Tashin Hankali: An Tattake Mutane a Gidan Bello Matawalle, Mutum 1 Ya Mutu

Tashin Hankali: An Tattake Mutane a Gidan Bello Matawalle, Mutum 1 Ya Mutu

  • Mutum ɗaya ya mutu, shida sun ji rauni a cunkoson jama’a da ya faru a gidan Ministan Tsaro Bello Matawalle a Gusau
  • Lamarin ya faru ne yayin tarbar Matawalle da masoya suka yi, inda cunkuson ya jawo aka rika tattake mutane, har wani ya mutu
  • Majiyoyi sun bayyana cewa yanzu haka an fara bincike domin gano ko akwai sakaci a wannan mummunan lamari da ya afku

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - An samu wani mummunan cunkoson jama’a a gidan ministan tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ke Gusau, jihar Zamfara.

Wannan turmutsutsi da aka samu a gidan ministan tsaro ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya tare da jikkatar wasu mutane akalla shida.

An samu asarar rai a cunkuson mutane da aka samu a gidan ministan tsaro, Bello Matawalle a Gusau.
Ministan tsaro, Bello Matawalle na gabatar da jawabi a ziyarar da ya kai mahaifarsa, Gusau. Hoto: @Bellomatawalle1
Source: Twitter

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:30 na daren ranar Alhamis, a lokacin da gungun masoya suka taru domin tarbar ministan wanda ya dawo garin domin wani taron APC, in ji rahoton Zagazola Makama.

Kara karanta wannan

Da gaske Donald Trump ya ce zai cafke Bola Tinubu cikin sa'o'i 24?

Mutum 1 ya mutu a gidan ministan tsaro

Rahotanni sun nuna cewa taron ya haddasa cunkoso fiye da ƙima, lamarin da ya haifar da rikice-rikice, turmutsutsi da kakkarfar zuga, har ya rikide zuwa tattake mutane da ya yi sanadiyyar mutuwa da jin raunuka.

Wadanda abin ya rutsa da su sun haɗa da matashi mai suna Khalifa Uzairu, mai shekaru 23, wanda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa a babban asibitin Farida.

Sauran da suka jikkata sun haɗa da Ayuba Sani, Muhammadu Adams, Aliyu Aminu, Shaaban Hamisu da Inusa Musa Shehu, waɗanda dukkansu aka garzaya da su asibiti domin kulawa.

Bisa bayanan da hukumomi suka fitar, babu wanda ke cikin mawuyacin hali, kuma jami’an lafiya suna ci gaba da ba su kulawa ta gaggawa.

Hukumomi sun fara bincike

A cewar majiyoyi, jami’an tsaro sun isa wurin da gaggawa domin shawo kan halin da ake ciki da hana tashin hankali.

Kara karanta wannan

'Ka nemi kashe ni,' Wike ya yi martani mai zafi ga Buratai bayan rigima da soja

An fara bincike domin gano musabbabin lamarin da kuma ko akwai sakaci ko laifi daga wasu bangarori, kamar yadda rahoton Makama ya nuna.

Hukumomin tsaro sun gargadi jama’a da su kasance masu bin dokoki da natsuwa a irin manyan tarurrukan da ake gudanarwa, domin kare rayuka da dukiyoyi.

Dandazon mutane ne suka tarbai ministan tsaro, Bello Matawalle a Gusau wanda ya jawo mutuwar mutum 1.
Dandazon mutane sun taru a wurin taron siyasar da ministan tsaro, Bello Matawalle ya halarta a Gusau. Hoto: @Bellomatawalle1
Source: Twitter

Martanin minista, Bello Matawalle

A wani saƙo da Ministan Tsaro Bello Matawalle ya wallafa a shafinsa na X, awanni kafin aukuwar lamarin, ya bayyana farin cikinsa da irin gagarumar tarbar da masoyansa suka yi masa a Gusau.

Ya rubuta cewa:

“A yau, Alhamis, 13 ga Nuwamba, 2025, na samu shiga Garin Gusau, Jihar Zamfara, domin ganawa da masoya da magoya bayan jam'iyyar mu ta APC, a gobe juma’a, a sakateriyar jam'iyya ta jiha dake Gusau.
"Naji daɗi matuƙa da irin kyakkyawan tarba dana samu daga dimbin masoya da magoya baya. Wannan karamci ya kara man kwarin guiwa akan wannan tafiya da muke yi ta inganta rayuwar al’ummar mu.”

Sai dai duk da wannan farin ciki, wanzuwar cunkoson har ya jawo asara ta rayuwa ta tayar da hankalin jama’a, inda ake sa ran ofishin ministan zai fitar da karin bayani nan gaba.

Kara karanta wannan

Malami ya fahimci muhimmin abu game da matashin sojan da ya yi gaba da gaba da Wike

'PDP za ta kai wa Matawalle hari?'

A wani labarin, mun ruwaito cewa, PDP mai mulki a Zamfara ta karyata zargin cewa tana shirin kai hari ga tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Jam’iyyar ta ce labarin ƙarya ne da aka kirkira don tada hankalin jama’a da haifar da rikici yayin da Matawalle ke shirin ziyartar mahaifarsa.

PDP ta ce hankalinta yanzu yana kan babban taron zaben shugabanninta na kasa da za a yi a Ibadan, har ta zargi APC da shirya makarkashiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com