Yadda Wata Ibo Ta Karya Dokar Katolika, Ta Sauya Suna bayan Shiga Musulunci

Yadda Wata Ibo Ta Karya Dokar Katolika, Ta Sauya Suna bayan Shiga Musulunci

  • Wata matashiya ’yar asalin kabilar Igbo ta bayyana yadda ta bar Katolika ta karɓi Musulunci, tana mai cewa ta samu natsuwa da cikakkiyar fahimta
  • Ta bayyana cewa sunanta na Katolika Modesta Mary ne, amma daga bisani ta gano Mary da Maryam suna da ma’ana ɗaya
  • Ta ce tana alfahari da karya dokar Katolika domin karɓar Musulunci, tana jaddada cewa har yanzu ita ’yar Igbo Musulma daga gidan Kirista

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Wata tsohuwar mai bin darikar Katolika, wadda yanzu ta koma Musulunci, ta bayyana yadda ta rungumi addinin da cikakken farin ciki.

Matashiyar ’yar kabilar Igbo mai suna Ugwu Kenechi Modesty Mary ta ce tana alfahari da karya dokar Katolika domin bin addinin da ya fi dacewa da ita.

Yar kabilar Igbo ta karbi Musulunci
Mary wacce ta bar darikar Katolika zuwa Musulunci. Hoto: @ugwukenechi_maryam.
Source: TikTok

Yar darikar Katolika ta karbi Musulunci

Kara karanta wannan

Abin da gwamnatin Tinubu ta ce kan juyin mulki a Guinea Bissau, ta yi gargadi

A cikin bidiyon TikTok da ta wallafa, Maryam ta nuna hotunanta lokacin da take mabiyar darikar Katolika, tana mai cewa sunanta Modesta Mary ne lokacin tabbatarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce daga bisani da ta bar Kiristanci ta gano Mary da Maryam ma’ana guda gare su, ɗaya na Turanci ɗaya kuma na Larabci.

Ta bayyana cewa yanzu ana iya kiranta Maryam ko Mary, domin duk suna ɗaya ne, Maryam ta ce ta yi alfahari da sabon yanayinta a Musulunci, tare da nuna hoton kanta sanye da hijabi a matsayin sabuwar Musulma.

Yar kabilar Igbo daga darikar Katolika ta koma Musulunci
Mary kenan daga darikar Katolika wacce ta gane gaskiya a Musulunci. Hoto: @ugwukenechi_maryam.
Source: TikTok

Daga wace kabila Maryam ta ke a Najeriya?

Maryam ta kara da cewa har yanzu ita ’yar kabilar Igbo ce Musulma daga gidan Kirista, wadda ta samu imani da natsuwa a Musulunci.

Ta shaida cewa wannan shawara ita ce mafi girma da ta taba ɗauka a rayuwarta wanda yanzu kuma tana jin dadin matakin da ta dauka wa kanta.

A rubutun da ta yi, Maryam ta ce:

"Ba kawai na karɓi Musulunci ☪️ ba ne, na canza suna ba. Sunana UGWU KENECHI MODESTA MARY. Lokacin da na karɓi Musulunci na gano cewa Mary da Maryam suna da ma’ana ɗaya, suna ɗaya ne; Mary Turanci ne, Maryam kuwa Larabci.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba bayan zubar da harsahi a kofar jami'ar ABU Zariya

"Don haka ga shi, za ku iya kirana Maryam ko Mary, duk ɗaya ne, ku tuna, har yanzu ni Musulmar Igbo ce daga gidan Kirista wadda ta sami gaskiya a Musulunci."

Wannan bidiyo da ta wallafa ya samu martanin mutane da dama inda da wasu ke taya ta murna da cewa ko Musulunci ko Kiristanci duk suna sonta a haka.

Wasu cewa suka yi babu wani karya doka da ta yi, ta zabi abin da ya fi mata ne a rayuwa inda suka yi mata fatan alheri.

Yarinyar uwar zumunta ta karbi Musulunci

Mun ba ku labari a baya cewa wata matashiya ta karɓi Musulunci a radin kanta, inda Malam Adamu Ashaka da Baban Chinedu suka jagoranci addu’o’i da jan hankali.

Baban Chinedu ya shawarce ta kan kalubalen da masu sauya addini ke fuskanta, yana mai cewa ta rungumi Musulunci saboda lahira.

Adam Ashaka ya kara da cewa duk wanda ya musulunta ba ya rasa jarabawa, yana karfafa mata gwiwa da ta dage cikin hakuri.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.