'Ba Kai ba Shugabancin Najeriya': Sarkin Lagos Ya Fadi Abin da Ke Ransa ga Atiku
- Sarkin Lagos, Oba Rilwan Akiolu, ya yi magana kan yiwuwar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya zama shugaban ƙasa
- Sarkin ya ce duk da hakan ƙaddara ce, amma zai yi wahala Atiku ya zama shugaban Najeriya saboda wasu dalilai
- Akiolu ya bayyana hakan yayin bikin zagayowar haihuwarsa ta 82 a fadarsa, inda ya ce shugaba Bola Tinubu ne Allah ya zaɓa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Sarkin Lagos, Oba Rilwan Akiolu, ya bayyana hasashensa kan neman takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Sarkin ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ba zai taɓa zama shugaban Najeriya ba saboda kaddara.

Source: Facebook
Sarkin Lagos ya taba Atiku kan siyasa
Basaraken ya faɗi hakan ne yayin hira da wakilin jaridar Tribune da wasu ‘yan jarida a fadarsa a yau Asabar 8 ga watan Nuwambar shekarar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan
"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin ya bayyana haka ne yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa wanda ya cika shekaru 82 da kuma shekara 22 a kan karagar mulki
A cewarsa, shugabancin Bola Ahmed Tinubu na yanzu al’amari ne da Allah ya tsara, don haka ya bukaci al’umma su ba shi goyon baya sosai.
Ya ce:
“Gobe ta Allah ce, amma bari in faɗi gaskiya, Atiku Abubakar ba zai taɓa zama shugaban Najeriya ba, Tinubu mutum ne mai tausayi da hangen nesa.”

Source: Facebook
Yadda Sarki ya yi hasashen nasarar Tinubu
Sarkin ya tuna cewa ya taɓa hasashen Tinubu zai zama shugaban ƙasa tun bayan zama Sarki a 2003, yana mai cewa zai gama wa’adinsa lafiya.
“Ni ba ɗan siyasa ba ne, amma na san Allah ne ya zaɓi Tinubu. A ranar 23 ga Mayu, 2003, na faɗi hakan."
- Oba Rilwan Akioluaf
Akiolu ya yaba da yadda Tinubu ya inganta Lagos lokacin yana gwamna, yana mai fatan Allah zai ba shi damar kammala wa’adinsa cikin nasara.

Kara karanta wannan
'Abin da zan faɗawa Trump ido da ido, idan na haɗu da shi': Barau Jibrin ya fusata
Rokon Sarkin Lagos ga gwamnatin Tinubu
Game da ci gaban Lagos, Sarkin ya ce jihar na fama da matsanancin cunkoso da matsin ababen more rayuwa saboda yawan mutane da tattalin arziki.
Ya sake roƙon gwamnatin tarayya ta bai wa Lagos matsayi na musamman, yana cewa tattalin arzikinta da muhimmancin da take da shi sun cancanci kulawa ta musamman.
Ya kara da cewa:
“Ina roƙon gwamnati ta bai wa Lagos matsayi na musamman, matsin da ake ciki ya yi yawa, kuma wannan abu ne da ya dade da kamata."
Wike ya fadi dalilin Atiku na barin PDP
A baya, an ji cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya sake taso da batun ficewar Atiku Abubakar daga jam'iyyar PDP watanni bayan aukuwar hakan.
Nyesom Wike ya bayyana cewa dole kanwar na ki ce ta sanya tsohon mataimakin shugaban kasar ya tattara 'yan komatsansa ya fice daga PDP.
Hakazalika, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya zargi masu sauya sheka daga PDP da cewa su ne suka lalata jam'iyyar kafin su fice.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng