Zaben 16 ga Fabreru: Kai ke da nasara - Oba na Legas ya yiwa Buhari albishir

Zaben 16 ga Fabreru: Kai ke da nasara - Oba na Legas ya yiwa Buhari albishir

- Sarkin Legas, (Oba of Lagos), Oba Riliwanu Akiolu ya ce Buhari mutum ne mai cika alkawarun da ya dauka kuma shi ne zai samu nasara a zabe mai zuwa

- Sarkin ya godewa Buhari akan namijin kokarinsa na nuna dattako da daukar 'yan Nigeria a matsayin mutane masu daraja

- Basaraken ya koka kan irin halin kuncin da gwamnatin baya ta jefa kasar

Sarkin Legas, (Oba of Lagos), Oba Riliwanu Akiolu ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari mutum ne mai cika alkawarun da ya dauka kuma shi ne zai samu nasara a zaben ranar 16 ga watan Fabreru, 2019.

Mr Akiolu ya bayyana hakan a lokacin da shugaban kasa Buhari da tawagar yakin zabensa suka kai masa ziyara a fadarsa da ke tsibitin Legas a ranar Asabar bayan dira jihar, a ci gaba da kaddamar da gangamin neman yakin zabensa, domin fuskantar zaben mako mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Hotuna: Yadda yakin zaben shugaban kasa Buhari ya ke gudana a Legas

Zaben 16 ga Fabreru: Kai ke da nasara - Oba na Legas ya yiwa Buhari albishir
Zaben 16 ga Fabreru: Kai ke da nasara - Oba na Legas ya yiwa Buhari albishir
Asali: UGC

Sarkin, wanda ya yi nuni da cewa kafatanin masu rike da sarautun gargajiya a jihar na farin ciki da karbar tawagar shugaban kasar, yana mai cewa ya godewa Buhari akan namijin kokarinsa na nuna dattako da daukar 'yan Nigeria a matsayin mutane masu daraja.

Ya baiwa shugaban kasa Buhari tabbacin cewa zai samu nasara a zabe mai zuwa kamar yadda ya samu nasara a zaben 2015.

"Ku sake baiwa Buhari wata damar, ni kuma ina mai tabbatar maku da cewa zaku sha mamakin yadda kasar za ta ci gaba," a cewar Mr Akiolu.

Basaraken ya koka kan irin halin kuncin da gwamnatin baya ta jefa kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel