2027: An Gyara Dokokin Zaben Najeriya a Zauren Majalisar Wakilai

2027: An Gyara Dokokin Zaben Najeriya a Zauren Majalisar Wakilai

  • Majalisar wakilai ta amince da wasu muhimman gyare-gyare a dokar zaɓe domin ƙarfafa INEC da rage matsalolin da ke tasowa bayan zaɓe
  • An yanke shawarar sauya wasu sassa da suka shafi shari’o’in kafin zaɓe, cancantar ’yan takara da kuma hukunci kan yin maguɗin zaɓe
  • Muhawara ta yi zafi kan batun hana ’yan takara da jam’iyyunsu rike tutar jam'iyya idan an kama su da bayar da bayanan ƙarya a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta ƙara ɗaukar matakai domin sake fasalin tsarin dokokin zaɓe a Najeriya, bayan amincewa da jerin gyare-gyare a kudirin gyaran dokar zaɓe.

Gyare-gyaren da aka amince da su sun mayar da hankali ne kan ƙarfafa ikon hukumar INEC, fayyace hanyoyin gudanar da zaɓe, da sauransu.

Kara karanta wannan

An fara martani kan sabon takunkumin da Trump ya kakabawa wa Najeriya

Zauren majalisar wakilai
'Yan majalisar wakilai yayin muhawara. Hoto: Abbas Tajudeen
Source: Facebook

Yadda aka tattauna kudirin dokar zabe

Premium Times ta rahoto cewa matakin ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin majalisar kan harkokin zaɓe, wanda shugabansa, Adebayo Balogun, ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan gabatar da rahoton, majalisar ta fara tattauna shi, inda mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Kalu, ya jagoranci tattauna sashe-sashe na kudirin.

’Yan majalisar sun yi nazari kan kowanne sashe, suka amince da gyare-gyare masu yawa da nufin ƙara gaskiya, inganta gudanar da zaɓe da rage rigingimun bayan zaɓe.

Dokoki game da shari'a kafin zabe

Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka amince da su shi ne batun ikon sauraron shari’o’i kafin gudanar da zaɓe.

Vanguard ta rahoto cewa majalisar ta yanke matsaya cewa dole irin waɗannan shari’o’i su kasance ƙarƙashin Kotun Tarayya ta jihar da abin ya shafa.

A cewar Balogun, an kawo wannan tanadi ne domin dakile dabi’ar kai ƙara zuwa wuraren da ba su da alaƙa kai tsaye da shari’ar, lamarin da ke janyo jinkiri da ruɗani.

Kara karanta wannan

'Buhari ya yi zargi ana bibiyarsa': 'Yarsa ta fadi yadda suke magana a boye a Aso Rock

'Yan Najeriya a lokacin zabe
Mutane a layin kada kuri'a a lokacin wani zabe. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

’Yan majalisa sun nuna cewa wannan mataki zai taimaka wajen hanzarta yanke hukunci da rage wahalar da jam’iyyu da ’yan takara ke fuskanta.

Wasu dokokin zabe da aka gyara

Majalisar ta amince da tsauraran hukunci kan maguɗin zaɓe, inda duk jami’in INEC da ya ayyana sakamakon ƙarya zai fuskanci ɗaurin shekaru biyar a gidan yari.

Haka kuma, rashin rubuta sakamako a takardar da doka ta tanada bayan ayyana shi zai janyo hukuncin ɗaurin shekaru 10.

Majalisar ta amince da sashe-sashe na 10 da 12 domin ƙarfafa ikon INEC wajen shirya zaɓe, kula da kayan aiki da tura ma’aikata.

Baya ga haka, an amince da hukuncin ɗaurin shekaru biyu ga duk kwamishinan zaɓe na jiha da ya ƙi fitar da sahihin kwafin sakamakon zaɓe idan an buƙata.

An kuma gyara sashe-sashe da suka shafi rajistar masu zaɓe, fidda sunayensu, gudanar da fidda gwani a jam’iyyu, tantance ’yan takara, da amfani da fasaha wajen zaɓe.

Kara karanta wannan

An fara gunaguni bayan mai tsaron Tinubu ya zama Birgediya Janar a soja

MURIC ta nemi sauke shugaban INEC

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar nan mai rajin kare hakkin Musulmi a Najeriya, MURIC ta nemi a sauke shugaban INEC.

MURIC ta bukaci sauke sabon shugaban hukumar ne bayan wata takarda da ta rubuta yana cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya.

Shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya ce bai dace wanda zai rubuta bayanan da ba gaskiya ba ne ya shugabanci hukumar INEC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng