Kisan Kiristoci: Ministan Tinubu, Keyamo Ya Tura Budaddiyar Wasika ga Shugaba Trump

Kisan Kiristoci: Ministan Tinubu, Keyamo Ya Tura Budaddiyar Wasika ga Shugaba Trump

  • Ana ci gaba da maida martani ga shugaban Amurka, Donald Trump bayan ya yi barazanar kawo farmaki don kare kiristocin Najeriya
  • Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya aika budaddiyar wasika ga Shugaba Trump kan zargin kisan kiristoci
  • Keyamo SAN ya bayyana cewa wannan zargi ba gaskiya ba ne domin matsalar tsaron Najeriya ta shafi kiristoci da musulmai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya rubuta budaddiyar wasika ga Shugaba Donald Trump na Amurka kan zargin kisan kiristoci a Najeriya.

Keyamo, wanda lauya ne da ya kai matsayin SAN ya musanta zargin, yana mai cewa bai dace da hakikanin gaskiyar abin da ke faruwa a ƙasar nan ba.

Festus Keyamo.
Hoton Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo da na Shugaba Donald Trump Hoto: @fkeyamo
Source: Facebook

Festus Keyamo ya bayyana haka ne a wasikar da ya aika wa Shugaba Trump, wacce ya wallafa a shafinsa na X yau Laraba.

Kara karanta wannan

Trump: Minista ya fadi dalilin Tinubu na ba shi muƙami, ya ƙaryata kisan Kiristoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan, wanda tsohon mai fafutukar kare haƙƙin ɗan adam ne ya roƙi Trump da ya hada kai da Najeriya wajen yaƙar ta’addanci, maimakon dogaro da rahotannin ƙarya daga waje.

Keyamo ya musanta zargin kisan kiristoci

Keyamo ya ce an haife shi Kirista kuma ya girma a matsayin Kirista, don haka ba zai taba yarda da yi wa kiristoci kisan kiyashi ba.

Ya tuna irin gwagwarmayar da ya sha ta kare haƙƙin ɗan adam da ta kai ga samun kyautar Global Human Rights Award a Washington a shekarar 2017.

Ya ce, sabanin yadda ake yadawa a duniya, ba gaskiya ba ne cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya saboda addininsu.

"Ba zan taɓa yarda in yi aiki a kowace gwamnati da ke kisan Kiristoci ba. Wannan zargi ƙarya ne kuma rashin adalci ne ga Najeriya,” in ji shi.

Festus Keyamo ya fadawa Trump gaskiya

Ministan ya bayyana cewa matsalar tsaro da ake fama da ita a wasu yankuna ta samo asali ne daga kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram, ‘yan bindiga da makiyaya.

Kara karanta wannan

Harin Amurka: Ana dar dar a Najeriya, malami ya tabbatar da kisan Kiristoci

Ya shaida wa Trump a wasikar cewa wadannan kungiyoyi na kai hare-hare ga dukkan ‘yan Najeriya, Musulmi da Kiristoci ba tare da bambanci ba.

Ya ƙara da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, duk da cewa Musulmi ne, mutum ne mai matsakaicin ra’ayi kuma yana da kyakkyawar alaka da Kiristoci.

Ya kuma yi nuni da cewa matar shugaban ƙasa, Remi Tinubu fasto ce a babban coci, yayin da yawancin ‘ya’yansa Kiristoci ne masu rike da addinin.

Haka kuma, ya jaddada cewa da dama daga cikin hafsoshin tsaro da Tinubu ya naɗa Kiristoci ne, don haka ba zai yiwu wannan gwamnati ta goyi bayan kisan kiristoci ba.

Abin da Ministan ya nema daga Amurka

"Najeriya ƙasa ce mai bin tsarin mulkin da ya tanadi ‘yancin addini. Ba a taɓa ɗaukar wani addini a matsayin na gwamnati ba. Matsalolin tsaro da muke fuskanta sun shafi Musulmi da Kiristoci duka.
"Yan Najeriya na bukatar a samu fahimta, haɗin kai, da tattaunawa mai kyau da gwamnatin ku (Amurka). Muna roƙon ku da ku tantance hanyoyin samun bayanai na gaskiya game da kasarmu."

Kara karanta wannan

CAN: Martanin Kiristocin Arewa bisa barazanar Trump na kawo farmaki a Najeriya

- Festus Keyamo.

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo.
Hoton Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo (SAN) Hoto: @fkeyamo
Source: Facebook

Ya ƙare wasikar da kiran ƙarfafa dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka, tare da tabbatar da cewa Najeriya za ta ci gaba da zama ƙasa mai zaman lafiya da jituwa tsakanin addinai.

Afenifere ta maida martani ga Trump

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kare al'adun Yarbawa ta Afenifere ta yi magana kan barazanar da shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi wa Najeriya.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa matakin Trump wata dabara ce da ke nuna rashin jin dadinsa kan wasu abubuwa da Gwamnatin Bola Tinubu ta dauko don gyara kasar nan.

Afenifere ta ce zargin cewa gwamnatin tarayya tana da hannu a kisan Kiristoci ba shi da tushe, kuma wani yunkuri ne na bata sunan kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262