Yayan APC sun yi ma gwamnan jahar Zamfara ruwan duwatsu a Gusau

Yayan APC sun yi ma gwamnan jahar Zamfara ruwan duwatsu a Gusau

Gwamnan jahar Zamfara, Abdul Aziz Yari ya tsallake rijiya da baya yayin da wasu matasa suka yi ma ayarin motocinsa ruwand duwatsu a garin Gusau, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gwamnan ya bayyana cewar yayan jam’iyyar APC dake adawa da shi ne suka jefeshi a daidai shataletalen Lalan dake garin Gusau a yayin dayake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna a ranar Lahadi, 16 ag watan Satumba.

KU KARANTA: Sheikh Nakaka ya zama sabon shugaban majalisar Malamai da Limamai ta Kaduna

Yayan APC sun yi ma gwamnan jahar Zamfara ruwan duwatsu a Gusau
Ayarin motocin gwamnan jahar Zamfara
Asali: Depositphotos

Sai dai ana zargin wadanda suka jefi gwamnan magoya bayan abokan hamayyar gwamnan ne na cikin gida, kuma hakan ya faru ne a daidai lokacin da manyan yan siyasa bakwai dake neman kujerar gwamnan suka shirya gangami a Gusau, ciki har da mataimakin gwamnan jahar Wakkala.

A yayin da ake cikin wannan gangami ne sai ayarin motocin gwamna Yari suka yi kicibus da dafifin mutanen, inda nan take aka shiga jefa masa duwatsu, hakan yasa aka fasa gilasan motoc da dama.

Amma ba tare da bata lokaci bane yansandan kwantar da tarzoma suka shiga harba bindiga a sama, wanda hakan ya fatattaki jama’a, tuni jama’a sun waste kuma hankula sun kwanta a garin Gusau.

Shima gwamnan jahar ta bakin mai magana da yawunsa, Ibrahim Dosara yayi kira ga magoya bayansa da kada su dauki fansa game da abinda yan adawa suka yi masa, sa’annan yayi kira ga jama’an jihar da su guji dukkanin wasu ayyukan tada hankali.

Daga karshen gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi kokarin gaske wajen hana matasa shiga cikin ayyukan da ka iya janyo tashe tashen hankula a jahar, musamman a tsakanin jam’iyyu da yan siyasa, sa’annan ya bukaci yan siyasa su wayar da kawunan mabiyansu game da muhimmancin zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel