Hotuna: Gwamnati Ta Aurar da Zawarawa da Marayu, Sun Samu Kayan Daki a Zamfara

Hotuna: Gwamnati Ta Aurar da Zawarawa da Marayu, Sun Samu Kayan Daki a Zamfara

  • Gwamnatin Zamfara ta yi wa marayu, zawarawa da marasa galihu 200 aure, inda ta gwangwaje su da kayan daki da sadaki
  • Shirin ya haɗa da ba ma'auratan kayan daki, gado da katifa da sadaki, sannan an ba wasu horo kan kiwon kaji da kwamfuta
  • Uwargidar gidan gwamnan Zamfara ta ce an shirya aurar da zawaran ne domin tallafawa marasa galihu da rage fatara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta hannun hukumar kula da zakka da sadaki, ta ɗaura auren gata ga mata 200 da suka haɗa da marayu, zawarawa da masu ƙaramin ƙarfi.

An gudanar da bikin gatan ne a ranar Litinin, a matsayin shirin karshe na ayyukan jin ƙai na hukumar na shekarar 2025, da suka haɗa da tallafin jari, biyan basussuka, ba da horo da koyar da sana’o’i.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya sanya ranar fara azumi, addu'o'i, ya shawarci Musulmi, Kirista

Gwamnatin Zamfara ta aurar da zawarawa da marayu 200
Uwargidan gwamnan Zamfara tana ba da sadaki da kayan daki ga sababbin ma'aurata. Hoto: @AM_Saleeeem
Source: Twitter

Uwargidar gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bayyana cewa shirin ya jaddada kudurin gwamnati wajen tallafa wa marasa galihu da ƙara musu martaba a cikin al’umma, in ji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ba biya sadaki, kayan daki

Uwargidar gwamnan ta ce matan da aka ɗaura wa aure sun samu kujeru, katifu, gado da sauran kayan daki domin fara rayuwa cikin mutunci. Haka kuma kowacce ta samu sadakin ₦200,000.

Ta ce shirin tallafawa marasa galihun ya haɗa da warware basussuka a kotunan shari’a da kurkuku ga mutanen da suka cancanta, domin su sake rayuwa cikin mutunci.

A cewar ta:

“Mun ba da tallafin jari ga ’yan kasuwa 200, inda kowane ya samu ₦50,000. Mun horar da mutane 100 kan kiwon kaji tare da ba su jari. Mun kuma horar da yara 10 kan koyon kwamfuta tare da ba su ƙananan kwamfutoci.”

Alfanun aurar da zawarawa da marayu

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Sakataren hukumar Zakka da sadaki, Malam Habib Balarabe, ya ce shirin ya na tattare da dukkan manyan manufofi na rage talauci a Zamfara.

Ya bayyana cewa an shirya auren ne domin tabbatar da cewa mata marasa galihu sun samu damar yin rayuwar aure, tare da ba wasu tallafi domin su fara kananan sana'o'i a gidajensu.

A cewar Malam Habib Balarabe:

“Mun shirya wannan domin rage fatara da rage yawan barace-barace a tituna.”
Uwargidan gwamnan Zamfara ta yi magana a wajen aurar da zawara da marayu 200
Uwargidan gwamnan Zamfara ta na jawabi ga sababbin ma'aurata. Hoto: @AM_Saleeeem
Source: Twitter

Amarya ta fi son aure kan komawa makaranta

Jaridar Punch ta rahoto daya daga cikin amaren, Zainab Mohammed mai shekara 17, ta nuna farin cikinta, inda ta ce ta fi son aure fiye da komawa makaranta.

Zainab Mohammed ta ce:

“Ina matuƙar godiya ga Allah. Ina farin ciki. Ni ba na wani sha'awar son komawa makaranta, aure ya fi min gaskiya.”

Bayan kayan daki da sadaki, gwamnati ta rarraba tallafin ₦30,000 ga sababbin ma’auratan.

An kashe N2.5bn a auren gata a Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kano ta ce daukar nauyin auren gata ba abu ne da ake yi a Najeriya kawai ba, ana yi a wasu wuraren.

Kara karanta wannan

Tuhume tuhumen da DSS ke yi wa matashin da ya nemi a kifar da gwamnatin Tinubu

Daraktan hukumar Hisbah, Abba Sa’idu Sufi, ya ce kasashen da suka ci gaba kamar Amurka, Iran, da Canada su na irin wannan.

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin kashe Naira biliyan 2.5 domin dakile barna da yaduwar zinace-zinace da sun sabawa addini.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com