'Yan Bindiga Sun Tarwatsa Fulani Makiyaya da Harbi, an Sace Shanu 168 a Filato

'Yan Bindiga Sun Tarwatsa Fulani Makiyaya da Harbi, an Sace Shanu 168 a Filato

  • Wasu 'yan bindiga sun kai hare-hare biyu a yankunan jihar Filato inda aka kashe fiye da shanu 160 bayan harbin makiyaya
  • Shugaban kungiyar MACBAN a jihar ya ce ya sanar da hukumomin tsaro nan take bayan faruwar lamarin domin a dauki mataki
  • Wani shugaba a kungiyar matasan Berom ya yi magana ga manema labarai game da harin da aka kai tare da sace shanun

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Rahotanni sun tabbatar da kai hare-hare kan makiyaya a Barikin Ladi da Jos ta Gabas, lamarin da ya haifar da sace shanu kimanin 168 tare da tarwatsa makiyayan da ke kiwo a yankunan.

Shugaban kungiyar MACBAN a jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya shaida wa manema labarai cewa hare-haren sun faru ne a ranar Laraba da yamma, inda aka yi awon gaba da dabbobi da dama.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 5 sun hada baki, sun gano hanyar kawo karshen 'yan bindiga gaba daya

Wasu shanu a wajen kiwo
Makiyaya tare da shanu suna kiwo. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kungiyar matasan Berom ta yi magana game da harin tare da neman a bar jami’an tsaro su gudanar da bincike cikin gaskiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kai wa makiyaya hari a Barikin Ladi

Ibrahim Yusuf Babayo ya bayyana cewa harin farko ya auku ne a yankin al’ummar Nding da ke yankin Fan a Barikin Ladi, inda aka sace shanu 137.

Ya ce ‘yan bindigan sun afka wurin kiwo suna harbe-harbe, abin da ya tilasta makiyaya tserewa domin kare rayukansu, yayin da masu harin suka tsere da dabbobin.

“Ranar 10 ga Disamba ne ‘yan bindiga suka mamaye wuraren kiwo suka fara harbi,”

- in ji Babayo

The Nation ta rahoto ya kara da cewa:

“Hare-haren biyu duk sun faru a rana guda, kuma mun sanar da DSS, Operation Enduring Peace, da ‘yan sanda nan take.”

An sace shanun Fulani a Jos ta Gabas

A karo na biyu, Babayo ya ce an kai hari a Kukhkah da ke karamar hukumar Jos ta Gabas, inda aka kwashe wasu shanu 34, sai dai uku daga cikinsu sun dawo gida daga baya.

Kara karanta wannan

Abin da Kiristoci suka fadawa dan majalisar Amurka da ya ziyarce su a Najeriya

Ya bayyana cewa shanun da aka sace mallakar mutane uku ne, Alhaji Wada Sale, Abdullahi Yusuf, da Alhaji Talba Abubakar.

Shugaban MACBAN din ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa makiyaya suna gudanar da sana’arsu ta halal, amma wasu bata-gari na neman tayar da hankula da kawo rashin zaman lafiya a yankin.

Martanin Berom kan sace shanu a Filato

A bangare guda, shugaban BYM, Barrister Solomon Dalyop, ya ce ba su samu wata shaida da ke nuna an sace shanu a Nding ba.

Shugaban ya ce al’ummar yankin Fan sun sha bayyana cewa ba su da filin kiwo, don haka Fulani su guji kiwo a yankunansu.

Gwamnan jihar Filato a ofis
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang. Hoto: Plateau State Government
Source: Twitter

Ya kara da cewa binciken da kungiyar ta gudanar bai tabbatar da sace shanu ba, yana mai kira da a bar jami’an tsaro su gudanar da bincike don sanin gaskiya.

Mataimakin jami'in hulda da jama’a na runduna ta 3, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce za a sanar da kwamandan sashen da kuma sashen leken asiri.

An kashe Musulmai 4,700 a jihar Filato

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar JCDA a Filato ta ce an kashe Musulmai kimamin 4,700 a sassan jihar.

Shugaban kungiyar ne ya bayyana haka yayin wani taron addu'ar tunawa da wadanda aka kashe a rikice-rikicen Filato.

Ya lissafo lokutan da aka kashe Musulmai ciki har da harin ranar sallah da kisan matafiya wurare mabanbanta na jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng