Sai fa an raba kasar nan Inji Nnamdi Kanu

Sai fa an raba kasar nan Inji Nnamdi Kanu

– Kwanan baya Kotun Tarayya ta bada belin jagoran Biyafara Nnamdi Kanu

– Daga fitowar ya shiga kai ziyara wajen manyan Inyamurai na kasar

– Sai dai har yanzu fa Nnamdi Kanu na kan bakar sa

Nnamdi Kanu yace dole a raba Najeriya.

Kanu na neman kasar Biyafara mai cin gashin kan-ta.

Duk da ya sha matsa har yanzu bai fasa ba.

Sai fa an raba kasar nan Inji Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu yace sai an raba Najeriya

Sai kwanaki Nnamdu Kanu wani jagora na tafiyar Biyafara ya samu ya bar gidan kaso bayan mai shari’a Binta Nyako ta bada belin sa ko da an zuba sharudda masu tsauri kwarai da gaske. Nnamdi Kanu dai ya dade a tsare a gidan yarin Kuje.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya dauki hayar manyan Lauyoyi

Sai fa an raba kasar nan Inji Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu a gidan rediyon BIyfara kwanaki

Shugaban kungiyar na IPOB mau fafutukar neman kasar Biyafara mai zaman kan-ta yace har yanzu yana kan bakan san a cewa sai an raba kasar Ibo daga Najeriya. Kanu yayi wannan maganar ne bayan ya kai wata ziyara.

Nnamdi Kanu ya ziyarci wata Majalisar kasar Ibo watau ECA a Garin Enugu. An dai haramtawa Kanu zama cikin taron Jama’a da kuma yin hira da ‘yan jarida ko tada wani taro.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An zabi matashi a kasar Faransa

Asali: Legit.ng

Online view pixel