'An Rasa Jigo a Najeriya,' Tinubu kan Rasuwar Tsohon Gwamna, Janar Mohammed

'An Rasa Jigo a Najeriya,' Tinubu kan Rasuwar Tsohon Gwamna, Janar Mohammed

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhinin sa kan rasuwar tsohon hafsan soja, Janar Abdullahi Mohammed Adangba
  • Ya yaba da irin rawar da marigayin ya taka wajen gina tsarin tsaro na kasa da kuma gudunmawarsa ga cigaban Najeriya
  • Shugaban kasar ya jajanta wa iyalan marigayin, gwamnatin jihar Kwara da kuma rundunar sojin Najeriya bisa babban rashin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi ta’aziyya tare da nuna jimami kan rasuwar tsohon gwamnan soja, Janar Abdullahi Mohammed Adangba (mai ritaya).

Daga cikin manyan mukaman da marigayin ya rike akwai matsayin mai bada shawara kan harkokin tsaro na kasa.

Bola Tinubu, Janar Abdullahi Mohammed
Marigayi Janar Abdullahi Mohammed da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan shugaba Bola Tinubu a wani sako da hadiminsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi, tsohon gwamna, NSA, Janar Mohammed ya rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Janar Mohammed Adangba ya rasu yana da shekara 86 kuma ya bayar da gagarumar gudumawa a tsarin tsaro.

Gudunmawar Janar Mohammed ga tsaro

A cewar sanarwar, Tinubu ya ce Janar Abdullahi Mohammed Adangba ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa tsohuwar hukumar tsaro ta kasa (NSO).

NSO ce daga bisani ta haifar da hukumar tsaron cikin gida (SSS), hukumar leken asiri ta kasa (NIA), da hukumar leken asiri ta soji (DIA).

Haka kuma, ya rike mukamin gwamnan tsohuwar Jihar Benue-Plateau daga shekarar 1975 zuwa 1976, inda ya bar kyakkyawan tarihi a tsarin mulki da gudanarwa.

Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin soja nagari mai jajircewa, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da tsaron kasa da dorewar zaman lafiya a Najeriya.

Yabon shugaba Tinubu ga marigayin

Shugaba Tinubu ya bayyana Janar Mohammed Adangba a matsayin mutum mai halin kirki, wanda ya hada kwarewar soja da hangen nesa na dan siyasa mai fatan cigaba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi halin da Tinubu ke ciki bayan barazanar Donald Trump

Tinubu ya kara da cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara yadda ake gudanar da harkokin fadar shugaban kasa, inda akidar tsari ta zama abin koyi ga wadanda suka yi aiki da shi.

Ta’aziyyar Tinubu ga al’ummar Kwara

Shugaba Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, gwamnatin Jihar Kwara, rundunar sojin Najeriya, da dukkan wadanda ke cikin jimami a kan rasuwarsa.

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban Najeriya yana jawabi a wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya bayyana Janar Adangba a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ‘ya’yan Najeriya masu kishin kasa, wanda gudunmawarsa za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa a tarihi.

A cewar fadar shugaban kasa:

“Najeriya ta rasa babban jigo wanda ya ba da gudunmawa mai yawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasa. Za mu ci gaba da tuna da shi da girmamawa.”

Janar Abdullahi Mohammed ya rasu

A wani labarin, mun kawo muku cewa 'yan uwan Janar Abdullahi Mohammed sun tabbatar da rasuwarsa a yau Laraba, 5 ga Nuwamba, 2025.

Bayan sanar da rasuwarsa, danginsa sun bayyana cewa ana cigaba da tsare-tsare kan yadda za a yi masa jana'iza kamar yadda Musulunci ya tanada.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gwangwaje tsohon hafsan sojoji da ya yi ritaya, ya kara masa girma

Marigayin ya yi aiki da tsofaffin shugabannin kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, Olusegun Obasanjo da Umaru Musa Yar'adua.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng