Gurbatar Ruwa: An Gano Babban Hadarin da ke Tunkaro Mutane a Kebbi da Jihohi 2

Gurbatar Ruwa: An Gano Babban Hadarin da ke Tunkaro Mutane a Kebbi da Jihohi 2

  • Hukumar NiHSA ta gano matsalar gurbacewar ruwan da mutane ke amfani da shi daga burtsatse, rijiyoyi da sauran nau'in ruwan kasa
  • Shugaban hukumar na kasa, Umar Mohammed ya gargadi jama'a su yi taka tsantsan domin an gano ruwan na dauke da sindarai masu illa
  • Masana sun fara gargadin mazauna yankunan da aka gano wannan matsala a jihohi uku da su daina shan ruwan da ba a tace ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta gano wasu sindarai masu hadari irin na guba a cikin ruwan kasa, wanda ya kunshi burtsatse da rijiyoyi a wasu jihohin Najeriya.

Wannan ya sa gwammatin ta yi gargadi cewa mazauna yankunan da abin ya shafa na iya zama cikin haɗarin shan guba da kuma kamuwa da ƙwayoyin cututtuka masu hatsari.

Kara karanta wannan

Mutane sun ga abin da ba su taba gani ba bayan maida Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato

Shugaban NiHSA, Umar Mohammed.
Hoton shugaban hukumar NiHSA na kasa, Umar Mohammed a ofis Hoto: @nihsa_ng
Source: Twitter

Premium Times ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin sabon rahoton kimanta ingancin ruwa da tasirin ambaliyar ruwa na hukumar Nigeria Hydrological Services Agency (NiHSA).

Hukumar NiHSA ta ce Jihar Kogi ce ta fi fuskantar babban matsala, musamman a ƙaramar hukumar Lokoja, sai kuma Legas da Kebbi.

Shugaban NiHSA, Umar Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

An gargadi mutane a jihar Kogi

Mohammed ya ce binciken da aka yi daga rijiyoyi da burtsatse a yankunan da abin ya shafa ya nuna cewa ruwan na ɗauke da sinadarai masu matuƙar haɗari kamar gubar ƙarfe, Cadmium, Nitrite, da Fluoride.

Haka kuma ya ce an gano ƙwayoyin cuta irin su, E. coli, Streptococcus da Salmonella duk a cikin gurbataccen ruwan kasa a jihar Kogi.

Umar Mohammed ya ce:

“Wadannan gurbatattun sinadarai da ke fitowa daga magudanan ruwa da suka lalace, sharar da aka zubar a ƙasa, da tsofaffin bututun ruwan sha na da babban hadari ga lafiyar jama’a.”

Kara karanta wannan

Birnin Shehu ya yi baƙo, DSS ta maida Nnamdi Kanu Sokoto, zai zagaye Najeriya

Ya jaddada cewa ambaliyar ruwa da ke yawan faruwa a yankunan kogin jihar Kogi ta ƙara tsananta matsalar.

Lagos da Kebbi na fuskantar hadari

A jihar Legas, rahoton ya gano matsalar gurbacewar ruwa musamman Ikeja da Ikoyi, inda aka gano sinadarai da ƙwayoyin cuta a ruwan rijiyoyi da burtsatse a yankuna da dama.

A Jihar Kebbi kuwa, musamman a ƙaramar hukumar Argungu, an samu sinadarin Arsenic mai tsananin yawa (0.75–4 mg/L) da ƙwayoyin cuta da dama.

Hukumar NiHSA.
Hoton jami'an hukumar NiHSA suna aikin gwale-gwale a gefen wani ruwan tafki Hoto: @NiHSA_ng
Source: Twitter

NiHSA ta ce yawan amfani da ruwan da ya ƙunshi sinadirin arsenic na iya haifar da lalacewar hanta da tsananin cututtukan hanji.

Masani a fannin ruwa, Mathew Ajisafe, ya shawarci mazauna yankunan da su daina shan ruwan rijiyoyi da burtsatse, yana mai kira ga jihohi da su gaggauta samar da ruwan da aka tace ga jama’a.

Wani malamin lafiya na fannin kula da tsaftar muhalli, Muhammad Bello ya shaida wa Legit Hausa ce har yanzu mutane na bukatar da wayar da kai kan illar shan ruwa mara tsafta.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Matasa 16 da suka gama digiri sun mutu a hanyar zuwa sansanin NYSC

Ya ce ya kamata gwamnati ta tashi tsaye domin wani lokacin gargadi da ankararwa kadai ba za su magance irin wadannan hadurra da ke tunkarar jama'a ba.

"Idan ka duba, wannan binciken a wasu wurare kadai aka yi shi, to ina tabbatar maka akwai wuraren da duk wanda ya ke da ilimi kan harkar cututtuka ba zai shiga ba.
"Ruwan burtsatse yana tattare da matsloli da dama musamman yanzu da ba a bin dokokin lafiya wajen gina shi, ya kamata mutane su kula, gyara kayanka, ba zai zamo sauke mu raba ba," in ji shi.

'Yan Najeriya sun koka da yajin aikin liktoci

A wani rahoton, kun ji cewa duk da wannan matsala da ake tunkara, likitoci na ci gaba da yajin aiki saboda kin biya maau bukatunsu a fadin Najeriya.

Mutane a Najeriya musamman marasa lafiya sun ahiga mawuyacin hali aaboda galibi ba za su iya biyan kudin jinya a asibitocin kudi ba.

Kungiyar lokitoci ta NARD ta tsunduma yajin aiki ne a ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamba, 2025 kuma ta ce ba za ta janye ba sai an biya bukatunta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262