Yan shi’an Najeriya sun nuna ma kasar Amurka yatsa game da kisan kiyashi da aka musu a Zaria

Yan shi’an Najeriya sun nuna ma kasar Amurka yatsa game da kisan kiyashi da aka musu a Zaria

Mabiya addinin shia’a dake Najeriya sun yi ma ofishin jakadancin kasar Amurka daker Najeriya tsinke a babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, inda suka zargi Amurka da hannu cikin kisan kiyashin da suka ce an musu a garin Zaria.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jagoran shirya zanga zanga, Mohammed Musa ne ya bayyana haka a gaban ofishin jakadancin kasar Amurkan, inda yace Amurka na yaudarar duniya da cewa wai tana kare yancin dan adam bayan itace kan gaba wajen aikata aika aika a duniya.

KU KARANTA: Dangote ne kan gaba a tsakanin attajirai mafi arziki a cikin bakaken fata

Yan shi’an Najeriya sun nuna ma kasar Amurka yatsa game da kisan kiyashi da aka musu a Zaria
Yan shi’a
Asali: UGC

Yan shi’an sun yi ma ofishin tsinke ne dauke da takardu masu kunshe da sakonni daban daban dake bayyana ra’ayinsu game da kasar Amurka, tare da rera wakokin goyon baya ga jagoransu Ibrahim Zakzaky.

Har ila yau, sakataren kungiyar, Mohammed Musa ya bayyana damuwarsa da rawar da Amurka ta taka yayin da Sojojin Najeriya suka far ma yan shia’a a garin Zaria na jahar Kaduna, inda suka ce an kashe sama da yan shia 1000, tare da jikkata wasu da dama.

“An binne mutanenmu sama da dubu daya a lokaci guda, wasunsu ma da ransu, ana ji suna kiran ‘ina da rai’ ‘ina da rai’, amma gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufai a karkashin umarnin gwamnatin kasar Amurka yasa Sojojin Najeriya suka binnesu.

“Kisan da aka mana a Zaria shine babban cin zarafin da aka taba yi ma dan Adam a nahiyar Afirka gaba daya, kuma ta tabbata Amurka ce ta dauki nauyin wannan kisa, kuma ita take kitsa duk wani kashe kashe da ake yi a Najeriya.” Inji shi

Daga karshe kungiyar ta jaddada manufarta na cigaba da gwagwarmayan neman adalci tare da ganin gwamnatin Najeriya ta sako mata jagoranta, Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenatu Zakzaky.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel