Dan Majalisar Tarayya Ya Sha da Kyar bayan ’Yan Bindiga Sun Kai Masa Farmaki
- Wani soja ya rasa ransa yayin da jami'an tsaro suka mayar da martani ga harin da yan bindiga suka kai kan dan majalisar tarayya
- Lamarin ya faru ne a kan hanyar Lumma–Babanna da ke Borgu a jihar Niger inda mutane da dama sun jikkata
- Shaidu sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun lalata akalla motocin tawagar dan siyasar 11 da harbin bindiga
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Minna, Niger - Dan majalisar tarayya, Jafaru Mohammad Ali Damisa, ya sha da kyar bayan harin yan bindiga da aka kai masa.
An tabbatar da cewa Damisa ya tsira daga harin da ake zargin ’yan ta’adda suka kai masa a ranar Talata 4 ga watan Nuwambar 2025 a jihar Niger.

Source: Original
An kai hari kan dan majalisar tarayya
Rahoton Bakatsine da ke sharhi kan matsalolin tsaro a X ya ce lamarin ya faru ne bayan da maharan suka yi wa tawagarsa kwanton bauna inda mutane da dama suka jikkata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun nuna cewa harin ya faru ne a kan hanyar Lumma–Babanna da ke cikin karamar hukumar Borgu, a jihar Niger.
Damisa, wanda ke wakiltar mazabar Borgu da Agwara a majalisar tarayya, yana kan hanyarsa zuwa Babanna domin wani aiki na gwamnati lokacin da maharan suka bude wuta kan tawagarsa.
Kokarin da jami'an tsaro suka yi a Niger
Shaidu sun bayyana maharan a matsayin “Lakurawa” wasu 'yan ta’adda da suka addabi al'umma, inda suka kai harin da rana suka kuma yi wa jami’an tsaro turjiya saboda rashin shiri.
Jami’an tsaro da ke rakiyar dan majalisar sun mayar da martani kai tsaye, sai dai a yayin musayar wuta, wani soja ya rasa ransa, wasu kuma sun jikkata sosai.
Haka kuma wasu magoya bayan dan majalisar tarayyar da ke tare da shi sun samu raunuka sakamakon harin, cewar rahoton Daily Post.
Tattaunawar Legit Hausa da kakakin yan sanda
Kakakin rundunar yan sansa, Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Legit Hausa a yau Laraba 5 ga wata Nuwambar 2025.
Abiodun ya ce tabbas a ranar 4 ga watan Nuwambar 2025 aka samu rahoton kai hari kan dan majalisar da misalin karfe 11 na rana.
Ya ce:
"A ranar 4 ga Nuwamba, 2025, da misalin karfe 11 na safe, an samu rahoto cewa an kai wa dan majalisar wakilai mai wakiltar Borgu/Agwara da tawagarsa hari a kauyen Audu-Fari, kan hanyar Babana, daga wasu da ake zargin 'yan bindiga ne.
"Sai dai jami'an tsaro da suke cikin tawagar sun dauki mataki nan da nan, sun fatattaki maharan tare da ceto dan majalisar lafiya, wasu mutane sun ji rauni, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likita."

Source: Facebook
Niger: Yawan motoci da aka lalata yayin harin
Wani shaidan gani da ido ya ce maharan sun yi ta harbi ba kakkautawa ba, inda motocin tawagar dan siyasar suka lalace sakamakon harbin bindiga.
Bincike ya nuna cewa akalla motocin tawaga 11 ne suka lalace kuma suka cika da hulunan harsashi kafin daga bisani a dauke su daga wajen.
Duk da munin harin, Damisa ya tsira ba tare da wani rauni ba, lamarin da ya sa ake yabawa kokarin jami’an tsaro da suka kare shi har ya kubuta da ransa.
'Yan bindiga sun sace mataimakin kakakin majalisa
A baya, an ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi ta'asa a jihar Kebbi bayan sun kai wani harin da ya ritsa da babban jami'in gwamnati.
Tsagerun 'yan bindigan sun yi awon gaba da mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi da suka kai hari a garinsa.
'Yan bindigan sun sace mataimakin shugaban majalisar ne lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida da ya kammala sallah a masallaci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


