Rayuwar Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Kowa Ya Sani

Rayuwar Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi: Abubuwa 5 da Ya Kamata Kowa Ya Sani

Bauchi - Rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ta girgiza al’ummar Najeriya da mabiya tijjaniyya a fadin duniya.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legit Hausa ta rahoto cewa, iyalan malamin ne suka sanar da cewa Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu da sanyin safiyar Alhamis, 27 ga Nuwamba, 2025.

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu
Sheikh Dahiru Usman Bauchi a wajen taron Mauludi a jihar Bauchi. Hoto: Fityanul Islam
Source: Facebook

Malamin, wanda ke cikin manyan malaman Qur’ani a Afrika ta Yamma, ya shafe kusan karni yana yada ilimi, zaman lafiya da tarbiyya ga miliyoyin mabiyansa, in ji rahoton BBC Hausa.

Sheikh Dahiru ya kasance fitila ga darikar Tijjaniyya, kuma sanannen jagora wanda ya yi tasiri a harkokin addini, mu’amala da siyasar Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan rahoto na Legit Hausa ya waiwayi wasu muhimman bayanai game da malamin, ya kuma haska abubuwan da suka bayyana shi a matsayin “jagoran darikar Tijjaniyya a Afrika” wanda ya shafe sama da shekaru 90 yana yi wa Musulunci hidima.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki: "Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi babban rashi ne ga Musulmai

1. Haihuwar Sheikh Dahiru Bauchi

An haifi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a ranar Laraba 28 ga Yuni 1927, a garin Nafada na jihar Gombe, kamar yadda rahoton Daily Trust ya nuna.

Mahaifinsa, Alhaji Usman Adam, dan asalin jihar Bauchi ne, kuma ya kasance sanannen malamin Qur’ani, yayin da mahaifiyarsa, Hajiya Maryam, ta fito daga gida mai zurfin addini a Gombe.

Sheikh Dahiru ya haddace Qur’ani tun yana ƙarami a hannun mahaifinsa, wanda ya ba shi hoto da kuma dora shi kan turba ta ladabi.

Daga nan ne ya fara yawo daga gari zuwa gari domin ya kara cika iliminsa a wuraren malamai daban-daban.

A hirarrakinsa da ya yi shekaru kafin rasuwarsa, yana yawan bayyana cewa “tafiya neman ilimi ita ce ta gina mi, ta kuma ba ni fahimta mai zurfi a Qur’ani.”

2. Iyalin Dahiru Bauchi da zuri'ar da ya bari

Sheikh Dahiru ya bar iyali mai yawan gaske. A cewar ɗansa, Sheikh Bashir Dahiru Bauchi, malamin ya haifi 'ya'ya fiye da 90, yayin da jikokinsa suka haura 100.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi, ya fadi alherin da ya yi masa

Kusan kashi biyu cikin uku na ‘ya’yansa sun haddace Qur’ani, inda ya taba shaidawa jaridar DW Hausa cewa yana da 'ya'ya mahaddata akalla 73 da jikoki 200.

Matan Shehun sun hada da Hajiya Fatima (Nana), Hajiya Khadija (Inna), Hajiya A’isha da Hajiya Maman Hamrat. Dukansu sun taka rawa wajen kula da makarantar Qur’ani da almajiran malamin.

3. Malaman da suka gina rayuwar Dahiru Bauchi

Ko da yake mahaifinsa shi ne farkon malamin da ya koyi Qur’ani a hannunsa, amma Sheikh Dahiru ya ci gaba da daukar darussa a wuraren malamai daban-daban, domin ya inganta karatun addini da ma’anar rubuce-rubucen addini.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi karatu a hannun Malam Baba Sidi, Malam Saleh da Malam Baba Dan Inna, in ji wani rahoto na amsoshin tambayoyin masu karatu a BBC Hausa.

Ya ziyarci Zaria, Kano da wasu manyan garuruwa domin daukar ilimi a wajen fitattun malamai irin su Malam Abdulkadir, Shehu Mai Hula, Shehu Tijjani da Shehu Atiku.

An rahoto cewa Sheikh Dahiru Bauchi na da kyakkyawar alaka da Sheikh Ibrahim Niass
Sheikh Dahiru Usman Bauchi, malamin Musulunci da ya rasu a ranar Alhamis. Hoto: Fityanul Islam
Source: Facebook

4. Dangantaka mai karfi da Sheikh Ibrahim Inyass

Ba abin mamaki ba ne cewa Sheikh Dahiru ya zama daya daga cikin manyan almajiran Sheikh Ibrahim Niass.

Kara karanta wannan

Hardar Kur'ani: Sheikh Dahiru Bauchi da zuriyarsa sun kafa tarihi a duniyar Musulunci

A wata hira da aka yi da shi da aka wallafa a shafinsa na YouTube, malamin ya ce dangantakarsu ta wuce tsakanin malami da almajiri — sun zama iyali, domin ya auri ‘ya’ya biyu na Niass.

Ya kuma ce ya yi aiki a matsayin khadimi, almajiri da kuma suruki, wanda hakan ya kara dankon soyayya da amana a tsakaninsu.

Shi kan shi Sheikh Dahiru ya sha fada cewa farin cikinsa mafi girma shi ne ganin darikar Tijjaniyya ta kara bunƙasa a Najeriya da Afrika.

5. Abubuwan da Sheikh Dahiru ya fi so

Malamin ya yi fice wajen son karatun Qur’ani — karantawa da koyar da shi. Ya kuma shahara wajen sanya fararen kaya, abin da ya dauka alama ce ta tsabta, annuri da biyayya ga sunnah.

A kullum ana ganin shehin malamin cikin shiga ta kamala bisa al'ada da addininsa na musulunci irinsu rawani, alkyabba da sauransu.

An sanya lokacin jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, an sanya lokacin da za a gudanar da jana'izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun sanar da cewar za a yi jana’izar malamin, a gidansa da ke Bauchi a ranar Juma'a, 28 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta girgiza Sanata Barau, ya fadi yadda ya ji

Jim kadan bayan sanar da rasuwar malamin, an ce gomman mutane sun fara tururuwa a masallacinsa da ke cikin kwaryar Bauchi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com