Ganawar Ladanin Masallacin Kano Ta Karshe da Iyalinsa gabanin Kashe Shi

Ganawar Ladanin Masallacin Kano Ta Karshe da Iyalinsa gabanin Kashe Shi

  • Matar Malam Zubairu, Ladani da ake kashe a unguwar Hotoro a Kano ta bayyana gani na karshe da ta yi wa Maigidanta kafin samun labarin rasuwarsa
  • Ta bayyana cewa sun hadu ne a rijiya yayin da yake shirin debo ruwan alwala domin kiran sallar Asuba, kamar yadda ya saba a kowace rana
  • Ta bayyana cewa bayan fitar Maigidanta, sai ta ji shiru bai kira Sallah ba, wanda ya sa ta fito domin sake alwala, amma ta ji ihun neman taimako

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Daya daga cikin matan Malam Zubairu Ladanin da aka kashe a Unguwar Hotoro a Kano, ta fito ta yi cikakken bayani kan yadda safiyarsa ta karshe ta gudana kafin rasuwarsa.

Kara karanta wannan

'Buhari ya yi zargi ana bibiyarsa': 'Yarsa ta fadi yadda suke magana a boye a Aso Rock

Ta shaida cewa sun haɗu da Asuba a tsakar gida bayan ta ji fitowarsa a lokacin da yake shirin ɗaura alwala domin kiran Sallah.

Matar Ladani ta fadi maganarta ta karshe da mijinta
Ladanin Kano da aka kashe, Malam Zubairu, a gefe kuma mutanen unguwa bayan daukar fansa Hoto: Hon Umar Mai Wayo
Source: Facebook

A hirar da ta yi da Premier Radio, wadda aka wallafa a shafin Facebook, an ce sun haɗu ne a kusa da rijiya yayin da yake ƙoƙarin jawo ruwan alwala a Unguwar ta su Hotoro a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganawar karshe na Ladanim da matarsa

Matar ladanin Kano ta ƙarshe, wadda ita ce Mai ɗakin Ladanin, ba a bayyana sunanta a bidiyon ba, ta bayyana cewa bayan ta ga yana ƙoƙarin jawo ruwa daga rijiya, sai ta karɓa ta jawo masa.

A kalamanta:

"Shi Ladani ne, ya tashi da safe da Asuba din zai tafi masallaci, sai ni ma na fito, da na fito, muka hadu a rijiya na ga zai ja ruwa, na ce ruwa za ka je? Ya ce e, na karba na jawo masa."

Ta ƙara da cewa:

"Sai ya shiga bandaki, ni kuma dama na riga na yi alwala, sai na shiga daki, ya yi alwala ya fita."

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya yarda matarsa, Aisha za ta kashe shi a Aso Rock Villa

Ta kuma ce:

"Da ya fita, ya je ya yi kiran Sallah na farko. Ya gama kiran sallah ni dai ina kwance, ba wai barci na ke yi ba."

Yadda matar Ladani ta samu gawar mijinta

Game da yadda ta samu gawar mijinta, matar ta bayyana cewa bayan ta lura lokacin Assalatu ya yi amma ba ta ƙara jin kiran sallar mijinta ba, sai ta fito domin ƙara alwala.

A nan ne ta fara jin ihun neman taimako, inda ta ce:

"Sai na ke jin ihu, wayyo Allah jama'a ku taimake ni, jama'a ku taimake ni." Ta ƙara da cewa ta ɗauka barawo aka kama: "Sai na ke cewa abokiyar zama na barawo aka kama, sai na kasa alwala, na tashi zan tafi, ta ce ba za ki yi alwala ba, na ce kyale ni."
Matar Ladani ta ce sun samu mijinsu ba ya motsi
Taswirar Jihar Kano, inda aka kashe Ladani Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ta ci gaba da cewa:

"Sai na fita kofar zaure, sai na ga makocinmu ya dawo, yana dawowa ya bude gidan shi ya dauki gora. Na tambaye shi Baban Wasilu mai ya faru? Bai kula ni ba, sai 'dana Uzairu shi ma ya fito da gudu, ya bi Baban Wwasilu, ni kuma da na shigo gida na kasa samun nutsuwa, sai na dau hijabi a igiya, sai na bi su."

Kara karanta wannan

"An san maboyarsa": Masanin tsaro ya yi magana kan kama Bello Turji

"Ina binsu makociyarmu ta ce an kashe Baba, na ce wane Baban? Sai ta fuskanta ban gane ba, ni kuma na san yana masallaci, sai na nufi hanyar masallaci, ina zuwa masallaci na gan shi a cikin jini. An yanke masa gefen wuyanshi, yanka sosai yadda kika san ana yanka dabba. Na je na tarar ma baya motsi."

Ta bayyana cewa bayan wannan mummunan lamari, ta koma gida inda ta sanar da abokiyar zamanta cewa an kashe maigidansu ne, ba wai barawo aka kama ba.

An yi wa ladani yankan rago a Kano

A baya, mun wallafa cewa an shiga firgici da tashin hankali a unguwar Hotoro Maraba da ke birnin Kano, bayan wani matashi ya kashe ladanin masallaci a lokacin sallar Asuba da safiyar ranar Litinin.

Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da Asubah, lokacin da matashin ya je masallaci domin yin sallah, inda ya tarar da ladanin tare da wasu mutane uku a cikin masallacin.

Bisa bayanan da aka samu, matashin ya nemi a tayar da sallah, amma ladanin ya sanar da shi cewa lokacin sallar Asuba bai yi ba tukuna, kuma nan take ya zaro wuka, ya jawo shi, ya yanka shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng