Mutane Masu Alaka da Zargin EFCC da Tinubu Ya Naɗa Jakadun Kasashen Waje
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen mutane akalla 35 ga Majalisar Dattawa domin tantance su a matsayin jakadun ƙasashen waje.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jerin sunayen jakadun da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tura ga majalisa makon da ya gabata ya jawo ce-ce-ku-ce.
Wannan ya biyo bayan bayyanar sunayen mutane da ake alakanta wa da binciken rashawa ko wasu makamantan laifuffuka.

Source: Facebook
Daga cikin jerin, sunayen mutane hudu musamman suka dauki hankali saboda matsalolin da aka taɓa danganta su da su a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Femi Fani-Kayode
Jaridar Punch ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta dade tana tuhumar tsohon ministan jiragen sama, Femi Fani-Kayode, da laifuffukan hada-hadar kuɗi ba bisa ƙa’ida
Haka kuma hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta shigar da wata karar bisa zargin amfani da takardun lafiya na boge a kotu.

Source: Twitter
Hukumar ta zargi Fani-Kayode da samun shaidar rashin lafiya ta boge daga wani Dr. Ogieva Oziegbe, wadda aka gabatar wa kotun tarayya a Legas.
Sai dai kotun da ke Ikeja ta yi watsi da dukkanin tuhume-tuhume da EFCC ke yi wa tsohon Ministan tarayyan.
Mai Shari’a Olubunmi Abike-Fadipe ta yanke cewa hukumar EFCC ba ta gaza kawo isassun hujjoji da za su tabbatar da cewa ya yi laifin -
2. Ayodele Oke
Jaridar The Cable ta bayyana cewa EFCC ta zargi tsohon darakta-janar na hukumar bincike ta kasa, NIA, Ayodele Oke da ɓoye $43m, £27,000 da N23m a wani gida a Ikoyi a 2017.

Source: Facebook
Sai dai a ranar 9 ga Yuni 2023, Mai Shari’a Chukwujekwu Aneke na Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi ya kori shari’ar baki ɗaya.
An ce EFCC ce da kanta ta nemi janye karar, kuma tawagar lauyan Oke ƙarƙashin jagorancin Kayode Ajulo ba ta ƙalubalanci hakan ba.
3. Ifeanyi Ugwuanyi
Rahotanni a kafafen sada zumunta sun yaɗa wa EFCC na bincikar tsohon gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, bisa zargin karkatar da N40bn zuwa N117bn lokacin da yake mulki.
Sai dai rahotanni daga The Guardian sun bayyana cewa wannan zargi bai fito daga EFCC ba, tare da ƙaryata cewa tsohon gwamnan ya tsere don gujewa kamun EFCC.

Source: Facebook
Daily Post ta ruwaito daga baya cewa EFCC na zargin wani hadimin gwamnan da karkatar da sama da N200m.
Amma gwamnatin jihar ta bayyana cewa ba shi da alaka da gwamnan kuma wannan ba ya nufin ana binciken Ugwuanyi a kan wata almundahana.
4. Okezie Ikpeazu
A lokacin mulkin tsohon gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu, an yi zargin cewa an samu gagarumin makarkashiya a kwangiloli.
Daga ciki har da batun N10bn da aka ware don gina filin jirgin sama na Abia da ake zargin an tura shi zuwa asusun mutane masu zaman kansu, kuma ba shaidar kwangila.

Kara karanta wannan
Obasanjo ya fadi matsayarsa kan tattaunawa da 'yan bindiga, ya ba gwamnati shawara
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa gwamnatin da ta gaje shi ta mikawa EFCC cikakken rahoto mai shafuka 360 domin daukar mataki kan zargin almundahana.

Source: Twitter
Rahoton, wanda Kwamishinan Yada Labarai a lokacin Prince Okey Kanu ya fitar, ya kuma ce an samu kwangiloli da dama da ba su da takardun bayanin kashe kuɗi yadda ya kamata. Haka kuma EFCC ta ayyana tsohon kwamishinan jihar, Christopher Enweremadu, a matsayin wanda ake nema saboda zargin karkatar da kuɗin gwamnati da wasosonsu.
Sai dai ba a zargi Ikpeazu kai tsaye da karɓar kuɗin ba, kuma shi ma ya musanta zargin cewa ya yi wasa da kudin jama’a kamar yadda wasu ke yada wa game da gwamnoninsa.
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa jakadu
A baya, mun wallafa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa jerin sunayen mutane da ya zaɓa domin su zama jakadun ƙasashen waje.
Daga cikin mutanen akwai mutane 15 daga Arewacin Najeriya, ciki har da tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, Mahmood Yakubu.
An ce daga cikin waɗanda aka maida su su zama jakadun aiki akwai tsofaffin jami’an diflomasiyya, yayin da wasu kuma aka nada su a matsayin jakadun ba na aiki ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
