An Yankewa Wasu Ƴan Najeriya 5 Hukuncin Kisa, Kotu Ta ba da Umarni a Rataye Su

An Yankewa Wasu Ƴan Najeriya 5 Hukuncin Kisa, Kotu Ta ba da Umarni a Rataye Su

  • Wata kotun Oyo ta samu wasu mutane biyar da laifin kashe direban tasi, Akeem Shittu, bayan wata hatsaniya a Ibadan
  • Alkalin kotun ta fara yanke masu hukuncin daurin shekaru 20, sannan ta yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya
  • Rahotanni sun bayyana cewa wadanda ake zargin sun yi wa direban dukan kawo wuka da ya zama ajalinsa a Afrilun 2024

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Wata babbar kotun Oyo da ke da zama a Ibadan, babban birnin jihar ta yanke wa mutum biyar hukuncin kisa ta hayar rataya.

Kotu ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta samu mutanen da laifin kashe wani direban tasi, Akeem Shittu, a wata arangama da ta faru a 2024.

Kotu ta samu mutane 5 da laifin kisan kai, ta yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Harabar ginin babbar kotun tarayya da ke Abuja. Hoto: David Exodus/Bloomberg
Source: Getty Images

Alkalin kotun, Mai Shari’a Oyeyemi Ajayi, ne ya yanke hukuncin kamar yadda jaridar Punch ta rahoto a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Cikin rashin imani, Boko Haram sun guntule kan mata saboda zargin tsafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta yankewa mutane 5 hukuncin kisa

Mai Shari’a Oyeyemi Ajayi ta bayyana cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne cikin hadin baki, don haka aka yanke masu hukunci na bai daya.

Wadanda ake zargin su ne; Segun Taiwo (36), Kehinde Ademola (46), Yahaya Adeniyi (45), Chinonso Samson (41) da Opadotun Michael (32).

Yayin yanke hukuncin kinsa, Mai Shari’a Ajayi ta ce kotun ta gamsu cewa akwai cikakken hadin baki tsakanin mutanen biyar kafin aukuwar kisan Shittu.

Ta fara yanke musu hukuncin shekaru 20 a kurkuku saboda hada baki, kafin ta yanke hukuncin kisa kan laifin kisan da suka yi.

A cewarta:

"A bisa abin da kotu ta gani, akwai cikakken hadin baki da ya kai ga mutuwar Shittu. A kan tuhuma ta biyu, an yanke wa kowanne wanda ake kara hukuncin kisa ta hanyar rataya.”

Hatsarin da ya rikide ya zama ajalin direba

Kara karanta wannan

Nnamdi Kanu: 'Yan Majalisa sun mika bukatarsu ga Tinubu kan jagoran IPOB

Kafin yanke hukuncin, lauyan gwamnati, K. K. Oloso, ta bayyana yadda lamarin ya fara da karamin hatsari tsakanin motar tasi da babur mai dauke da fasinjoji biyu.

Lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Afrilu, 2024, a Elepe, kan titin Arulogun, Ojoo, Ibadan, inda aka ce bangarorin da hatsarin ya shafa sun je wani gidan shan giya domin tattauna biyan diyya, amma rikici ya barke.

Daga nan ne wadanda ake zargin suka tsare direban tasin don kada ya bar wurin, kuma suka yi masa dukan da ya kai ga ajalisan lokacin da ya yi yunkurin guduwa, in ji rahoton Daily Post.

Alkalin kotun ta bayyana cewa mutane sun hada baki wajen kashe direban tasin
Taswirar jihar Oyo da ke a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda aka gano mota da kayan direban

Bayan faruwar kisan, jami’an bincike sun biyo diddigin motarsa da kayayyakinsa, suka gano su a shagon da ke da alaka da daya daga cikin wadanda aka yanke wa hukunci.

A cewar mai gabatar da kara, laifin da wadanda ake kara suka aikata ya sabawa sashe na 316 da sassa na 319 da 324 na dokar laifuffukan jihar Oyo ta 2000.

Ko a 2024, wata kotu a Osogbo, jihar Osun, ta yanke wa wasu mutum biyu, Wasiu Afolayan da Kola Adeyemi, hukuncin kisa saboda laifin hada baki da fashi da makami.

Kara karanta wannan

Amarya ta kashe ango a 'wani yanayi' bayan kwana 3 da daura masu aure a Katsina

Kotu ta yanke wa mutane 4 hukuncin kisa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kotun Ebonyi ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda sun kashe wani Chinonso Elom.

Wadanda aka yankewa hukuncin su ne; Anthony Elom, Chibueze Onwe, Chukwuemeka Ugah da Uchenna Odono, dukkansu ’yan garin Ohaukwu.

Alkalin kotun, Esther Otah, ta ce duk da Anthony ne ya harbe Elom, sauran sun hada baki da shi, don haka kowa na da hannu a kisan mutumin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com