Manyan Abubuwa 3 da Suka Jawo Ake Kashe Bayin Allah a Neja da Jihohin Arewa 5

Manyan Abubuwa 3 da Suka Jawo Ake Kashe Bayin Allah a Neja da Jihohin Arewa 5

  1. Fadar shugaban kasa ta danganta rashin tsaro a Arewa ta Tsakiya da rikicin mallakar ƙasa, satar ma’adinai da ta’addanci
  2. Gwamnati ta kafa ƙungiyoyin zaman lafiya a kananan hukumomi 121 don haɗa shugabanni, manoma da makiyaya
  3. Shugaba Bola Tinubu dai ya ba da umarni da a gaggauta farfado da ilimi a Arewa don rage ayyukan ta'addanci a shiyyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Fadar shugaban kasa ta bayyana wasu manyan dalilai da ke haifar da kashe kashen bayin Allah da rashin tsaro a Arewa ta Tsakiya.

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce mallakar ƙasa ba bisa ka’ida ba, satar ma’adinai da kuma ta’addanci su ne ummul aba'isin kisan mutane.

Fadar shugaban kasa ta yi magana game da ayyukan ta'addanci a Arewacin Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya na jagorantar taron NEC a fadar shugaban kasa Abuja. Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Manyan dalilan kashe kashe a Arewa

Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan hulɗar al’umma (Arewa ta Tsakiya), Dr. Abiodun Essiet, ce ta bayyana hakan a fadar shugaban kasa, Abuja, in ji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Abiodun Essiet ta ce rikicin yankin Arewa ya samo asali ne daga tsofaffin matsaloli na tarihi da rikicin albarkatun ƙasa.

A cewarta, wadannan rikice-rikice ne suka ƙara ta’azzara sakamakon ayyukan ƙungiyoyin 'yan ta'adda da ke cin gajiyar rashin kwanciyar hankalin garuruwa.

“Mun gano cewa rashin aminci tsakanin al’umma, mallakar ƙasa da ta’addanci da kuma satar ma’adinai sune manyan abubuwan da ke haifar da tashe tashen hankula."

- Dr. Abiodun Essiet.

An kafa ƙungiyoyin zaman lafiya a Najeriya

Dr. Essiet ta ce gwamnati ta kafa tsarin zaman lafiya a kananan hukumomi 121 da ke Arewa ta Tsakiya — ciki har da 32 a jihar Neja, 21 a Kogi da 23 a Benue.

A cewarta, wannan tsarin zai haɗa shugabannin gargajiya, ƙungiyoyin manoma da makiyaya, da matasa domin kawo fahimtar juna da sasanci a yankunan da ke fama da rikici.

Ta kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya ta gano cewa rashin kyawun hanyoyi, musamman a tsakanin Kogi da Kwara, ya taimaka wajen yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Hafsan sojan kasa Janar Shaaibu ya gana da Tinubu, ya ba shi bayanan tsaro

“Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarni ga ma’aikatun da suka dace su gaggauta gyaran hanyoyin yankin."

- Dr. Abiodun Essiet.

Abdullahi Tanko Yakasai ya ce gwamnati na kokarin mayar da yara zuwa makaranta
Hoton shugaban kasa Bola Tinubu da na Abdullahi Tanko Yakasai. Hoto: @dawisu
Source: Facebook

An waiwayi yaran da ba sa zuwa makaranta

Shi kuma mai ba shugaban kasa shawara kan Arewa maso Yamma, Abdullahi Tanko-Yakasai, ya ce ofishinsa yana aiki don rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Yakasai ya ce gwamnati na bayar da kayan karatu, kayan makaranta da littattafai ga yara masu rauni, tare da tallafawa iyaye don dawo da su cikin tsarin ilimi.

Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa Tinubu ya amince da shirin tallafin taki ga manoma, rance ga ɗalibai da kuma wayar da kai kan dokokin haraji da rajistar katin zaɓe.

Sabuwar kungiyar ta'addanci a Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sabuwar ƙungiyar ta’addanci da ake kira Mahmuda ta ƙara kaimi wajen kai hare-hare a jihar Kwara.

Aƙalla mutane shida, ciki har da matashi dan shekara 19 da wani ɗan sa-kai, sun rasa rayukansu a harin da aka kai Ilesha Baruba da Kemaanji.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada belin tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, ya fito bayan mako 3 a kurkuku

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya kai ziyara Kaiama tare da jami’ai domin duba matsalar da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com