'Ya'yana guda 70 ne suka haddace Al-Qur'ani mai girma daga Baraka har Nasi - Sheikh Dahiru Bauchi

'Ya'yana guda 70 ne suka haddace Al-Qur'ani mai girma daga Baraka har Nasi - Sheikh Dahiru Bauchi

- Sheikh Dahiru Bauchi sanannen malami ne da ya yi suna a nahiyar Afirka saboda hidimarsa ga addinin musulunci

- Shehin malamin na da shekaru 92 a duniya kuma yana da yara 80, Malamin ya bayyana cewa a cikin yara 80 guda 70 ne suka haddace kur’ani

- Shehin ya rubuta kur’ani sau biyu, yana kan na ukun kuma ya yi aikin hajji sau 48 a duniya

Sheikh Dahiru Usman Bauchi sanannen malamin darikar Tijjaniya ne da ake ji dashi a duk fadin nahiyar Afirka. Ya sadaukar da rayuwarshi wajen hidimtawa Al-Qur’ani ta hanyar koyar dashi ga jama’a.

An haifi shehin malamin a ranar 28 ga watan Yuni 1927 wanda ya yi dai-dai da 2 ga watan Muharram 1346. An haifeshi a garin Nafada da ke jihar Gombe (al’adar Fulani ce haihuwar dan fari a gidansu mahaifiya).

Cikakken bafulatani ne gaba da baya. Mahaifiyarshi sunanta Maryam ‘yar Ardo Sulaiman, mahaifinshi sunanshi Alhaji Usman dan Alhaji Adam.

Shehin malamin ya haddace kur’ani a wurin mahaifinsa inda daga baya ya tura shi Bauchi don neman tilawa. Malamin ya yi auren fari a 1948 lokacin yana da shekaru 20 a duniya.

KU KARANTA: Tirkashi: Babban fasto ya mutu jim kadan da barin shi jam'iyyar PDP ya koma APC

Sheikh Dahiru ya ce yana da ‘ya’ya kimanin 80 kuma 70 daga ciki sun haddace kur’ani. Wasu daga ciki sun haddace tun suna da shekaru 7 a duniya, tun kafin su iya rubutun allo.

“Akwai yarana hudu da suka haddace tun suna da shekaru biyar. Ban sani ba ko cikinsu akwai wanda ya rubuta kur’ani. Saboda su kan fita kasashen duniya don karatun fannonin addini har da na boko. Akwai daraktoci a cikin ‘ya’yana a yanzu,” cewar Shehun malamin.

Sheikh Dahiru Bauchi na da mata hudu, duk da wasu sun rasu, wasu kuma sun fita. Ya yi aikin hajji 48 a rayuwarshi kuma yana da makarantu 300. Shehin malamin ya rubuta kur’ani sau biyu, yana kan rubuta na ukun.

Allah ya kara wa rayuwar shehi albarka, Ameen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng