Daskarewan MMM: Wanni matashi ya sha maganin sauro a jihar Benue

Daskarewan MMM: Wanni matashi ya sha maganin sauro a jihar Benue

- Wani matashi mai shirin aure mai suna Adakole ya kusa hallaka kansa yayinda aka daskarar da MMM

- Mutumin ya kwakwali maganin sauro lokacin da ya samu labarin daskarewar MMM

- Abokinshi yace ya sanya N300,000 domin kudin ya kara yawa kafin ranan aurensa,laraba 28 ga disamba

Daskarewan MMM: Wanni matashi ya sha maganin sauro a jihar Benue
Daskarewan MMM: Wanni matashi ya sha maganin sauro a jihar Benue

Saura kiris Wani matashi mai shirin aure mai suna Adakole ya hallaka kansa yayinda aka daskarar da MMM.

Adakole ya kwakwali maganin sauro a Otukpo, jihar Benue lokacin da ya samu labarin daskarewar bankin Mavrodi Mondial Moneybox MMM.

Akwai tashin hankali a Najeriya lokacin masu shafin yanar gizon suka fadawa yan Najeriya cewa sun daskarar da shafin na tsawon wata 1 domin tabbatar da tsaro.

KU KARANTA:Hadarin jihar Katsina

Shi kuma Adakole ,wanda ke shirin aure, bayan samun wannan labara,ya sha maganin sauri kawai.

Abokinsa yace Adakole ya kusa haukacewa klokacin da ya samu labarin cewa abun ya daskare.

Abokinsa yace :

“Kole abokin na ne, tare muka taso a Ugbokolo ,amma lokacin da ya je Abuja domin ganawa da faston budurwarsa,yace wani ya gayyacesa zuwa yin MMM amma ni da budurwarshi mun masa gargadi amma yace ba cuta bane.

“Ya sanya N300,000 da yake shirya ma aurensa a ranan 28 ga watan disamba. Da safe sai y kira ni cewa I duba yanar gizo domin tabbatar da cewa shin da gaske ne an daskarar da shafin, sai nace masa hakane,kawai ya fara iwu.

“Danaji iwun kawai sai na je gidansa da wuri a Sabon gari ,sainaga ya sha maganin saurn Raid. Sai na kira budurwarshi na fada mata. A yanzu dai yana asibiti.”

Ku kasance tare da mu: https://www.facebook.com/naijcomhausa, https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel