mu in ba da kai ba,' suka rufe shi da jifa da duka.
Kalli bidiyon a kasa:
Mutane sun yi martani kan bidiyon

Source: Original
Legit Hausa ta tattaro ra'ayoyin mutane a kan wannan bidiyo na aturen dan majalsa, wanda wani Mai-Islam Bukkuyum ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa Buhari ya sauya fasalin Naira daf da zaɓen Tinubu a 2023
Bilyaminu Hassan Bukkuyum:
"Wallahi tallahi saura Matawallen Maradun."
Abdullahi Garba Marmaro
"Alhamdullahi, hayaƙi fidda na kogo. Wallahi Mai Islam duk bala'in da muke ciki a Arewa, matasan Arewa suka jawo mana shi, don suke ba azzalumai kariya da sunan iyayen gidan siyasa."
Hon Lauwali Aliyu Gummi:
"Yadda kun kaga wanga dan majalisar ya sha kashi yau, wallahi duk kaddarar Allah da ta sa Bello Matawalle karamin minista yattai Dansadau wallahi sai ya sha fiye da shi, balle ma gashi yanzu suna haushi da shi tunda an ce ya na goyon bayan ta’addanci."
Adam Sa'id Palladan:
"Lallai mutane sun fara waye wa."
Usman B Tela:
"Allah ya kara hada kan talakan najeriya, godiya mu ke mutanen Zamfara."
Sagir Aliyu Abdullahi:
"Bai daku ba wallahi, ai da kun ba shi kashi sosai tunda ba shi da amfani."
Nasiru Aliyu:
"Allah ka isar mana ga azzaluman shugabanni marasa amfani. Amma wwallahi hakan bai kamata ba, ka dubi yanda wannan ya mare shi, ko bai haifaiba ya yi kane da shi. Allah ya sawaka, Allah ka mana mafita ta alheri ba don halin mu ba."
Abbas Sabo:
"Kallon fina finan Indiya ya sa 'yan Najeriya sun fara wayewa, ya kamata a cikin 'yan sanda mu samu Singham."
Matasa sun rufe shugaban kasa da jifa
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu fusatattun mutane kimanin 500 sun kewaye motar shugaban ƙasar Ecuador, Daniel Noboa, inda suka yi masa ruwan duwatsu.
Shugaban ƙasa Daniel Noboa, ya tsira daga wannan yunƙurin kai masa hari da fusattun masu zanga-zanga suka yi a yankin Canar da ke tsakiyar ƙasar ta Ecuador.
Gwamnatin kasar ta fitar da sanarwa bayan harin, in da ta bayyana cewa duk wanda aka kama cikin lamarin zai fuskanci tuhuma ta ta’addanci da kuma yunƙurin kisan kai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


