‘Abin da Ya Sa na Hana Biyan Kujerar Makkah a Mulkina’: Tsohon Gwamna

‘Abin da Ya Sa na Hana Biyan Kujerar Makkah a Mulkina’: Tsohon Gwamna

  • Tsohon Gwamna a Najeriya ya fadi dalilin dakatar da daukar nauyin Musulmi da Kiristoci zuwa Makkah da Jerusalem
  • Dattijon ya ce ya fi ganin muhimmancin karkatar da kuɗin zuwa ilimi da kayan makarantu domin ingnanta rayuwar mutane
  • Ya ce ya biya kuɗin WAEC ga ɗalibai, ya samar da kujeru da tebura, ya kuma yi ayyukan karkara ba tare da kawo ma’aikata daga waje ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abeokuta, Ogun - Tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Cif Olusegun Osoba, ya bayyana dalilin da ya sa ya dakatar da tallafin da gwamnatin jiha ke ba Musulmi da Kirista.

Osoba yana magana ne kan tallafi ga mahajjata zuwa Makka da Jerusalem a lokacin mulkinsa daga 1999 zuwa 2003.

Tsohon gwamna ya fadi dalilin hana daukar nauyin mahajjata a mulkinsa
Tsohon gwamnan Ogun, Olusegun Osoba. Hoto: Senator Solomon Olamilekan Adeola.
Source: UGC

Tsohon gwamna ya fifita ilimi kan komai

Rahoton Vanguard ya ce Osoba ya karkatar da kuɗaɗen zuwa bangaren ilimi da gyaran rayuwar al'umma.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan bukatar Nnamdi Kanu ta a dauke shi daga gidan yarin Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osoba ya ce abin ya dame shi ƙwarai ganin yadda ɗalibai a makarantun gwamnati ke kwasar tebura da kujeru daga gidajensu, kana kuma ƙwararrun ɗalibai da dama ba sa iya rubuta jarrabawar WAEC saboda iyayensu ba su iya biyan kuɗi ba.

Ya ce:

“Lokacin da na hau mulki a 1999, abin ya bani haushi ƙwarai ganin ɗalibai na ɗaukar tebura daga gida, sannan wasu dalibai ba sa iya rubuta WAEC saboda rashin kuɗi.”
Tsohon gwamna ya fifita ilimi kan biyawa Musulmi da Kirista zuwa bauta
Tsohon gwamnan jihar Ogun a Najeriya, Cif Olusegun Osoba. Hoto: Michael Olatunji.
Source: Facebook

Osoba ya hana biyan kudin zuwa Makkah, Isra'ila

A cewarsa, maimakon a kashe kuɗin jama’a wajen aikin hajji na Musulmi da tafiyar Kirista zuwa Jerusalem, ya fi son a saka kudin a ilimi ta hanyar samar da tebura da kujeru a makarantu.

Ya kara da cewa:

“Na gaya musu cewa maimakon kashe kuɗi a kan mahajjata, ko Musulmi ko Kirista, bari mu dakatar da hakan domin mu yi teburori. Na biya kuɗin WAEC na dukkan ɗalibai. Ko iyayenka suna da hali ko ba su da shi, gwamnati ta biya.”

Kara karanta wannan

Iyalai za su ɗasa, Shettima ya kaddamar da shirin tallafin N1bn ga ƴan kasuwa

Osoba ya yi kira ga gwamnati a kowane mataki ta rungumi tsarin ci gaba mai ɗorewa, yana mai cewa rashin hakan yana kawo cikas wajen cigaban Najeriya.

Haka kuma ya bukaci ‘yan Najeriya su koma noma don dogaro da kai, tare da shawartar gwamnonin jihohi su zuba jari sosai a harkar noma don yaƙar rashin abinci.

Yayin da yake tunawa da shugabancinsa, Osoba ya ce ya dogara kacokam da ma’aikatan gwamnati ba tare da ɗauko wani daga waje ba.

Ya ce:

“Ban taɓa kawo kowa daga wajen jihar ba domin ya yi aiki tare da ni, ko mai tura sako ne. Duk wani nasara da muka samu aikin ma’aikatan gwamnati ne.”

Gwamnan Kebbi ya ware N10bn kan aikin hajji

Kun ji cewa Gwamnatin Kebbi ta ware Naira biliyan 10 domin samun karin kujerun aikin hajjin bana 1,300 ga maniyyatan jihar.

An tsawaita wa’adin biyan kudin Hajj zuwa 16 ga Disamba, wanda hakan zai ba wa duk maniyyata damar samun kujerunsu.

Hukumar Hajj ta Kebbi ta riga ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2026, tare da tabbatar da cewa kowa zai samu damar sauke farali.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.