'Musulmi zai Zama Shugaban Amurka,' Sheikh Gumi Ya Yi Hasashe

'Musulmi zai Zama Shugaban Amurka,' Sheikh Gumi Ya Yi Hasashe

  • Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce wata rana Musulmi zai zama shugaban Amurka
  • Hasashen Gumi ya zo ne bayan nasarar Zohran Mamdani da ya zama Musulmin farko da ya lashe kujerar magajin garin New York
  • Legit Hausa ta gano cewa Mamdani ya yi nasara ne bayan fafatawa mai zafi da kuma adawar shugaban kasa Donald Trump

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa wata rana Musulmi zai zama Shugaban Amurka, inda zai kai Musulunci har cikin Fadar White House.

Sheikh Gumi ya yi wannan hasashe ne bayan nasarar Zohran Mamdani, wanda ya zama Musulmin farko da ya lashe zaben magajin garin birnin New York, daya daga cikin manyan biranen Amurka.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Tsohon hafsan sojoji ya gano manufar Amurka kan Najetiya

Sheikh Ahmad Abubakkar Gumi
Malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi. Hoto: Salisu Hassan Webmaster
Source: Facebook

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Gumi ya taya Mamdani murnar lashe zaben New York.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gumi ya ce Musulmi zai shugabanci Amurka

Yayin da ya ke taya Zohran Mandani murnar zama Musulmi na farko da ya lashe zaben magajin garin New York, Sheikh Gumi ya rubuta cewa:

“Mamdani ya yi nasara! Mutanen da ke Washington su shirya samun bugun zuciya! Musulmai za su kai Fadar White House.”

Kalaman Sheikh Gumi sun haifar da ce-ce-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke ganin cewa malamin yana nufin Musulmai za su samu damar shiga manyan mukamai a kasashen Yamma.

Gumi, wanda aka fi sani da ra’ayinsa na adawa da manufofin Amurka da Isra’ila kan mamayar yankin Falasdinawa a Gaza, ya bayyana nasarar Mamdani a matsayin sabon babi a tarihi.

Zohran Mamdani
Zohran Mamdani da ya lashe zaben New York a Amurka. Hoto: Zohran Kwame Mamdani
Source: Facebook

Zohran Mamdani, mai shekaru 34, ya lashe zaben magajin garin New York a matsayin ɗan jam’iyyar Democrat, inda ya doke abokan hamayyarsa Andrew Cuomo da Curtis Sliwa.

Kara karanta wannan

Musulmi, Zohra Mamdani ya lashe zaben Amurka duk da barazanar Trump

Nasarar Mamdani ta zo ne duk da adawar da Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna masa, inda ya yi barazanar rage tallafin gwamnatin tarayya ga birnin idan aka zabe shi.

Mamdani da kalamansa kan Trump

Bayan bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, Mamdani ya yi jawabi mai zafi ga magoya bayansa, inda ya soki Shugaba Trump kai tsaye.

Rahoton Reuters ya nuna cewa ya ce:

“Donald Trump, na san kana kallonmu, ka kara sauti."

An ce maganarsa ta nuna cewa zai kasance babban abokin adawa da manufofin shugaban kasar, musamman kan batun shige da fice da bambancin addini.

Masu sharhi sun bayyana Mamdani a matsayin jagoran sabuwar tafiyar matasa masu fatan adalci, wadanda ke son ganin Musulmai da sauran addinai suna da wakilci a siyasar Amurka.

Gumi ya gargadi Najeriya kan Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi gargadi kan zuwan Isra'ila Najeriya.

Malamin ya yi gargadi da cewa nan gaba kadan za a iya fara kashe malaman Musulunci a Najeriya idan ba a yi taka tsan-tsan ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Rigima ta kaure a zaman Majalisar Wakilan Tarayya, an yi musayar yawu

Ya yi magana ne bayan wasu jami'an gwamnatin Isra'ila sun gana da Kiristocin Najeriya a wata ziyara da suka kawo kasar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng