Abu namu maganin a kwabemu: Gwamnati za ta gina kwalejin kimiyya da fasaha a Daura

Abu namu maganin a kwabemu: Gwamnati za ta gina kwalejin kimiyya da fasaha a Daura

Sanatoci daga majalisar dattawa sun amince a kafa sabuwar kwalejin kimiyya da fasaha a garin Daura ta jahar Katsina, domin habbaka ilimin kimiyya a tsakanin al’ummar dake wannan yanki, tare da kawo cigaba a yankin gaba daya.

Majiyar Legit.com ta ruwaito shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki ne ya bayyana haka ta bakin dan majalisa mai wakiltar Abuja a majalisar dattawa, Sanata Philip Aduda a yayin taron sauraron ra’ayin jama’an kan batun kafa kwalejin.

KU KARANTA: Rundunar Yansandan Najeriya ta yi ram da wasu miyagun barayin mutane 10 a Katsina

Sauran makarantun ilimi da majalisar ta amince a kafa sun hada da Jami’ar ilimi ta gwamnatin tarayya a Aguleri jahar Anambra, kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya a Ikom jahar Krosribas, da kuma cibiyar kere kere ta kasa a Uromi, jahar Edo.

Abu namu maganin a kwabemu: Gwamnati za ta gina kwalejin kimiyya da fasaha a Daura
Daura
Asali: Facebook

Sanata Tijjani Yahaya Kaura, mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da ilimin gaba da sakandari da gidauniyar ilimi ya bayyana cewa majalisar za ta samar da dokokin da zasu kafa wadannan makarantu don zama ginshiki a garesu.

Da yake jawabinsa, Sanata mai wakiltar yankin Daura a majalisar dattawa, Sanata Ahmad Babba Kaita, wanda shine ya kirkiri kudurin kafa kwalejin, ya bayyana ma mahalarta taron cewa ya tsohon Sanatan Daura, marigayi Sanata Bukar Mustapha ne ya fara kokarin samar da kuduri.

Abin mamaki a cewar Babba Kaita shine duk da dimbin tarihin da Daura take da shi, amma bata da wani cibiyar gwamnatin tarayya. “ Yankin Daura ne kadai bata da wata cibiyar gwamnatin tarayya a cikinta, idan aka kafa kwalejin, za ta samar ma matasan guraben karatu, don haka wannan abune mai kyau.”

Haka zalika shima kaakakin majalisar dokokin jahar Katsina, Abubakar Yahaya Kusada ya shaida ma taron cewa kafa wannan kwaleji zai daidaita Daura da sauran yankunan jahar Katsina, musamman game da samun cibiyoyin gwamnatin tarayya.

Daga cikin wadanda suka mara ma wannan kuduri baya a yayin zaman kwamitin akwai Sarkin Daura Alhaji Umar Farouq, wanda ya samu wakilcin Sarkin Sudan, Wazirin Daura, Alhaji Ibrahim Alhassan, da Sarkin Kudu, Injiya Abdullahi Bukar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel