Zakka na iya kawar da talauci – Sarki Sanusi

Zakka na iya kawar da talauci – Sarki Sanusi

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya bayyana zakka a matsayin wani makami da za’a iya amfani da shi wajen yakar talauci a tsakanin al’umma.

Basaraken a wajen taron raba zakka wanda gidauniyar bayar da tallafi na Jaiz ta shirya aka kuma gudanar a fadarsa da ke Kano, yace idan har aka tsara rabon zakka yadda ya kamata, zai rage yawan talauci a kasar.

Akalla mata 100 ne suka amfana daga rabon kayayyaki kamar su kekunan dinki da injin nika, firinjin daskarar da kankara da kuma kudade.

Sarki Sanusi ya tuna cewa a lokacin zamanin wasu kalifofin annabi bayan mutuwar manzon tsira annabi muhammed, babu talakawa a karninsu da suka cancanci karban zakka saboda wadanda aka rarraba a shekarun baya yasa duk sun zamo masu dogaro da kai.

Zakka na iya kawar da talauci – Sarki Sanusi
Zakka na iya kawar da talauci – Sarki Sanusi
Asali: Depositphotos

A cewarsa ana tura kudaden ne zuwa sauran kasashen waje. Sarkin ya jadadda cewa addinin Islama addini ne da ke gudana a aikace.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya shiga dimuwa – Tambuwal ya yi ba’a ga gwamnan Kaduna

Ya yaba ma bankin Jaiz kan samar da gidauniyar tallafawa gajiyayyu da kuma kawo rabon da suka yi Kano tare kuma da zabar mata a matsayin wadanda za su amfana daga shirin.

Sarki Sanusi ya bukaci wadanda suka amfana daga shirin da su yi amfani da kayayyakin da aka rarraba masu wajen dogaro da kansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel