Nnamdi Kanu: 'Yan Majalisa 44 Sun Tura Wasika ga Tinubu kan Sakin Shugaban IPOB
- 'Yan Majalisar Wakilai 44 sun fara kokarin lallaba Bola Ahmed Tinubu domin ya saki shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
- Sun rubuta wasika kai tsaye zuwa ga Shugaba Tinubu kan shari'ar da ake wa jagoran masu fafutukar ballewa daga Najeriya
- Wasikar ta bayyana cewa ci gaba da tsare Nnamdi Kanu na kara dagula harkar tsaro a Kudu maso Gabashin Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugabanni da masu ruwa da tsaki musamman daga Kudu maso Gabashin Najeriya na ci gaba da kiraye-kirayen a saki Nnamdi Kanu.
Kanu, wanda shi ne shugaban kungiyar 'yan aware ta IPOB, wacce Najeriya ta ayyana a matsayin kungiyar ta'addanci a shekarun baya, na ci gaba da fuskantar shari'a.

Source: Facebook
'Yan Majalisa 44 sun tura wasika ga Tinubu
Premium Times ta ruwaito cewa 'yan Majalisar Wakilai 44 sun aika wasika ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, suna rokon ya ba da umarnin sakin Nnamdi Kanu nan take.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun kuma shawarci shugaban kasa da ya fara tattaunawar siyasa mai faɗi domin warware matsalolin tsaro da siyasar Kudu-maso-Gabas.
‘Yan majalisar, wadanda suka fito daga jam’iyyun siyasa daban-daban, daga Arewa da Kudu, sun aika takardar mai shafuka biyu ga Shugaba Tinubu.
Abin da wasikar 'yan majalisa ta kunsa
A cikin wasikar, ‘yan majalisar sun roƙi shugaban kasa da ya umurci Antoni Janar ya yi amfani da huruminsa na doka wajen dakatar da shari’ar Nnamdi Kanu.
A cewarsu, hakan zai buɗe kofar tattaunawa da za ta samar da mafita ta dindindin da adalci, suna masu cewa tsawon lokacin da Kanu ya shafe a tsare ya ƙara tabarbarewar tsaro a Kudu.
Sun kafa hujja da yadda aka samu zaman lafiya a yankin Neja Delta ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna tsakanin gwamnati da tsagerun yankin.
A rahoton Daily Trust, wani sashen wasikar ya ce:
"Muna roƙon Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya umurci AGF da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi ya dakatar da gurfanar da Mazi Nnamdi Kanu.”
Sunayen wadanda suka sa hannu a wasika
Wasikar ta samu sanya hannun manyan ‘yan majalisar wakilai ciki har da Ikenga Ugochinyere, Obi Aguocha, Murphy Osaro, Peter Akpanke, Mudshiru Lukman, Paul Nnamechi, Sunday Cyriacus, Obed Shehu da Dominic Okafor.
Sauran sun hada da Ugwu Emmanuel, Daniel Ago, Chike Okafor da Adam Ogene, Emeka Chinedu, Chimaobi Sam, Alex Ikwechegh, Donatus Matthew, Ibe Osonwa, Okey-Joe Onuakalusi, Thaddeus Atta da Udema Okonkwo.

Source: Twitter
Ragowar sun kunshi Cyril Godwin, Chinwe Nnabuike, Kana Nkemkama, Peter Aniekwe, Gwachem Maureen, Anayo Onwuegbu, Nwobosi Joseph, Amobi Godwin, Blessing Amadi, Anthony Adepoju da Joshua Gana.
Haka zalika Chris Nkwonta, Emeka Idu, Peter Uzokwe, Matthew Nwogu, Tochukwu Okere, Benedict Etanabene, Godwin Offiono, Ngozi Okolie da Nnamdi Ezechi sun rattaba hannu a wasikar.
Nnamdi Kanu ya hargitsa zaman kotu
A baya, kun ji labarin cewa an samu yamutsi a babbar kotun tarayya da ke Abuja, yayin zaman yanke hukunci shari’ar shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.
Kanu ya dage cewa ba za a iya karanta hukuncin ba illa sai idan kotu ta nuna masa dokar da ta haramtawa wanda ake tuhuma damar gabatar da jawabi a rubuce.
Rashin jituwa tsakanin Kanu da kotu ya jawo tsaikon shari’a yayin da mai shari’a, James Omotosho, ya dakatar da zaman don bai wa jami’an tsaro damar fitar da shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



