Yan PDP Sun Nemi Agajin Trump, EU yayin Zanga Zanga, Sun Roki Bangaren Shari'a

Yan PDP Sun Nemi Agajin Trump, EU yayin Zanga Zanga, Sun Roki Bangaren Shari'a

  • Wasu magoya bayan jam'iyyar PDP sun gaji da halin da ake ciki a Najeriya yayin da suka gudanar da zanga-zanga a Abuja
  • An yi zanga-zangar lumana a Abuja, inda suka kai korafi ga Ofishin Jakadancin Amurka, Tarayyar Turai da Sufeton 'Yan sanda
  • Zanga-zangar mai taken “Kare Dimokuradiyya daga Barazana” ta nemi tallafin ƙasashen duniya wajen hana danniya da take hakkin yan adawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wasu mambobin ƙungiyar masu ra'ayin jam’iyyar PDP sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja.

An yi zanga-zangar domin neman taimako daga ketare inda suka kai ziyara ga manyan ofisoshi na ƙasashen waje.

Yan PDP sun yi zanga-zanga a Abuja
Dandazon magoya bayan PDP kenan yayin zanga-zanga a Abuja. Hoto: @OfficialPDPNig.
Source: Twitter

Hakan na cikin wani rubutu da shafin jam'iyyar adawa ta PDP ya yi a yau Alhamis 6 ga watan Nuwambar 2025 a shafin X.

Kara karanta wannan

Luguden wuta a Najeriya: APC ta rubutawa majalisar Amurka wasika kan Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barazanar da Trump ya yi ga Najeriya

An gano masu zanga-zangar a bakin ofishin jakadancin Amurka inda suke neman daukin kasar domin kare yan adawa.

Wannan zanga-zanga ta zo ne a daidai lokacin da ta yi tsami tsakanin Najeriya da Amurka bayan zargin da shugaba Donald Trump ya yi wa kasar.

Trump ya zargi Najeriya da yin sakaci yayin da ake yi wa Kiristoci kisan kare dangi wanda ya ce hakan take hakkin addininsu ne da neman karar da su a doron kasa.

Daga bisani, shugaban ya bukaci Najeriya da ta dauki matakin kawo karshen ta'addan da zubar da jini ko kuma ya dauki matakin soji a kan kasar.

Yan PDP sun nemi agajin Trump yayin zanga-zanga
Shugaban jam'iyyar PDP a Najeriya. Hoto: Peoples Democratic Party, PDP.
Source: Twitter

Masoyan PDP sun yi zanga-zanga a Abuja

Masu zanga-zangar sun ziyarci Ofishin Jakadancin Amurka, Tarayyar Turai, Ma’aikatar Shari’a, da Hedikwatar ‘Yan sanda.

Sun gabanatar da korafin ne domin neman a kare dimokuradiyya daga barazana da tsoratarwa daga gwamnati mai ci.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ba ku sani ba game da Zohran Mamdani, sabon magajin garin New York

Masu zanga-zangar suna ɗauke da kwalaye masu rubuce-rubuce kamar “A kare dimokuradiyya,” “A daina danniya,” da “A mutunta dokoki da tsarin mulki.”

Abin da masu zanga-zangar ke bukata

Shugaban ƙungiyar ya ce, manufarsu ba don jam’iyyar PDP kaɗai ba ce, amma don kare rayuwar dimokuradiyya da 'yancin siyasa a Najeriya.

A cewarsa:

"Muna sanar da duniya cewa tsoratarwa da kama-kame na siyasa sun kai bango, kuma dole a tsaya da gaskiya.”

An ga jami’an tsaro sun kewaye wuraren zanga-zangar don tabbatar da zaman lafiya, yayin da jakadanci da hukumar Turai suka karɓi ƙorafin ƙungiyar.

PDP ta fadi dalilin hukunta maciya amana

Mun ba ku labarin cewa shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Ambasada Umar Iliyasu Damagum, ya yi magana kan rikicin da jam'iyyar ke fama da shi.

Umar Damagum ya bayyana cewa lokacin da ya hau kujerar shugancin jam'iyyar, ya same ta cikin tarun matsaloli wanda har yanzu aka gaza kawo karshen wasu daga ciki.

Shugaban na PDP ya nuna akwai masu ganin laifinsa kan kin daukar matakin ladabtarwa kan wasu mambobin jam'iyyar da suka saba doka da ya hada da cin amana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.