‘Babu Adalci’: Bello El Rufai Ya Tabo batun Hukuncin Nnamdi Kanu a Najeriya
- Hon. Bello El-Rufai ya yi magana game da yadda bangaren shari'a ke yanke hukuncin musamman kan wadanda ake zargi da laifufffuka
- El-Rufai ya soki bambancin hukuncin da ake bai wasu da ake zargi da ta’addanci, yana kira a samar da tsarin shari’a mai daidaito
- Dan majalisar ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan sabon tsare-tsaren tsaro, yana kuma neman ƙarin albashi da jin daɗin jami’ai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Bello El-Rufai, ya kalubalanci rashin daidaito a hukunci kan zargin ta'addanci.
Bello El-Rufai ya soki yadda ake samun bambanci game da yanke hukunci ga wadanda aka samu da laifin ta’addanci a Najeriya.

Source: Twitter
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a X yayin zaman majalisar inda ya bukaci kawo sauyi a yadda ake hukunce-hukunce.

Kara karanta wannan
Abu ya gagara: Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan matsalar tsaron Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nnamdi Kanu: Bello El-Rufai ya soki bangaren shari'a
Bello ya ce akwai bukatar tsarin shari’a ya kasance a bude kuma hukunci ya zama iri daya ga kowa.
'Dan majalisar ya ambaci hukuncin da aka yankewa mamban kungiyar Ansaru, Husseini Ismail, wanda kotun tarayya ta Abuja ta yanke masa shekaru 20 a kurkuku.
Sannan ya kwatanta shi da hukuncin da kotu ta yi ga shugaban kungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, inda aka yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai.
Ya ce:
“Akwai wani dan Boko Haram mai suna Husseini Ismail da aka yanke masa hukuncin shekaru 20, amma an yanke wa Mazi Nnamdi Kanu hukuncin rai-da-rai, me ya kawo bambancin nan?”
Bello ya ce wannan ya kara tabbatar da maganar cewa shari’a tana tafiya ne ta hanyoyi daban-daban, abin da ke kara kawo matsaloli a kasa.
Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan sabon tsarin sauya tsaro da ya bayyana, yana rokon majalisa ta tabbatar da cewa an aiwatar da shirin cikin lokaci.

Kara karanta wannan
"Mutane suna da mantuwa," Sheikh Gumi ya yi magana kan zargin goyon bayan 'yan bindiga
Ya ce:
“Shugaban kasa ya fito da tsari mai kyau, matsalar mu ba yin tsari ba ne, aiwatarwa ce matsala da takamaiman lokaci.”

Source: Twitter
Bello El-Rufai ya bukaci karawa jami'an tsaro albashi
Bello, wanda shi ne ɗan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jaddada bukatar inganta walwala da albashin jami’an tsaro, yana mai cewa Najeriya na fama da ƙarancin ma’aikata.
Ya bayyana damuwarsa kan karuwar jahilci da rashin aikin yi a Arewa, yana mai cewa hakan ya mayar da yankin wurin aikata laifuffuka da tsattsauran ra’ayi.
Bello ya kara da cewa yadda matasa ke kallon bidiyon ‘yan ta’adda a TikTok suna nuna kudi yana sa su kwaikwayon su saboda rashin aikin yi da ilimi.
Bello El-Rufai ya nemi afuwar Goodluck Jonathan
A baya, an ji cewa dan majalisar wakilai a jihar Kaduna, Bello El-Rufai, ya nemi afuwar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
El-Rufai ya nemi afuwar ne bayan sukar tsohon shugaban kasar inda ya ce rashin wayonsa ne ya sa ya soke shi.
Ya bayyana cewa sai bayan ya ga mahaifinsa na shirin ziyartar Jonathan domin shawarwari ne ya gane irin mulkin kirki da aka yi a wancan lokaci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
