ECOWAS, Sanusi II da Malaman Musulunci Sun Zauna kan Ta'addanci, an taɓo Karatun Allo

ECOWAS, Sanusi II da Malaman Musulunci Sun Zauna kan Ta'addanci, an taɓo Karatun Allo

  • Yayin da ake tsaka da fuskantar barazanar Donald Trump a Najeriya, Kungiyar ECOWAS tare da shugabannin addinin sun gana
  • An yi ganawar tsakanin malaman Musulunci da kungiyar inda suka kuduri aniyar hada kai wajen yakar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi
  • Taron ya mayar da hankali kan inganta makarantu na addini da karfafa matasa don rage daukar su cikin kungiyoyin ta’addanci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ta jagoranci wata ganawa domin kawo karshen ta'addanci.

Kungiyar ECOWAS ta gana da kungiyoyin malamai Musulmai domin yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi a yankin Sahel.

ECOWAS ta gana da sarakuna da malamai kan ta'addanci
Shugaban ECOWAS, Omar Touray da Sarki Sanusi II. Hoto: ECOWAS - Cedeao.
Source: Facebook

Ta'addanci: ECOWAS ta gana da malaman Musulunci

Rahoton Punch ya ce wannan kiran ya fito ne a karshen taron farko na Musulmai kan tsaro da shugabanci wanda aka gudanar a majalisar ECOWAS da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Yan Majalisa 31 sun goyi bayan matakin da Amurka ta dauka kan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taken taron ya kasance “Rawar da Kungiyoyin Musulmai ke takawa wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel.”

ECOWAS da kungiyar Ansariddeen Attijaniyya ne suka shirya taron, inda shugabanni, sarakuna, da masana suka halarta daga kasashe daban-daban.

Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Touray, ya bayyana taron a matsayin muhimmin mataki wajen karfafa hadin gwiwa don magance ta’addanci a yammacin Afirka.

Ya ce rahoton 2025 kan ta'addanci ya nuna cewa Afirka ta zama cibiyar ta’addanci ta duniya.

Touray ya kara da cewa, akwai bukatar a gyara tsarin makarantun allo ta hanyar mayar da su na zamani domin hana samari fadawa cikin tsattsauran ra’ayi.

“Ya kamata mu sabunta makarantunmu don su zama cibiyoyin ilimi da ci gaba."

- Omar Touray

Sarki Sanusi ya yi magana kan ta'addanci a Afirka
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II yayin rangadi. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Twitter

Abin da Sanusi II ya ce a taron ECOWAS

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya yaba wa ECOWAS bisa jajircewarta wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Yan PDP sun nemi agajin Trump, EU yayin zanga zanga, sun roki bangaren shari'a

Ya ce:

“Mu hada kai domin gina makoma mai kyau ga yaranmu da al’ummarmu.”

Wakilin kungiyar Tarayyar Afirka, Mohamed Chambas, ya jaddada cewa, taron ya samar da shawarwari da dabaru don amfani da tasirin kungiyoyin Musulmai wajen hana tsattsauran ra’ayi.

Chambas ya ce mahalarta sun yarda cewa koyarwar Musulunci ta gaskiya na jaddada zaman lafiya, adalci, da girmama rayuwar ɗan Adam.

Sun kuma gano talauci, rashin aikin yi, da rashin adalci a matsayin tushen daukar matasa cikin kungiyoyin ta’addanci.

Taron ya kammala da amincewa da “Sanarwar Yankin Sahel” wadda ta kunshi hanyoyin bunkasa ilimin Musulunci da karfafa zaman lafiya, hakuri, da hadin kai tsakanin al’umma a yankin Afirka ta Yamma.

Sanusi II ya gargadi Tinubu kan bashi

Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai kamata a rika ciwo bashi bayan cire tallafin mai ba.

Sarki Sanusi II ya yabawa gwamnati wajen daidaita tsarin musayar kudi da cire tallafin mai amma ya ce ba za a ga sakamako ba sai an sauya tafiya.

Kara karanta wannan

Najeriya da sauran ƙasashen Afrika da Amurka ke yi wa kallon barazana

Sanusi II ya ce matsalolin tattalin arzikin Najeriya sun samo asali ne daga rashin daidaito a manufofin gwamnati da kashe kudi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.