Gwamnan Enugu Ya Yi Layar Zana Tun Bayan Mika Mulki? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamnan Enugu Ya Yi Layar Zana Tun Bayan Mika Mulki? Gaskiya Ta Bayyana

  • An musanta zargin cewa tsohon gwamnan Enugu da ya gabata, Ifeanyi Ugwuanyi, ya gudu don tsira daga EFCC
  • Ƙungiyar kare hakkin ɗan adam (HURIWA) ta ce wakilanta sun ziyarci tsohon gwamnan kwanan nan amma babu tabbacin ko EFCC ta fara bincikarsa
  • Ta ce hukumar EFCC ce kaɗai ke da hurumin bayyana cewa tana tuhumar wani mutum ko akasin haka

Ƙungiyar marubuta masu fafutukar kare haƙƙin ɗan adam (HURIWA) ta bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, na nan bai gudu ba.

A cewar ƙungiyar, tsohon gwamnan bai tsere daga Najeriya don guje wa tuhumar hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa watau EFCC ba.

Tsohon gwamnan Enugu.
Gwamnan Enugu Ya Yi Layar Zana Tun Bayan Mika Mulki? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: PDP Update
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Guardian ya ce kodinetan HURIWA na ƙasa, Emmanuel Onwubiko, ne ya musanta zargin tsohon gwamnan ya gudu a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Rigima Sabuwa: Gwamnan PDP Zai Yi Binciken Kwakwaf Kan Gwamnatin Da Ya Gada, Ya Bayyana Dalilansa

Ya ce a 'yan kwanakin nan, mambobin ƙungiyar sun gana da tsohon gwamnan na jam'iyyar PDP a gidansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan PDP na nan a gidansa

Mista Onwubiko ya ce wannan ci gaban ya saɓa wa rahoton da wasu ke yaɗawa cewa tsohon gwamnan ya sa kafa ya gudu domin kar EFCC ta titsiye shi.

Haka nan ƙungiyar HURIWA ta jaddada cewa hukumar EFCC ce kaɗai ke da alhakin fayyace gaskiya kan ko ta fara bincikar tsohon gwamnan PDP kan zargin karkatar da wasu kuɗi ko ba haka bane.

HURIWA ta ce ba ta yi yunkurin bincikar jigon PDP ba saboda ya yi amfani da kuɗaɗen jihar Enugu wajen bunƙasa bangaren fasaha, kiyon lafiya, ayyukan raya ƙasa da sauransu.

Sanarwan ta ce:

"Rahoton da ke cewa tsohon gwamna ya gudu ba gaskiya bane domin yana nan a cikin jihar Enugu yana karban baƙi daga ƙungiyoyi daban-daban, sarakuna, da abokai, har sabon gwamna yana neman shawarinsa."

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Muhimman Abubuwan da Su Wike Suka Tattauna da Shugaba Tinubu a Aso Rock Sun Bayyana

Kotu Ta Dakatar da NLC da Wasu Kungiyoyi Daga Shiga Yajin Aiki

A wani labarin kuma Kotun ɗa'ar ma'aikata ta hana NLC da sauran ƙawayenta shiga yajin aiki kan cire tallafin Fetur.

Alkalin ya haramtawa dukkan ƙungiyoyin tafiya yajin aiki daga ranar 7 ga watan Yuni, har sai Kotun ta yanke hukuncin karshe kan karar da aka shigar gabanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel