An nemi Femi Fani-Kayode an rasa a shari’ar badakalar Dala biliyan 2.1

An nemi Femi Fani-Kayode an rasa a shari’ar badakalar Dala biliyan 2.1

Rashin zuwan Femi Fani-Kayode gaban kotu ya sa an dage shari’ar da ake yi da shi a wani kotun babban birnin tarayya da ke birnin Abuja.

A lokacin da Magatakardan kotun ya kira sunan Femi Fani-Kayode, sai dai Lauyan da ya ke kare sa watau Ahmed Raji SAN kawai aka gani.

Tsohon Ministan kadai ake kara a shari’a mai lamba ta FHC/ABJ/CR/140/2016 da ke gaban Alkali John Tsoho kamar yadda mu ka samu labari.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta bayyana cewa ana tuhumar Fani-Kayode ne da karbar miliyan 26 daga cikin kudin makamai.

Fani-Kayode wanda ake kira FFK ya karbi wannan kudi ne a ofishin Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, ONSA, a shekara 2015.

KU KARANTA: EFCC sun kama sama da mutum 90 a gidan rawa a Oyo

An nemi Femi Fani-Kayode an rasa a shari’ar badakalar Dala biliyan 2.1
EFCC ta na zargin Femi Fani-Kayode da karbar N26m a hannun Sambo Dasuki
Asali: Depositphotos

EFCC ta maka ‘Dan siyasar a kotu ta na zarginsa da laifuffuka da su ka hada da karkatar da wadannan miliyoyi da sabawa dokar yawo da kudi.

A lokacin da aka shirya a kotu domin cigaba da shari’a a gaban Alkali, sai Lauyan wanda ake zargi ya mike a madadi ya bada hakurin rashin halarta.

Lauya Ahmed Raji ya shaidawa kotu cewa wanda ake zargi bai samu labarin wannan zama ba a dalilin dage shari’ar da aka yi kwanakin baya.

Wannan ya fusata Lauyan EFCC, Mohammed Abubakar. A karshe dai dole Alkali y adage shari’ar zuwa Ranar 10 da 11 ga Watan Maris mai zuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng