'A Yi Hattara': Yadda Maganin Sauro Ya Kashe Miji da Mata da Ƴaƴansu 2 a Kano

'A Yi Hattara': Yadda Maganin Sauro Ya Kashe Miji da Mata da Ƴaƴansu 2 a Kano

  • Miji da mata da ƴaƴansu biyu sun bakunci lahira yayin da maganin sauro da suka kunna ya jawo gobara a gidansu
  • Hukumar kashe gobara ta Kano ta bayyana cewa maganin sauron da aka kunna ne ya haddasa gobarar da ta kona gidan
  • Masana sun gargadi jama’a cewa shakar hayakin maganin sauro guda daya yana kusan shakar sigari 75 zuwa 137

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - A kalla mutane huɗu 'yan gida daya ne suka rasa rayukansu a wata mummunar gobara da ta tashi a safiyar Laraba a jihar Kano.

An ce gobarar ta tashi a wani gida da ke Kundila, Layin Baba Impossible, cikin karamar hukumar Tarauni a babban birnin na Kano.

Maganin sauro ya jawo gobara ta tashi a wani gida a Kano, mutane hudu sun mutu.
Hoton maganin sauro ya na ci da wuta. Hoto: Andrei310 / Getty Images
Source: Getty Images

Maganin sauro ya jawo gobara a Kano

Gobarar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 4:13 na Asubah, ta ƙone ginin bene ɗaya gaba ɗaya kafin a samu damar kai ɗauki ga waɗanda ke ciki, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da hare hare, ƴan sanda sun yi karin haske kan zargin hari a cocin Gombe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta samu kiran gaggawa daga ɗaya daga cikin ma’aikatanta, HFS Abba Datti.

HFS Abba Datti ya ruwaito cewa gobarar na ci gaba da ƙona gidan lokacin da ya kira, inda nan da nan tawagar gaggawa daga hedikwatar NFS ta nufi wurin don aikin ceto.

Da jami’an suka isa wurin, sun tarar da ginin bene mai faɗin kafa 40 zuwa 30 yana cin wuta, tare da dakuna da falo da kicin duk sun kama da wuta.

Hukumar ta tabbatar da cewa maganin sauro da aka kunna a falon gidan ne ya haddasa tashin gobarar.

Yadda miji, mata da 'ya'yansu suka mutu

Mutane biyar ne ke cikin gidan lokacin da gobarar ta tashi: mai gidan, Shodandi mai shekara 43, matarsa Rafi’a mai shekara 30, 'ya'ya mata biyu — Mardiya mai shekara uku da Yusira mai shekara ɗaya da rabi — da ɗansu Aminu mai shekara 12.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Kakakin hukumar, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da cewa mahaifin, mahaifiyar da ƙananan yaransu biyu sun kone kurmus kafin jami’ai su iya shiga ciki.

Sai dai an samu nasarar ceto ɗansu na fari, Aminu Shodandi, wanda yanzu haka yana samun kulawar likitoci, in ji rahoton Punch.

Hukumar ta yi ta’aziyya ga iyalan tare da gargadi ga mazauna jihar da su yi hattara da amfani da maganin sauro musamman a lokacin sanyi da ke kawo yawaitar gobara.

Masana sun ce shakar maganin sauro guda daya yana iya zama daidai da shakar hayakin taba-sigari 75 zuwa 137.
Wani mutumi ya na kunna maganin sauro. Hoto: Chalffy / Getty Images
Source: Getty Images

Masana sun bayyana illar maganin sauro

Masu bincike daga Jami’ar Sydney sun bayyana cewa maganin sauro na iya fitar da hayaki mai tsananin haɗari, wanda ke ɗauke da sinadaran da ke jawo tangardar numfashi idan aka rufe ɗaki.

Rahoton binciken da aka wallafa a shafin jami'ar ya nuna cewa kunna maganin sauro ɗaya na iya zama daidai da shakar hayakin taba-sigari 75 zuwa 137.

Ba a tabbatar da cewa yana haifar da cutar huhu kai tsaye ba, amma masana sun ce zama cikin hayakin na dogon lokaci na iya janyo matsalolin numfashi sosai.

Kara karanta wannan

Cocin katolika ya fadi halin da ake ciki bayan sace dalibai a Neja

A zantawar Legit Hausa da Dr. Shamsu Abubakar na babbar asibitin koyarwa na tarayya da ke Katsina, ya yi magana bayani game da illolin maganin sauro.

A cewar Dr. Shamsu:

"Shakar hayakin maganin sauro ya na kusan dai dai da shakar hayakin sigari, duk da cewa sinadaran da ke cikinsu sun bambanta, amma illar kusan daya ne.
"Ga masu cutar numfashi, watau Asma, to shakar hayakin maganin sauro yana tado da da wannan cuta, musamman a yara, yana gurbata masu numfashinsu.
"Sannan akwai wani ciwo, shi ma na hanyar iska ne, da yake sanya hanyar iskar ta takure, ya sanya mutum ya rika tari, yana fitar da majina, shi ma yawan shakar maganin sauro zai iya tayar da wannan cuta.
"Kuma wannan cuta tana dadewa sosai a jikin mutum, sannan ta na hana mutum ya shaki iska yadda ya kamata.
"Sannan, dadewa ana shakar maganin sauro zai iya kawo hadarin kamuwa da cutar kansa, ba wai yana kawo kansa ba, yana kara kawo hadarin kamuwa da ita.
"An san cewa akwai hadurra da dama da idan suka yi yawa ne suke jawo cutar kansa. To daya daga ciki shi ne wannan maganin sauron, saboda wadannan sinadaran da ke cikinsa.

Kara karanta wannan

Asiri ya bankadu: An kama magidanci yana neman sulalewa da gawar matarsa a babur

"Sannan yawan shakar hayakin maganin sauro na sanya makoshi ya rika yin ba dadi, har a rika jin zafi ko makoshi ya bushe, sannan yana jawo kumburin ido, ko a ji ido na zafi ko ciwo."

Dr. Shamsu ya kuma ce hayakin maganin sauro yana gurbata yanayi, inda ya ce ba a samu lafiyayyar iska mai kyau a inda hayakin maganin sauro ya gurbata.

Matashi ya sha maganin sauro a Benue

A wani labarin, mun ruwaito cewa, saura kiris wani matashi da ke shirin yin aure, mai suna Adakole ya hallaka kansa yayin da aka dakatar da shirin MMM.

Adakole ya kwalkwali maganin sauro a Otukpo, jihar Benue lokacin da ya samu labarin daskarewar bankin Mavrodi Mondial Moneybox MMM.

An ce matashin ya sanya N300,000 a cikin wannna tsari na samun kudi wanda zai yi amfani da su a bikinsa, amma aka hana kowa cire kudinsa daga MMM.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com