Kanu da Mutanen da Suka Wakilci Kansu a Kotu ba Tare da Lauya ba da yadda Ta Kaya
Abuja, Nigeria - A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamba, 2025, babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta kama jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da laifi.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kotu ta gamsu da hujjojin da aka gabatar a gabanta tun farkon shari'ar cewa Kanu na da hannu a ayyukan ta'addanci a wasu sassan Najeriya.

Source: Twitter
Kotu ta karkare shari'ar Nnamdi Kanu
Jaridar The Cable ta kawo cewa alkalin kotun, mai shari'a James Omotosho ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai-da-rai bayan ya same da shi laifuffukan ta'addanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kafin kai wa ga matakin yanke hukunci, shari'ar Nnamdi Kanu ta zo da abubuwa daban-daban na hayaniya da fadan da ya yi da lauyoyin da ke kare shi.
Wannan lamari ya ja hankalin 'yan Najeriya musamman lokacin da jagoran IPOB din ya shaida wa Kotu cewa shi zai kare kansa da kansa a shari'ar da ake masa.
Duk da kotu ta yi kokarin ba shi lokaci domin ya kare kansa bayan rabuwa da lauyoyi, Nnamdi Kanu bai iya yin abin da zai nuna bai aikata laifuffukan da ake tuhumarsa ba.
Mutanen da suka wakilci kansu a kotu
Bisa haka muka tattaro muku mutanen da suka taba kokarin kare kansu da kuma yadda aka karkare a kotu a Najeriya. Ga su kamar haka:
1. Nnamdi Kanu
A 2015, dakarun hukumar DSS suka kama Nnamdi Kanu a karon farko kan zargin cin amanar kasa, inda aka tsare shi na tsawon shekara guda kafin kotu ta ba da belinsa a 2017, in ji rahoton Tribune.
Daga baya shugaban na IPOB ya samu dama ya sulale daga Najeriya lokacin da sojoji suka kai mamaya gidansa a 2017, amma a 2021 aka sake kama shi a Kenya kuma aka taso shi zuwa Najeriya.
Bayan haka ne gwamnatin Najeriya ta sake gurfanar da shi a babbar kotun tarayya kan tuhume-tuhume bakwai da suka shafi aikata ta'addanci a Najeriya.
A watan Oktoba, 2025, Kanu ya kori gaba daya lauyoyinsa kuma ya sanar da kotu cewa a shirye yake ya kare kansa a zaman shari'ar da ake masa.

Kara karanta wannan
DSS ta shaida wa kotu yadda Tukur Mamu ya rika wadaƙa da 'kasonsa' na kudin fansa
Tawagar lauyoyin Kanu, wacce ta kunshi manya ciki har da Kanu Agabi (SAN) da Ifedayo Ikpeazu (SAN), sun sanar da janyewarsu daga shari'ar bayan da shugaban IPOB ya dage cewa ba ya bukatar wakilcin lauya.

Source: Twitter
Kanu, wanda ya yi magana daga wurin da ake tsare da shi, ya shaida wa kotu cewa ya rasa kwarin gwiwa kan lauyoyin da ke kare shi kuma shi da kansa zai dauki nauyin shari'arsa.
Jaridar This Day ta ruwaito Kanu yana cewa "Na yanke shawarar kare kaina a wannan lamari."
Duk da damarmakin da kotu ta ba shi na kare kansa, Kanu ya jaddada cewa babu wani abu da zai gabatar, inda ya dage cewa babu wata hujja da za a tuhume shi da laifin ta'addanci.
Bayan gaza gabatar da hujjojin da za su nuna gaskiyarsa, kotu ta sa rana kuma ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa samunsa da laifin ta'addanci.
2. Sheikh Abduljabbar Kabara
Shari'ar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da gwamnatin Kano na daya daga cikin shari'o'in da suka ja hankalin jama'a musamman a Arewacin Najeriya.
An gurfanar da Abduljabbar ne kan zargin munanan kalamai da rashin ladabi ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (S.A.W) a karatuttukansa.
BBC Hausa ta tattaro cewa daya daga cikin abubuwan da suka jawo tsaiko a shari'ar Abduljabbar Kabara shi ne yadda yake rigima da lauyoyinsa tare da korarsu gaba daya.
Malam Abduljabbar ya riƙa faɗa da lauyoyinsa da ke kare shi a gaban kotu inda ya rinƙa korar su bisa zargin haɗa baki da gwamnati da zamba cikin aminci.

Source: UGC
Haka nan kuma malamin ya shaida wa kotu cewa shi mutum ne da zai iya tsayawa a gaban kuliya domin kare kansa. Aƙalla ya kori lauyoyinsa fiye da guda uku.
A karshe dai babbar Kotun Shari'ar Musulunci ta Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifin kalaman rashin ladabi ga Annabi SAW.
3. Simon Ekpa
Simon Njoku Ekpa, ɗan asalin jihar Ebonyi a Najeriya da ke zaune a kasar Finland na daya daga cikin masu fafutukar ballewa tare da kafa kasar Biafra.
A 2022, yayin da yake ƙasar Finland, ya ayyana gwamnatin Biafra a matsayin wacce ta fara aiki a ƙasar, kuma a 2023 ya ayyana kansa a matsayin Firaministan Biafra a ƙasar waje.
A watan Nuwamba na shekarar 2024, Hukumar Bincike ta Ƙasar Finland (NBI) ta damke Ekpa, bisa zargin ayyukan ta'addanci a Najeriya, cewar rahoton The Nation.
Bayan gurfanar da shi a gaban kuliya, Kotun Finland ta tsare Ekpa a gidan yari bisa zarginsa da laifin tunzura jama'a don aikata laifi da nufin ta'addanci.

Source: Twitter
Duk da cewa ya dauki lauya, a tsakiyar shari'ar Simon Ekpa ya yi kokarin wakiltar kansa a gaban kotu, inda ya musanta duka tuhume-tuhumen da ake masa, ya amince da laifi daya wanda ya shafi biyan haraji a Finland.
A watan Satumba na 2025, aka yanke wa Ekpa hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bayan samunsa da laifuffukan da suka shafi ta'addanci, ciki har da safarar makamai zuwa Najeriya.
Kotu ta hukunta jagoran ISWAP
A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta kama jagoran kungiyar ta'addaci ISWAP, Hussaini Isma'ila da hannu dumu-dumu a kai hare-hare a Kano.

Kara karanta wannan
An yi yunkurin kashe alkalin da ya yanke wa Nnamdi Kanu hukunci? Kotu ta yi bayani
Hakan dai ya biyo bayan shafe tsawon lokaci ana shari'a bayan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta cafke shi, sannan ta gurfanar da shi a gaban babbar kotu.
Kotun ta samu jagoran ISWAP din da laifin ta’addanci kuma ta yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan yari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

