Majalisa za Ta Sa Labule da Gwamnatin Tarayya kan Barazanar Trump
- Majalisar Dattawa ta bayyana cewa za ta tattauna da bangaren zartarwa kan barazanar mamayar Najeriya da Donald Trump ya yi
- Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio ya ce batun yana da nasaba da harkokin diflomasiyya, don haka ana bukatar martani na kasa baki daya
- Gwamnatin tarayya ta sake nanata cewa babu wani kisan kare dangi a Najeriya, inda ta bayyana cewa kalaman Trump ba daidai ba ne
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa majalisar za ta tattauna da gwamnatin tarayya kan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump.
Trump ya ayyana Najeriya a matsayin kasar da ta bari ana kashe kiristoci, saboda haka ya yanke shawarar ya dauki matakin da ya dace, daga ciki har da kawo wa kasar hari.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a martaninsa, Akpabio ya ce batun ya shafi manufofin diflomasiyya da hulɗar ƙasashen duniya, saboda haka ba za a yi magana gaba-gadi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin majalisa kan kalaman Trump
New Telegraph ta wallafa Sanata Akpabio na cewa yanayin sarkakiya na batun da ake magana a kai, ya sa ba za su ce komai ba sai an gana da bangaren tarayya.
A makon da ya gabata, ya yi barazanar kai hari da dakarun Amurka ga Najeriya bisa zargin ana kisan Kiristoci a ƙasar.
Trump ya ce:
“Idan gwamnatin Najeriya ta ci gaba da barin kashe Kiristoci, Amurka za ta dakatar da duk tallafin da take bayarwa, kuma za ta iya shiga ƙasar da makamai don kawar da ‘yan ta’adda.”

Source: Facebook
Akpabio ya bayyana cewa har yanzu majalisar ba ta fara tattauna wannan batu ba, amma za ta yi hakan tare da gwamnatin Tinubu domin sanin matsayinta kafin ɗaukar wani mataki.
A kalaman Akpbaio:
“Na ƙi amincewa da kowane kudiri a yanzu saboda muna jiran sanin yadda gwamnati za ta dauki mataki kan lamarin."
Gwamnati ta musanta zargin kisan Kiristoci
A gefe guda, gwamnatin tarayya ta sake jaddada cewa babu wani kisan kare dangi da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.
Ministan bayani da daidaita ra’ayi, Mohammed Idris, ya bayyana hakan bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa, Abuja.
Ministan ya ce masu tsattsauran ra’ayi da ke yada labarin cewa ana kisan Kiristoci suna ƙoƙarin raba ƙasa da haddasa rikici.
Ya kara da cewa shugaba Tinubu yana gudanar da lamura cikin natsuwa duk da barazanar da Trump ya yi.
Mohammed Idris ya tabbatar da cewa ƙasashen duniya sun fahimci kokarin da gwamnati ke yi wajen tabbatar da tsaro.
China ta gargadi Amurka kan Trump
A baya, mun wallafa cewa kasar China ta gargadi Shugaban Amurka da ya jingine duk wani yunkuri na kawo hari Najeriya, kasa mai cikakken ikon gudanar da al'amuranta.

Kara karanta wannan
"Najeriya ba ta da damar goyon bayan kisan addini": Minista ya karyata Trump a idon duniya
Wannan na zuwa ne a matsayin goyon baya ga Najeriya duba da karfin alakar kasuwanci da masana,antu a tsakanin kasar da China, musamman a 'yan kwanakin nan.
China ta kara da cewa ta aminta da yadda gwamnatin Najeriya ke gudanar da al'amuranta, da kuma kokarin da ta ke yi wajen kawar da matsalolin tsaro a kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

