Cibiyar Zakkah da Wakafi Ta ba Matasa Horo kan Yaki da Talauci a Gombe

Cibiyar Zakkah da Wakafi Ta ba Matasa Horo kan Yaki da Talauci a Gombe

  • Cibiyar Zakkah da Wakafi ta jihar Gombe ta gudanar da horo ga matasa fiye da 80 a taron shekara-shekara karo na shida
  • Masana daga sassa daban-daban sun gabatar da makaloli game da yaki da talauci, dogaro da kai da kuma dabarun noma da ICT
  • Matasan da suka taba halartar shirin sun shaida cewa horon ya taimaka musu wajen samun sana’a da gina rayuwarsu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Cibiyar Zakkah da Wakafi ta jihar Gombe ta sake gudanar da taron shekara-shekara na horas da matasa, inda wannan karo ya kasance na shida a tarihinta.

Taron ya gudana ne karkashin jagorancin shugaban cibiyar, Dr Abdullahi Abubakar Lamido, wanda ya bayyana manufar shirin a matsayin matakin yaki da talauci tare da karfafa matasa.

Kara karanta wannan

Jonathan ya gana da Tinubu, ya fada masa abin da ya faru da shi a Guinea Bissau

Taron Zakkah da Wakafi a jihar Gombe
Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron Zakka da Wakafi a Gombe. Hoto: Zakah & Waqf Foundation Gombe Nigeria
Source: Facebook

Cibiyar ta wallafa yadda shirin wannan shekarar ya gudana a jerin sakonnin da ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan zangon, matasa sama da 80 daga sassa daban-daban na jihar Gombe ne suka samu damar shiga shirin.

An gayyato manyan masana daga fannoni daban-daban domin gabatar da makaloli da zasu ilmantar da matasan kan hanyoyin ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwa.

Muhimmancin horarwar da cibiyar ke bayarwa

A jawabin da ya gabatar ga mahalarta taron, shugaban cibiyar, Dr Abdullahi Abubakar Lamido ya jaddada cewa manufar shirin ita ce cire matasa daga kangin talauci, tare da karfafa musu gwiwa.

Dr Lamido ya ce horas da matasa wata hanya ce ta gina al’umma mai dorewa, musamman ma a Arewa, yankin da ke fama da matsalolin tattalin arziki.

Ya gabatar da makala mai tsawo game da muhimmancin Wakafi a tsarin ci gaban al’umma, tare da bayyana yadda amfani da shi yadda ya kamata zai iya taka muhimmiyar rawa wajen rage talauci.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba bayan zubar da harsahi a kofar jami'ar ABU Zariya

Abubuwan da aka koya wa matasa a Gombe

Wani malami, Dr Usman Ali, ya gabatar da takarda dangane da dogaro da kai ga matasa, inda ya ja hankalinsu su guji zaman banza tare da mayar da hankali kan koyon sana’o’i.

Ya ce kowane matashi na da damar kaiwa ga nasara muddin ya dage kan abin da ya zaba domin gina rayuwarsa.

A nasa bangaren, Dr Abubakar Sadiq Usman ya yi tsokaci game da tarihi da kuma muhimmancin koyon sana’ar iyaye kamar yadda ake yi a shekarun baya.

Ya yi magana yana mai cewa hakan shi ne ginshikin da ake dogaro da shi wajen hana zaman banza a cikin al’umma.

Masani a fannin ICT, Dr Najib A.A Gambo, ya yi wa matasa bayani kan dabarun samun kuɗi ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Dr A.A Gambo ya nuna hanyoyin da za su iya amfani da ilimin ICT wajen tafiyar da kasuwanci ko samar da ayyukan yi.

Masani a bangaren noma, Dr Adamu Tilde, ya bayyana damarmaki da hanyoyin da matasa za su iya amfani da su a harkokin noma.

Kara karanta wannan

Ana so a rika hukunta jami'an gwamnati da ke tattaunawa da 'yan bindiga

Dr Adamu Tilde ya fadi yadda ya fara gidan gona ya samu nasara duk da kalubale iri-iri da ya fuskanta.

Bayanin wasu mahalarta taron Zakka da Wakafi

A yayin tattaunawa da mahalarta wannan karon, Muhammad Shamsuddin ya ce an tabo fannoni da dama na rayuwa wadanda idan mutum ya mayar da hankali a kansu zai samu nasara.

Abdulaziz Musa kuwa ya ce shirin ya ba shi karfin gwiwa sosai, inda ya fahimci cewa duk abin da mutum ya dage da shi zai iya bunkasa rayuwarsa.

Ya mika godiya ga cibiyar saboda koyar da su muhimmiman abubuwan da za su taimaka musu wajen inganta rayuwarsu.

Mahalarta taron Zakkah da Wakafi a Gombe
Wasu mahalarta shirin Zakkah da Wakafi karo na 6 a Gombe. Hoto: Zakah & Waqf Foundation Gombe Nigeria
Source: Facebook

Shaidu daga wadanda suka amfana a baya

Daga cikin wadanda suka halarci shirin a baya akwai Muhammad Nasir Ishaq, wanda ya ce tun daga karo na hudu da ya samu halarta ya fara samun canji a rayuwarsa.

Isma’il Ibrahim Musa kuwa ya bayyana cewa horon da ya samu ya ba shi damar bude shago, wanda ya taimaka masa ya gina gida tare da daukar nauyin iyalinsa.

Kara karanta wannan

'Ana cikin tsoro,' 'Yan majalisar sun yi zazzafar muhawara kan rashin tsaro

An yi taron MCAN a jihar Gombe

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar masu hidimar kasa Musulmi ta shirya taron Arewa maso Gabas a jihar Gombe.

Shugaban kungiyar ya ce an zabi sababbin shugabanni da za su ja ragamar MCAN a jihohin Arewa maso Gabas.

Abdulmalik Mahmud Adam ya yi kira ga gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya da ya sama musu motar zirga-zirga.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng