EndSARS: Abubuwa 5 da IGP ya sanar yayin soke rundunar SARS
- Rundunar 'yan sandan Najeriya karkashin Sifeta Janar Mohammed Adamu ta kafa tarihi
- A yau Lahadi, 11 ga watan Oktoba ne shugaban 'yan sandan ya sanar ya rusa rundunar SARS
- Ya ce za a kafa kungiyar bincike ta musamman a kan cin zarafin da jami'an ke yi wa jama'a
Hukumar 'yan sandan Najeriya a ranar Lahadi, 11 ga watan oktoban 2020, ta ji koken jama'a inda sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya soke runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami (SARS).
Rusa rundunar wacce shugaban 'yan sandan Najeriya ya sanar a jawabin da yayi ga 'yan kasa, babu shakka ya kafa tarihi.
Hakan ya biyo bayan gagarumin zanga-zanga da matasan Najeriya suka dinga yi tun daga ranar Alhamis da ta gabata.
Muhimman abubuwa a cikin sanarwar shugaban 'yan sandan sun hada da:
1. An rushe dukkan rundunar SARS a fadin jihohi 36 da birnin tarayya tun daga yau
Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya rushe dukkan runduna ta musamman ta 'yan sanda masu yaki da fashi da makami a fadin Najeriya.
2. Dukkan jami'an 'yan sandan da ke rundunar SARS za a sauya musu wuraren aiki
Sifeta janar na 'yan sandan ya ce dukkan jami'an da ke karkashin rundunar za a sauya musu wurin aiki.
3. Ana shirya sabon tsarin 'yan sanda
IGP Adamu ya kara da cewa ana shirya sabon shirin 'yan sanda na yaki da fashi da makami tare da sauran miyagun laifuka.
4. Shirya zauren tattaunawa da tsari na masu ruwa da tsaki
Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya ce ana shirya kaddamar da zauren 'yan kasa da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa.
5. Za a kaddamar da kungiyar bincike a kan cin zarafin da 'yan sandan suke wa jama'a
Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya ce za su fara binciken dukkan cin zarafin da ake zargin 'yan sandan da shi.
KU KARANTA: Zaben Ondo: Akeredolu ya lallasa Jegede a sakamakon kananan hukumomi 12
KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke mace mai ciki wata 9 da wasu matasa 2 a kan fashi da makami
A wani labari na daban, Wasu 'yan daba wadanda har yanzu ba a gano su waye ba, sun soka wa wani matashi wuka yayin da ake rumfar zabe a garin Akure da ke jihar Ondo.
Kamar yadda mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar ya tabbatar wa da Channels TV, matashin ya tashi kuma ya bayyana wa jami'an tsaro abinda ya faru.
Mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar, Lanre Bankole, ya ce ana kan bincike kuma za a bankado masu hannu a cikin aika-aikar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng