Tashin Hankali: An Lakadawa Limamin Masallacin Juma'a Duka har Ya Mutu a Kwara

Tashin Hankali: An Lakadawa Limamin Masallacin Juma'a Duka har Ya Mutu a Kwara

  • Fusatattun matasa sun kashe limamin garin Sokupkpan, Abdullahi Audu, bisa zargin shi da haddasa mutuwar wani matashi
  • An ce 'yan uwan matashin sun zargi limamin da rike kurwar dan uwansu, tare da saka masa rashin lafiyar da ta zama ajalinsa
  • Jami'an 'yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa an kama mutum hudu da ake zargi da hannu a kisan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kwara - An shiga tashin hankali a Sokupkpan, wani gari da ke cikin ƙaramar hukumar Edu, jihar Kwara, bayan kashe limamin garin, Mallam Abdullahi Audu.

Rahotanni sun nuna cewa wasu fusatattun matasa ne suka kashe Liman Abdullahi, bisa zargin cewa shi ne ya lashe kurwar wani matashi, Ibrahim Gana har ya mutu.

Kara karanta wannan

Bayan daura aure, matashi 'dan shekara 25 ya caka wa matarsa wuka har lahira a Sakkwato

Fusatattun matasa sun kashe limamin masallacin Juma'a a jihar Kwara kan zargin maita.
Hoton babban masallacin kasa na Abuja. A kula, an yi amfani da hoton don misali kawai. Hoto: Adam Abu-bashal/Anadolu Agency
Source: Getty Images

An zargi limamin Juma'a da maita

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa matasa sun lakadawa limamin duka har ya mutu a ranar Laraba, 5 ga watan Nuwamba, 2025, in ji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tashin hankalin ya fara ne bayan an wayi gari da mutuwar matashi Ibrahim Gana, wanda ya dade yana fama da rashin lafiya, da ta ɗaure wa mutane kai.

Kafin rasuwarsa, rahotanni sun ce Ibrahim Gana ya rika cewa limamin garin yana yawan zuwa masa a mafarki, kuma ya kama kurwarsa, har dai wasu suka fara yarda da maganarsa.

Wani mazaunin yankin ya ce:

“Yayin da jikinsa ya kara tsananta, mutane suka fara gaskata cewa limamin ne ya sanya masa wannan cuta, ta hanyar lashe kurwarsa.
"Bayan rasuwar Ibrahim ne wasu matasa suka yanke hukuncin cewa limamin ne ya kashe shi, abin da ya jawo suka sauke fushinsu kansa."

Kara karanta wannan

Rubutu a Facebook ya jefa 'yan Kwankwasiyya 2 a gagarumar matsala a Kano

Matasa sun kashe limamin da duka

A ranar Laraba, bayan jana’izar marigayin, wasu daga cikin ‘yan uwansa — Mohammed Shaba, Mamudu Gana da Ndakpotun Issa — suka tara wasu matasa domin su kai wa limamin farmaki.

Duk da cewa dattawan garin sun yi ƙoƙarin hana su, matasan suka yi biris, suka rufe limamin da duka, inda ya mutu a sakamakon raunin da ya samu.

Wani ganau ya ce:

“Sun zarge shi da kashe matashin ta hanyar maita. Duk wanda ya yi ƙoƙarin hana su, sai su yi masa barazana shi ma."

An ce ‘yan sanda daga ofishin rundunar na Tsaragi sun isa wurin bayan kisan, inda suka kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a kisan.

Kara karanta wannan

Femi Falana: Babban lauya ya fallasa Trump kan zargin kisan Kirsitoci

'Yan sanda sun ce an kama matasa 4 da ake zargi da hannu a kisan limamin masallaci a Kwara
Taswirar jihar Kwara da ke a Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

’Yan sanda sun kama mutane 4

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis, tana mai bayyana shi a matsayin “mummunan kisa”.

Ta ce binciken farko ya nuna cewa bayan rasuwar Ibrahim Gana mai shekaru 25, ‘yan uwansa suka zargi limamin da zama silar mutuwarsa, sannan suka tara jama’a suka kashe shi.

Sanarwar 'yan sandan ta ce:

“Mutane hudu sun shiga hannun hukuma, kuma bincike yana ci gaba da gudana domin kama sauran da suka tsere."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke rikakkun masu garkuwa da mutane, an kwato kudi da makamai

Kwamishinan ‘yan sanda, Adekimi Ojo, ya la’anci wannan aika-aika tare da jan kunnen jama’a su guji ɗaukar doka a hannunsu.

'Yan bindiga sun kashe limami da iyalansa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, limamin Juma’ar Maru da wasu ƴan gidansa sun mutu a hannun ƴan bindiga bayan kwashe watanni a cikin daji.

Masu majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigar sun yi amfani da dutse mai zafi wajen azabtar da jikansa mai shekara biyu har malamin ya mutu.

Duk da an biya kudin fansa har Naira miliyan 11, 'yan bindigar ba su sako duka mutanen da aka sace ba, wasu na nan a hannun masu garkuwa da mutanen.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com