Kano na cikin Alheri, Gwamna Abba Ya Sanya Hannu kan Dokar Kafa Sabuwar Kwaleji
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan dokar kafa kwalejin Gaya domin fadada ilimi da bunkasa fasaha a Kano
- Majalisar Kano ta fara amincewa da kudirin bayan rahoton kwamitin mutum 14 da aka nada domin tabbatar da kafa kwalejin
- Sabuwar makarantar za ta samar da ayyukan yi, karuwar fasaha da ci gaban tattalin arziki ga Gaya da yankunan makwabta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu a kan dokar kafa kwalejin fasaha ta Gaya, wacce za a yi a karamar hukumar Gaya.
Rahoto ya nuna cewa sanya hannu kan dokar wani muhimmin mataki ne da zai fadada damar karatun gaba da sakandare da kuma bunkasa fasaha a Kano.

Source: Twitter
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yunkurin karfafa ilimi da fasaha a Kano
Sanusi Dawakin Tofa ya sanar da cewa an gudanar da bikin rattaba hannun a fadar gwamnati tare da shugabannin majalisar dokoki ta jihar.
Gwamna Abba ya ce kafa kwalejin Gaya wani muhimmin ginshiki ne a burin gwamnatin sa na farfado da ilimi a matakai daban-daban da kuma samar da gajeru da dogayen kwasa-kwasan fasaha ga matasa.
Sanarwar ta rahoto Gwamna Abba Yusuf yana cewa:
“Wannan matakin babbar nasara ce ga yunƙurin mu na inganta ilimi. Kwalejin Gaya za ta bai wa matasanmu damar koyon fasahohi da za su inganta tattalin arziki.”
Gwamnan ya yaba wa majalisar dokoki bisa saurin tabbatar da kudirin, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewar su wajen kara inganta ilimi a Kano.
Gudunmawar kwamitin kafa kwalejin Gaya
Kudirin kafa sabuwar makarantar ya fito ne bayan rahoton kwamitin mutum 14 da gwamnatin Kano ta kafa a Agusta 2025 domin tsara dukkanin matakan bude kwalejin.
Kwamitin, wanda mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya kaddamar, ya yi aiki karkashin jagorancin Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, shugaban jami’ar Northwest.
Mun ruwaito cewa, ayyukan da kwamitin ya gudanar sun hada da:
- Shirya wa da tura kudirin kafa kwalejin ga majalisa, da tabbatar da amincewa da shi.
- Neman amincewar hukumar kula da ilimin fasahohi ta NBTE.
- Kula da fara gina makarantar.
- Daukar ma’aikata da fara jarabawar shigar karatu ga dalibai.
- Tattaunawa da masu ruwa da tsaki don ganin kwalejin ta fara aiki.
Tun a lokacin, gwamnatin Abba ta umurci kwamitin da ya tabbatar da kwalejin ta fara karatu kafin zuwan sabuwar shekarar karatu.

Source: Facebook
Amfanin kwalejin Gaya jihar Kano
Dawakin Tofa ya bayyana cewa kafa sabuwar kwalejin fasahar na da nasaba da manufofin gwamnatin Kano na saukaka samun ilimi da kuma bunkasa tattalin arziki a jihar.
A cewarsa, kwalejin za ta samar da dimbin ayyukan yi, habaka fasaha, kirkire-kirkire da kuma inganta tattalin arziki a Gaya da yankunan da ke makwabtaka.
Gwamnatin Kano ta ce wannan mataki wani bangare ne na sabuwar dabarar ilimi da nufin canza fasalin karatun fasaha da kimiyya domin mikawa matasa damar gina rayuwarsu cikin alfahari.
Za a tilasta koyarwa da harshen Hausa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar Kano ta fara duba kudurin doka da zai wajabta koyarwa da harshen Hausa a makarantun jihar.
Hon. Musa Ali Kachako ne ya dauki nauyin kudurin wanda ya ce zai taimaka wajen inganta fahimtar dalibai da rage faduwa a jarrabawa.
Kudurin ya shiga hannun Kwamitin Ilimi na majalisar dokokin domin karin nazari da bayar da shawarwari kafin karatun sa na gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


