An Jero 'Zunuban' da Marigayi Buhari Ya Aikata a Mulkinsa daga 2015 zuwa 2023

An Jero 'Zunuban' da Marigayi Buhari Ya Aikata a Mulkinsa daga 2015 zuwa 2023

  • Kungiyar Amnesty International ta soki marigayi Muhammadu Buhari, tana zarginsa gwamnatinsa da take haƙƙin ɗan Adam
  • Masu kare hakkin jama'an sun ta tuno kisan kiyashin ’yan Shi’a, kashe masu zanga-zangar Biafra, da murkushe zanga-zangar #EndSARS
  • Amnesty ta kuma zargi gwamnatin Buhari da tsangwama ga ’yan jarida, masu kare haƙƙin ɗan Adam, da cin zarafin mata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar Amnesty International ta soki gwamnatin Muhammadu Buhari kan take hakkin dan Adam.

Marigayi Buhari da ya rasu a watan Yulin 2025 a London ya mulki Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2023.

An zargi gwamnatin Buhari da kisan kiyashi
Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Abubuwan da Amnesty ke zargin Buhari da su

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin kungiyar da ta wallafa a shafin Facebook a daren jiya Litinin 15 ga watan Disambar 2025.

Kara karanta wannan

Manyan badakalolin siyasa 5 da suka faru a shekarar 2025 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta ce Buhari ya ci zarafin yan jaridu da tauye hakkin yan Adam wanda ya jawo asarar rayuka da dama.

Har ila yau, kungiyar ta tuna irin kisan kiyashi da aka yi wa 'yan Shi'a a Zaria da ke jihar Kaduna lokacin mulkin Nasir El-Rufai.

Sanarwar ta ce:

"Muhammadu Buhari ya mulki Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2023. akwai wasu daga cikin manyan keta haƙƙin ɗan Adam da aka samu a lokacin mulkinsa."

Daga abubuwan da ta jero akwai:

1. Kisan kiyashin 'Yan shi'a a Zaria (Disamba, 2015)

Ta ce sojojin Najeriya sun kashe fiye da mutane 350 maza, mata da yara a Zaria, an yi wannan kisan kimanin shekaru 10 da suka wuce inda sojoji suka yi ƙoƙarin rufe laifin.

Rahoton Amnesty International ya nuna cewa an ƙone mutane da ransu, an rushe gine-gine, an kuma jefa gawarwaki a kaburburan jama’a, babu wanda aka hukunta.

Kara karanta wannan

Yadda hadiman Buhari suka so ayyana Ahmad Lawan a matsayin dan takarar APC a zaben 2023

2. Kisan gilla ga masu zanga-zangar Biafra

Jami’an tsaro sun aiwatar da kashe-kashe ba tare da shari’a ba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 150 daga cikin masu zanga-zangar neman kafa Biafra.

Mafi muni ya faru ne ranar 30 ga Mayu, 2016, lokacin da akalla mambobi da magoya bayan IPOB 1,000 suka taru a Onitsha, jihar Anambra.

3. Rikicin manoma da makiyaya:

Gazawar gwamnatin Buhari wajen hukunta masu laifi ta ƙara ta’azzara rikicin manoma da makiyaya, inda aka samu akalla mutuwar mutane 3,641 cikin shekaru uku.

An samu hare-hare akalla 310 tsakanin Janairu 2016 zuwa Oktoba 2018, musamman a jihohin Adamawa, Benue, Kaduna, Taraba, Plateau da Zamfara.

4. Tsangwama ga ’yan jarida:

Ta ce a lokacin Buhari, an kama, an tsoratar da gallaza wa ’yan jarida bayan an kai hari ko tsangwama ga akalla ’yan jarida 19 tsakanin Janairu da Satumba 2019.

Wasu uku sun tsere sun ɓuya, haka kuma, jami’an tsaro sun kai samame ofisoshin Daily Trust da Premium Times.

Kara karanta wannan

"Ba zan taba komawa APC ba," Sanata ya yi kaca kaca da gwamnoni 6 a Najeriya

Amnesty ta tuno mulkin Buhari da ta ce na zalunci ne
Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad.
Source: UGC

5. Murkushe zanga-zangar #EndSARS (2020):

Zanga-zangar lumana ta #EndSARS da ke neman kawo ƙarshen ta’addancin rundunar SARS ta ’yan sanda ta gamu da kisan gilla.

Akalla mutane 56 aka kashe a faɗin ƙasa, ciki har da akalla mutane 12 a Lekki Toll Gate da Alausa ranar 20 ga Oktoba, 2020.

6. Cin zarafin mata da rikicin Boko Haram ya rutsa da su:

Dubban mata da ’yan mata da suka tsira daga Boko Haram sun sake fuskantar cin zarafi daga jami’an tsaro da CJTF, inda aka yi musu fyade, wasu lokuta wajen musayar abinci.

7. Tsangwama ga masu kare haƙƙin ɗan Adam:

An kama Omoyele Sowore, Olawale Bakare da Agba Jalingo ba bisa ka’ida ba a watan Agusta 2019 saboda sukar gwamnati.

Hukumar DSS ta ƙi bin umarnin kotu na sakin Sowore da Bakare, yayin da aka ci gaba da ƙin amincewa da belin Agba Jalingo ba tare da hujja ba.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari ya yarda matarsa, Aisha za ta kashe shi a Aso Rock Villa

Aisha ta fadi silar rashin lafiyar Buhari

An ji cewa Aisha Buhari ta ce ba guba ba ce ta jawo rashin lafiyar da ta kai shugaba Muhammadu Buhari jinyar kwanaki 154 a 2017 London.

Ta bayyana cewa jita-jita a fadar Aso Rock sun jawo tsaiko da katse shan magani da aka saba ba shi a lokuta na musamman.

Bayanan Aisha Buhari sun fito ne daga wani sabon littafin tarihin marigayin da aka ƙaddamar a fadar shugaban kasa a Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.